Wace Ta Dace Dani

5 2 0
                                    

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*WACE TA DACE DANI?*

*story n written by*
*Ummy Ontop*


Wattpad @UmmyOntop


17-18




Dameer da ammi suna dinner su da dare ammi tace wa Dameer nikam na koshi xanyi ciki idan ka k'ara kasameni a part dina akwai maganar dazamuyi tana gama fad'an haka ta tashi ta wuce, shidai Dameer ya lura da Ammi yau cikin farinciki take daidai lokacin daze k'ara mata farinciki akan farinciki kenan zesanar mata da yafitar da matar aure.


Bayan ya k'arasa kamar yacce ta umarceshi haka yayi part din ammi ya wuce, da sallama ya shiga tana zaune tana latsa waya, ajiyewa tayi ganin Dameer tana murmushi dan albarka k'araso ka samu waje ka zauna mana , cikin jin dadi shima ya k'arasa ya zauna kusa da ita a k'asa,

Dameer ta kira sunanshi, na'amm ammina
Kai yaro ne mai ladabi da biyayya bani Ba yaro ma kana darajashi bare babba, tunda nake dakai baka taba b'atamin Ba, ban taba saka Abu ka bujiremin ba shiyasa kullum cikin albarka ta kake shiyasa kullum nake k'ara godewa ubangiji daya bani kai a matsayin d'a ina alfahari sosai da halayyanka.

Dameer yayi murmushi kafin yace" ai ammi tarbiyyarki ce wannan shiyasa nake alfahari dake da Abba kunbani tarbiyya ta gari sedai Nace Allah yasaka muku da gidan aljanna Allah ya jaddada rahma ga Abbana, amin Yaron kirki.

Hakan ya kuma tabbatar min dacewa zaka amince da duk abunda zan fadama yanzu, inaso ka kasa kunne ka saurareni, Ina jinki Ammi, Yawwa inason fadama Zancen auranka da Dina ne ,gaban Dameer ne ya yanke ya fad'i take zufa tasoma karyomai, ammi taco gaba dacewa , burin mahaifinka mukeson cikawa dan mungama magana da Dadyn Dina auran naku baze wuce nanda wata d'aya ba , gashi ga dukkan alamu jininku ya hadu duda basanin juna kukayi ba. Jimmm shiru ya ratsa wajen , ammi ta katse shirun tare dacewa" koh bakaji ba bakace komai ba" se lokacin Dameer yadawo cikin hayyacinshi , dakyaryasake yanayinshi yace" ammi ai kuke da iko akanmu Kome kuka yanke muna shirye da karbanshi hannu biyu. Allah ubangiji yayima albarka Ameen Ammi .

Haka sukayi sallama Deemer yabaro site din ammi jiki sanyaye.



*****




Zaune take kan gadonta ta rungume pillow tayi nisa cikin tunanin Dameer yau Allah ya hada da damasoyin ta , Allah ka mallakamin shi a matsayin miji , Allah kasa babu wata acikin rayuwar shi , wayarta yahau ruri sunan misha ya bayyana a wayar dauka tayi bayan sun gaisa suka taba hira sannan sukayi sallama.

Momy ce ta turo koafar dakin Dina tashigo bakin gado ta zauna , Dina ta matso kusa da ita ta kwantar da kanta a cinyar Momy , uwar son jiki wannan mijinki yashiga uku, rufe fuskarta Dina tayi da tafi hannunta uhm uhm momy, ba wannan ba magana Nazo zanyi dake cire hannunta tayi daga fuskarta tace tou momy, momy tana shafa kanta tace " yer aljanna ke yarinya ce mei hankali shiyasa mahaifinki yake tinkaho dake kuma baya shayin ya zarta da hukunci koda babu shawaranki sabida yasan yarinya mai biyayya yake da ita , sabida haka yace na sanar miki da ya sa ranar auran ki wata d'aya... Zunbur Dina tayi ta mike daga kwanciyar da take innalillahi waEnna Elaihi rajiUn, momy mekikace , lallai abunda kunnan ki yaji haka ne, kofa aka turo aka shigo Dadyne Yashigo yer lele nasan bazaki bujirewa magana ta ba kuma nasan zabin dana miki bazaki nadamarshi ba idan kikamin wannan kingamamin komai duniya da lahira.hawaye dakeson zubowa daga idanunta tayi kokawar maidawa kafin tayi karfin halin cewa Dady kanada iko akaina kome kayi na karbeshi hannu biyu albarka ka ita kawai nakeso .


Dady dan farinciki sai sa mata albarka kawai yake yace tou Allah yamiki albarka tilon y'a kinfiyemin yara dubu samu yara na gari masu hankalinki sai antona ina godiya ga Allah dayasanya kika zama y'ata , ahaka dai momy da Dady suka fita daga dakin suka barta , suna ficewa ta kifa kan gadon ta ta fashe da kuka mai tsanani.
Innalillahi waEnna Elaihi rajiUn kaddara ta kenan ina murnan ganin zabin zuciya ta ashe zabin iyayena zan rayu dashi Allah ka kawo min dauki Allah ka fitar ni cikin wannan yanayi taci gaba da kuka.

