Wace Ta Dace Dani?

17 3 0
                                    

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*WACE TA DACE DANI?*

*story n written by*
*Ummy Ontop*



*Alhmdlhi!!! Fan nasake dawowa bayan tsawon lokaci ina fatan zaku bani hadin kai domin da zafinta na dawo , kubiyoni cikin wannan labari mai cike da sarkakiya danjin yacce zaka kaya*




Wattpad @UmmyOntop

Page 1-2



Lamis!lamis!!lamis!!! kallonshi budurwa da ake kira da limis batayi ba bare tasamu damar bashi amsa, ran yasir idan yayi dubu ya b'aci a fusace ya k'araso gurin da lamis ke zaune cikin zafin nama ya daga hannunshi yasauke a fuskar lamis, yakuma yunkurowa ze kuma kaimata wani Marin a karo na biyu akayi saurin damke hannunshi kull karka soma maimaita danyen aikin nan, haba! Kai dan saurayi yazaka mari mace har kana kokarin kara mata wani kuma a bainar jama'a wannan ba girman ka bane Sam baikamaceka ba gaka da siffar mutumin kirki , mata abun atausaya musu ne , akuma girmamasu , mata sunada daraja babba, yasir banda muzurai da huci ba abun da yake yi , warce hannunshi yayi daga rukon da saurayin yamishi ya nuna lamis da tsaya wacce tun ganin saurayin nan bata iya motsin kirki ba hankalinta yabar jikinta zuciyarta gaba daya bata tare da ita, yasir yace" wallahi lamis saikinyi mugun nadama matukar baki bani kudina ba na baki nan da zuwa la'asar karfe hudu daidai naga kudi na idan ba haka ba zakiyi gagarumin nadamar amsar kudin nan, nawa ne kudin? saurayin ya tambaya ,yana faman muzurai yace" dubu talatin ne, yasa hannu a aljihu yaciro dubu hamsin yace ga kudin ka, nan kidan ya chanja salo yasir ya dagaje baki cewa yake" hamsin fa ka bani yahaura talatin din, eh ka rike duka kasha ruwa nan gaba ka rike girmama mata aduk inda ka gansu please, daga haka yasa kai yayi gaba .

Lamis data lulu wani kagin da batasan sanda tajeba ta Ankara da  ya tafi ta tashi da Sauri tabi bayanshi ta taddashi yana kokarin barin harabar makarantar tayi saurin tare gaban motarshi ba shiri yayi saurin taka burki , yayi k'asa da gilas din motarshi ta karaso yazaka tafi ,ya tsyaa kallon ta dan be fahimci metake nufi ba, yazaka tafi banyima godiya ba ta fada cikin yanayin marairaicewa , murmushi yayi da yakara bayyanar da asalin kyanshi , murmushin nan yakuma tasiri a zuciyar lamis , wani kallo take mai mai cike da ma'ana tace" na gode sosai da karemun mutunci na dakayi agurin yasir, da za'a samu mutanen kirki irinka za'amu cigaba a rayuwa, murmushin yasake yimata sannan yace" babu komai yen mata amma kema ki rikà kame mutuncin ki da kanki basai wani ya kare miki ba kuma ki rika hakuri da yacce kika samu kanki karkice dole saikin nema wajen da za'a wulakantako shi abun dunia ba komai bane idan kayi hakuri zaka samu wataran Allah yana sane da komai ki kame kanki yerUwa , inshaAllah nagode da tunatarwar ka , daga haka bai tsaya kunajin mezatace ba yaja motarshi yayi gaba , shikuma wannan haka yake ya tafi bangama magana ba koh sunanshi da number shi be bani ba.

******

K'aton gida ne na alfarma daga waje gate din Gidan seka daga kai sama zakaga karshen shi, daga wajen gidanma abun kallo ne hakan ze shedama ciki kuma aljanna ce ta dunia.
Horn yake dannawa ajere cen saiga megadi ya fallo a guje ya wangale tafkeken gate din gidan, a miliyan ya danna hancin motar cikin fakeken gidan , wata runface da akayita ta alfarma dan Adana motoci ciki yashige ya faka tangamemiyar motar tashi yaziro kafafuwanshi waje adaidai lokacin da wayar shi tahau ruri sunan Dr mahad na yawo saman screen dinshyi, dauka yayi tare da kara wayar a kunne kana yafito daga motar yayi cikin gidan wanda tafia ce medan nisa daga wajan da aka ware dan adana motoci, ya akayi Dr cewar Dameer
" wallahi mutumina baka da kirki ka shanyani kasan kuma kai nake jira"
Dameer yace" kazo ka sameni a gida semu wuce mana"

Mahad yaja dan k'aramin tsaki yace ok senaxo, daga haka Dameer ya katse wayar ya k'arasa shiga cikin makeken falon da ya hadu da kayan alatu, falon anyi barin kudi acikinshi ya hadu iya haduwa sai wanda ya gani.

Upstairs ya haye sanadin be tadda kowa a falon ba direct dakinshi yawuce , ashe bamuga komai ba se anshiga dakin Dameer xa'asan gidan yaci kudi iya son ranshi , dakin babu tarkace dayawa ciki da falo ne amma yayi kyau komai kwallian blue ne acikin falon yayin da cikin dakin maroon ne yasha kyau Bango guda hotonshi ne a manne yayi masifar kyau cikin hoton.

Kayan jikinshi yacire yashige toilet ya watso Sabon wanka ya fito yashirya cikin kaya coffee colour shadda ya gyara sumar kanshi yasha turare da agogo da takalmi yadau phone nashi yayi waje , part din amminshi yayi yayi mata sallama tabashi izinin shigowa yashiga da sallama , cikin girmamawa ya tsuguna ya gaishe da mahaifiyarshi ta amsa tanamai samai albarka da farincikin samun da maiadabi da girma ma mutane.

Tun yaushe ka dawo baka sanarmin ba shine sai yanxu , Sosa qeya yayi yana murmushi yace" sori ammi nazaci ko bacci kikeyi kuma mahad na jirana xamu fita shiyasa na wuce naje na shirya , tou yaron kirki yanzu ka wuce kaci abinci karka sake Ka fita bakaci komai ba kaji ko, yadan gyada kai yana murmushi cen k'asan zuciaya shi yana cewa" naga ranar dazan girma abincin ma kullum sai an sakani naci Allah ya barmin ammina" sallama yamata sannan ya wuce dining room dan cin abinci already suna zaman jiranshi dama  , xamanshi keda wuya saiga sallaman Dr Mahad , k'arasowa ciki Dr yayi yaja kujera dayacikin kujerun dinin din ya xauna bayan sun gama gaisawa Dr yace ina ammi ne tana ciki Dameer ya bashi amsa a takaice
Tou kayi ka gama ni nayi ciki wajen ammi zanje mugaisa.


Ku cigaba da bina cikin labarin nan mai ratsa xucia ina alfahari daku ma fans

Maimunatooh

WACE TA DACE DANIWhere stories live. Discover now