LOKACINE

615 5 0
                                    

2

Gyaran gidanta ta kamalla kamar yadda tasaba kullum inta dawo daga aiki,saboda komai yakasance mata  cikin sauki gobe dasafe,don bata dawowa sai karfe hudu inta fita tara nasafe kasancewar wani kampani ne take aikin.
saida ta tabbata komai ya kammala har girki,sannan taje ta fesa wanka taci kwalliya yadda tasaba don tarbar maigida saboda tasan duk inda yake yanzu yayo gida kasancewar shi dankasuwa kullum agida yake maghrib,saidai ko idan hold up yarikeshi,hakika Bilkis indai tsabta ce da kwalliya daduk wasu nau ika da sirrika na zama da miji baa magana don duk abubuwan datasan idan tayi zata farantawa Mijinta yi take,kuma duk inda ake tunanin cikakkiyar mace takai,ga addini,ga kyau ga sura mai kyau,banda dai wannan rashin haihuwar babu abinda mijinta Adnan yanema yarasa don shi kanshi Adnan din yasan duk abinda namiji yake  nema dai a wajen mace Bilkis tabashi,banda haihuwa wanda yasan ba yinta bane yin Allah ne,don haka yake kara so ta a kullum.
wayannan dabiu nata hade da halayyarta ta kirki sune suke kara kaunarta azuciyar mijin nata.

Kamar yadda  tasaba tarbarshi  aduk sanda  yadawo yauma haka tayi cikeda farinciki da annushuwa  ta rungumeshi shima ya mayar mata tareda manna  mata kiss a goshi saidai kallo daya tamishi tasan yana cikin damuwa kasancewarta  mace wadda ta gama karantar  mijin nata tsab,"Soulmate meya faru lafiya naganka  haka ?"ta watsa mushi tambayar cikin sassanyar muryarta fuskarta daukeda damuwa,"wato duk yadda yaso ya boye damuwarshi  karta gane saida taganoshi  kamar dai koda yaushe" yace aranshi,murmushin dole ya kirkiro  don bayason ma ya fada mata yadda sukayi da umma dazu duk da yasan tanada fahimta da juriya da tsananin hakuri amma wannan karon yasan sai ahankali don tunda ake takurar da matsawar akan haihuwar umman bata taba mishi irin kalaman datayi na yau ba,datace ta kayyade musu lokaci kuma dole ya auri lubna in waadi ya kare,hakika yasan wannan abune dazaisa zuciyarta ta sosu ba kadan ba tunda itama cikin damuwa take atitur cikin shan magunguna sukeyi shida ita duk inda dayansu yaji  labarin maganin haihuwa saiya nemo amma shiru hardai wani likita ya gargadesu akan shan magunguna barkatai ita haihuwa baa mata haka lokacinta inyayi batareda kasha komai ba zatazo,"kayi  shiru mijina"ta katse  mishi tunani,bayan sun zauna kallonta yayi yaji tausayinta ya kamashi hakika yasan bilkisu masoyiyarshi ce ta kwarai mai kaunarshi tsakani da Allah inba haka ba ko wulakancin da cin mutumcin da danginshi suke mata hadeda gori dawatace datuni sunsa ta fusata ta maida martani koma tace tagama zaman auren amma abune da samsam bata taba yunkurin yiba  hasalima bata  taba tanka musu saidai in an mata din tashiga daki taci kukanta  ya rarrasheta.

Ganindai ba kyaleshi zatayi ba da tanbayar  ne yasa ya labarta  mata komai don bazai iya mata karya ba,ai wasu zafafan hawaye ne suka fara zubo mata dabata ma sani ba,"aure fa kace,?"tace tareda mikewa dukda dai tun kwanaki ta lura da take takensu tasan dole lokaci irin wannan na nan zuwa tunda aduk sanda maaurata suka sami jinkirin haihuwa mijinsu yakan kara aure idan bashida raayin hakan kuwa kamar Adnan akan tursasa musu yin hakan ita kuma mace koba ita bace mai matsalar tana iya hakura tazauna dashi,"saboda Allah yamana  jinkiri shine zaka kara aure haba Adnan kasan banida damuwa aduniya sama da wannan acewai ka kara aure saboda gazawata,ace wai yau bawai don raayinka zaka kara aure ba sai don nagaza Adnan?"tace cikin muryar kuka,kamata yayi ya zaunar  da ita kan kujera,"wallahi ko kadan wannan ba idea ta bace kinsanni ai,rabin raina ba fa ina nufin ni na bijiro da zancen auren nan ba wallahi umma ce,kema kinsan nasha fada miki ko har karshen rayuwarmu zamu kai babu haihuwa bandamu ba saboda bazan iya son wata mace ba  ma har inaurota inba keba don bazan iya adalci ba ina gudarwar  kaina azabar ubangiji Habibty,babu abinda kika rageni dashi wallahi I love you dearly"kallonshi kawai take tama rasa mezatace sai aikin hawaye,"wai tabamu nan da watanni tara id...."to mu zamu bawa kanmu haihuwar kenan ?sanin kanka nefa har kwana  nake ina salloli ina adduoi bana bacci akan rashin haihuwar nan wane kokari ne banayi?naga karewa ma yin IVF dinmu biyu amma was it a success?inbanda wahala da tashin hankali me muka fuskanta wannan bai ishemu isharar Allah yana sane damu ba mu hakura,kuma meyasa bazaka fuskantar da ita ba cewar komai LOKACINE amma ace anbaka lokacin abinda  bakada  tabbas akai  kuma kahau kai kazauna  haba Adnan, ya Allah ga baiwarka"tace cikin kuka tareda dafe kanta,hakika yasan ranta yabaci tunda har  take furta maganganu irin wayannan to amma yazaiyi yasan anmata laifi anmata ba daidai ba,duk yadda ya kaiga fahimtar da ita akan ta fuskanci  lamarin nan bilkis takasa fahimta don idanunta sunriga sun rufe.

Bilkis macece mai matukar hakuri kowa ya shaida don duk rashin mutumci da takurar da dangin Adnan suke mata bata taba sanarda kowa ba ko mahaifiyarta data kasance kamar kawarta aminiyarta saboda tsabar kusancinsu,amma hakika yau kam tana cikin tashin hankali don batamasan yazatayi ba,don bawai kishiyar bace bata so aa dalilin yin kishiyar ne yake tada mata hankali saboda tasan duk ranarda Adnan yakaro aure har akayi saa macen tasamu ciki to fa tasan karshen wulakancin dabata taba gani ba shi zata gani don hatta Adnan dinma tasan ba lallai ya raga mata ba tunda dan adam ne don bashida buri a rayuwa tun kafin suyi aure daya wuce na yaga jininshi shima kawai dai don Allah bai basu bane shiyasa yake hakuri kuma fargabarta da tsoronta karya juya mata baya yadaina sonta duk soyayyar dayake mata ya dauketa chak yamaidata kan uwar yarshi ko danshi da abinda ta haifa don tabashi abinda ita takasa bashi,wayannan abubuwan su suke tada mata da hankali suke sata cikin wani yanayi.

LOKACINEWhere stories live. Discover now