Idanunta sunyi jajur sedataji kanta yafara sarawa sannan ta tsagaita da kukan tayiga toilet.





******





A bangaran lamis kuwa hankalinta yadawo jikinta yanzu domin kuwa hartaje gida ta fadawa iyayen ta zuwan iyayen Dameer , koda baba yasira taji bayanin lamis babi wani fatan alkhairi sena tsiya , tou Allah yasa da gaske yake wannan shegun samarin naki har akwai wanda ze iya auran ki kin girma kin gandame kingama tsufa din Allah ya tsaremin yarana karki goga musu wannan baqin jinin naki.itadai lamis bata damu ba domin indai irin wannan nentasabaji awajen baba Yasira itadai fatanta ta auri Dameer tasake sabuwar rayuwa.



*****



Zagaye dakinshi yakeyi Ammi yazakimin haka Ammi dakin nemi shawarata, yazanyi da soyayyar Lamis yanzu *WACE TA DACE DANI* Allah kaine mafi Sanin abun boye kai kasan *WACE TA DACE DANI* Allah kamun zabin alkhairi, toilet yayi wanka yadauro alwala yayita jera salloli dan neman zabin Allah, bashi ya tsayar da salla nan ba se uku  saura, nade k'afafunshi Yayi sannan yadaga hannayenshi yafara addua, Allah kamin zabin dayake alkhairi gareni Allah Lamis itace zabin zuciya ta, Dina zabin Mahaifiyata Narasa *Wace ta dace dani* Allah ka zabamin alkhairi cikin biyun nan Allah ka sanya soyayyar wacce take alkhairi a rayuwata cikin zuciya ta haka dai yayita addua harseda uku tayi sannan yatashi Yayi addua bacci ya kwanta badan yanajin baccin ba.

A bangaran Dinama haka ne sedarayi addua sosai ta roki ubangiji alkhairi sannan ta kwanta har bacci barawo Yayi awun gaba da ita.



*****



9:00am amma be tashi ba yanata bacci wayarshi ce taketa ruri, dakyar ya janyota ya kara a kunne muryar lamis ta doki dodon kunnenshi Good morning My Prince,murmushi Yayi sannan yace morning princess. Dadi lamis bazata iya kwatanta yacce takeji ba wai zabin zuciyarta ne yau take waya dashi. Kara godewa ubangiji tayi.

Waya suka taba kadan kafin suyi sallama.cike da kewan juna dan basuso sudenajin muryar juna ba.

Tashi Yayi a gaggauce yashiga yayo wanka ya shirya yafita koh breakfast be tsayayi ba Ya wuce wajen Dr mahad.

Falo ya sameshi yana breakfast.

Yacce yaga abokin nashi yasan yana cikin wani hali kuma koh sanar mishi beyi ba besan da zuwanshi ba, gaisawa sukayi bayan dameer ya zauna. Anya lafiya kake Aboki naganka kamar a hautsine, uhm babu lafiya Dr, innalillahi waEnna Elaihi rajiUn Dr ya furta kafin yace "meyake faruwa kuma? Yayi tambayar cike dason jin abunda yake faruwa.

Uhm Dr ka tayani da addua tun cen dama ina fadama kamar bani da rabo akan yarinyar nan lamis , ka duba yacce nasha wahalar namanta kuma nasameta amma bazata zama mallakina ba sedai iko na ubangiji.

Nifa ban gane inda ka dosa ba kamun bayani sosai, ajiyar numfashi Dameer yayi kafin yace" Ina yer kanin Abba dake rayuwa a India, eh meya faru nagane ta wacce kake ban labarin ta akan kuna samun sabani ko eh ita, tou ta dawo tagama karatun ta wai yanzu itace za'ayima aure da ita har ansa rana nanda wata daya.

What Dr yafada cike da furgici ya mike tsaye kai yadafe yace" innalillahi waEnna Elaihi rajiUn " gaskia kana cikin tashin hankali abokina ana wata ga wata na rasama *WACE TA DACE DAKAI* biyayya ga iyaye samun nasara ne barema kai ita kadai ta ragema , Son zuciya shine burin kowace zuciyar dan adam , ita zuciya batasan rarrashi ba indai akan abunda takeso ne, amma kaciga ba da addua babu abunda yafi karfin addua.

Inayi Kuma dole na k'ara, amma yanzu Dr mene shawaranka ya zanyi da Lamis mezan cemata, ya zanyi kabani shawara kaina ya kulle.

Nima kaina ya kulle bani da shawara dazan iya Baka daya wuce muci gaba da addua muga yacce abun zekaya idan har auran Yer uwarka yazama gasken gaske ka sanarwa da Lamis halin da ake ciki kawai , uhm kai gani kake auran zabin mama ba gaske bane kenan , a'a ba haka nake nufi ba sonake muga meze faru tunda bamusan abunda ke boye ba , ynxu zata yiwu ka sabarwa da lamis Kuma azo auranka da yerUwarka be faru ba .uhmm shikenan Allah yamun jagora ya haskamun lamurana  Dr ya amsa da Amin.

WACE TA DACE DANIWhere stories live. Discover now