LOKACINE
Na Dr,MrsSUMAYYA DANZABUWA
1"Wai yanzu kana nufinn saidai muzuba maka ido muyita kallonka kenan Adnan?wannan wace irin rayuwace ka zabarwa kanka?shekaru daidai dai har uku dayin aure amma ace shiru babu wani labari?kuma idan ance yarinyar nan daka auro juyace kace aa,kadinga kumbure kumbure kenan kanajin haushi bayan kasan sarai ai ba karya akayi ba,ance ka auri yarinyar nan Lubna ko ka dace kaki,kuma dai koba komai mudai munsan kaf danginmu badaga wajena ba bakuma daga wajen marigayi mahaifinka ba babu juya ko daya hasalima bamu tabajin labarin anyi aure a dangi ba mace ta wuce watanni tara bata haihu ba amma kai anzuba maka ido abu yakici yakicinyewa kamar cin kwan makauniya haba"cewar dattijuwar dake zaune kan kujera ta kashe dauri akalla a shekaru zatayi hamsin da biyar,amma dayake cikin gata take da rufin asiri hakan baya wani nunawa a tattare da ita fes take,kuma tsaf tsaf maida dubanta tayi ga wawakekiyar talabijin din dake zaune kan wani makeken tv stand dake a palon,sannan tacigaba da mita,"Umma don Allah don annabi kibar maganganu irin wayannan mu har wane dadewa mukayi bamu haihu ba?Akwai mutanen da sukeyin shekaru goma,ashirin basu haihu ba amma idan lokacin da Allah ya tsara yai sai kiga sun samu haihuwar komai fa hakurine,mu donmunyi shekaru uku ai bawani abu bane bamu dade ba ,ita fa haihuwar nan LOKACINE kuma sai Allah yakawota tukun,mu bamu wani damu ba wallahi bamu matsawa kanmu ba,daga ni har ita Bilkis din tunda munsan bamu isa mubawa kanmu ba bayan Allah baibamu ba komai fa na rayuwar nan rubutacce ne kuma LOKACINE dashi sai Al...."shekeke tajuyo tana kallonshi baki bude,hakan ne yasashi kasa karasa zancen nashi,cikeda mamakin yadda yake mata waazi kamar wata wadda bata ma san metake ba bare ace tasan addini ,"to yimin waazi nace yimin waazi har ni zaka fadawa Allah yace Annabi yace ka isa?to wallahi bari kaji indai daranmu da lafiyarmu nabaku watanni tara kirge yafara daga yau dinnan damukayi magana dakai indai wannan juyar matar taka bata haihu ba zaka auri Lubna babu fashi "amma umm..."bana bukatar raayinka bakuma na neman yardar ka umarni ne nake baka a matsayina na mahaifiyarka uwar data haifeka yarinyar nan(lubna) tana sonka kowa yasani kaine kake kinta ni nataba ganin wannan irin mugun halin ace wai alheri yana bin mutum yana gudu?to ahir kar inji kar ingani nagama magana banason jin wani zance tashi kabani waje kar raina yabaci"tace tun kafin ya tanka bare yakare kanshi,ko yakara wani bayani,gudin ganin bacin ranta tunda yasan akoda yaushe abinda yake hadashi da ita kenan ranta yabaci hakan yasa yatashi yatafi zuciyarshi fal da tunannika yana sake sake.
"Wai don Allah meyake damun wasu iyayen ne?yana zamanshi lafiya da matarshi tsahon shekaru uku kenan basu taba samun koda sabani ba bare sukai karar juna wani wajen amma haka kawai mahaifiyarshi da yanuwanshi sun dauki kahon zuka sun dora mata don kawai bata haihu ba acewarsu juya ce tunda su dai duk danginsu babu wanda yataba daukan tsahon lokaci haka bai haihu ba,kuma shi abinda yake damunshi shine yanada yanuwa hudu duka mata yayye biyu kanne biyu kuma duk sunyi aure sun haihu indai batun jikoki umma take Allah yabata maza da mata to meyasa tadage saiya haihu?ko don shikadai ne namiji?yasha mata wannan tambayar yana tsammanin jin wata ansa mai muhimmanci kuma gamsasshiya daga gareta amma saidai yaji tace kawai naka yayan nakeson gani tunda naga na sauran.
"To wai mutane suna laakari dacewar wasu maauratan tsarin iyali sukeyi suke jinkirta haihuwa saboda basu shirya ba?rashin shiri yana nufin babu isashen kudin dazaa kulada jariri da lafiyarshi data mahaifiyarshi in an haifeshi,wasu kuma matan basuda lafiya dabazasu iya daukar ciki ba alokacin daakeso sai sanda Allah ya tsara,wasu kuma mazan ne,wasu kuma ba tsarin sukayi ba bakuma rashin lafiyar bace jinkiri ne kawai daga wajen ubangiji wanda yasan halinda suke ciki kenan shida bilkis ayanzu tunda dai sunsha zuwa asibiti sau ba addadi tunda umma tafara matsawa don su indan tasu ne zasuyita jira har sai sanda Allah ya tsara musu,bawai don basason haihuwar ba aa sai don suna matukar kaunar junansu,sun kuma yarda da kaddara,rashin haihuwa ba dalili bane dazaisa kaunar dasukewa junansu ta chanja,saidai kash aduk sanda akayi gwajin ana tabbatar musu dacewar lafiyarsu kalau kuma dadin dadawa ita batashan komai bare ma ace suna sane amma dukda haka Wannan baiyiwa Umma ba.
Tun bata damuwa
itama(bilkis) yau da gobe harta fara damuwa saboda ko taro ne na danginsu Adnan din baya baya sukeyi itadashi in an fada musu zaayi taro ko tanason zuwa hanata yake tun sanda taje wani suna aka sata kuka,acikin mutane aka dinga mata gori ana maganganu ana habaice habaice harda hanata daukan yarinyar wai kar tashafa mata juyanci.Zuwa yanzu ta fawwalawa Allah lamuranta tasan shine maiyin yadda yaso akuma sanda yaso,suma wayanda suke da yayan bawai wayonsu bane ko wata dabara tasu tabasu.