LOKACINE

290 5 0
                                    


3

"Don Allah kibude kofar nan,kibar kukan nan haka kiyi hakuri"yacigaba da bugu,don tunda tashige dakin ta kullo take aikin kuka taki budewa ma bare ta fito tana jinshi yanata magana don ita wannan alamari yagama bata mata rai tunda take dashi bata tabajin rashin son ganinshi ba ko jin wash kalamanshi sai yau,tayaya ma zaa raina mata wayo bayan asibitin nan tare suke zuwa kuma an tabbatar musu dukansu basuda matsala to don meyasa ita kadai zaa takurawa ai in gaskiya zaabi bai kamata amata abinda ake mata ba"Don Allah kibude ki tausaya min wallahi ba fada ta bace amma tunda abin hakane zanje in roketa abar maganar nan haka don bazan juri ganinki cikin bakinciki ba,wallahi nima baso nake ba umma ce"yace cikin muryar kuka,karo nafarko tunda take dashi data taba jin kukanshi harda shesshsheka hakika Adnan indai jarumta ne ba baya ba amma wai yau shiyake kuka kamar karamin yaro sakamakon jin sautin kukan bilkisun shi Allah sarki.
Saida taji shiru har tayi tunanin ma yabar wajen sannan tazo tabude kofar ga mamakinta yana nan ya baje yana hawaye koda ya ganta saurin tashi yayi tareda rungumeta  itama rungumeshin tayi suka cigaba da  kuka babu mai rarrashin wani.
"Zansan duk yadda zanyi inga baayi abinnan ba(auren)don bazan taba  jurar ganinki cikin yanayi mai tayarda hankali ba irin wannan ki yafemin"kara rungumeshi tayi tsam tsam kamar wani zai kwace mata shi,"yanzu shikenan idan yayi auren haka wata zata dinga rungumeshi itama innalillahi wa inna ilaihi rajiun"tunaninnika kala kala suka dinga mata yawo akai,"don Allah don Annabi kiyi hakuri kibar kukan nan haka babu abinda zai faru inshaallah kinsa ni maisonki ne akoda yaushe bana burin yimiki abinda zai bata miki rai komin kankantarshi kuwa,duk abinda bakyaso ina kokarin kiyayewa kiyi hakuri zan sameta musake magana h.."Allah yasa taji don nasan wanna abune data dade tana buri fasashi saidai wani ikon Allah Adnan ka...."zan lallabata wallahi dazun ma nanu mata na amince ne kawai don naga ranta yabaci amma abune da k...."Adnan Allah yasa dai tajika ni ban hakanaka kara aure ba dalilin karin auren ne yake damuna saboda nidakai munsan ance mana lafiyarmu kalau to meyasa ake daukan laifin akoda yaushe ake  doramin?why me?kawai saboda nice macenni nake da alhamin dauka da rainon ciki? H...."takasa karasawa,haka yadinga mata kalamai masu dadi yana lallabata yana kwantar mata da hankali.

"Umma Don Allah don annabi abar maganar nan haka,wallahi tunda kikamin zancen nan (na auren lubna)hankalina ya kasa kwanciya kwata kwata banajin dadin jikina da ruhina gabaki daya,infact kwanan tashin hankali nayi,kuma yarinyar nan banasonta wallahi umma,kinsan imatukar kaunar  matata fiyeda yadda kike tunani don bana iya yiwa kowace mace kallon mace inba ita ba haihuwar nan kuma ta Allah ce bamu isa mubawa kanmu ba sai Allah yabamu,mexai hana mu yarda da kaddara dakuma fatan jinkirin nan yazama alkhairi agaremu,yanzu idan kika matsa saina auri lubnan itama tazo bata haihu bafa?don Allah don Annabi kiyi hakuri kibarni nacigaba da zama da Bilkisu ita kadai wallahi a tsarin rayuwata babu na auren mata biyu bansan yadda zanyi ba"yakarasa zancen tareda zaro hankicinshi daga aljihu ya share hawayen dake tsiyayowa daga idanunshi"kagama?nace kagama?"tagyara zama,"to Adnan bari kaji idan kaga baka auri lubna ba to nice na mutu,ko kuma kai ko ita,wannan dalilin ne kawai zai hana ayi auren nan amma zance yana nan daram babu fashi ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi kasawa ranka salama domin kuwa aure kamar anyishi ne angama muddin waadin dana daukar wa matarka yacika bata haihu ba kuma dakake zancen wani ita kadai kake iya yiwa kallon mace matar taka har wata macece?nace har wata macece?ai  duk macen dabata haihu bata  cika mace ba don kaji in gaya maka,mtsw zancen banza ma kenan hardawani bakasan yazakayi ba idan ka auri mata biyu kana magana kamar wani sakarai ba namiji ba,inka bani haushi ma sai ka rabu da ita(bilkis din)"saurij dagowa yayi yafara kallonta,"eh kalleni dakyau nafada inyaso inga karewar hauka ai kasanni kasan halina ka kiyayeni fa,idan kanason kacigaba daganin bacin raina kasake tadomin  da zancen banzan nan kaji"tace tareda mikewa tashige ciki tabarshi yana kuka kamar karamin yaro "don Allah don Annabi umma karkimin haka nifa danki ne meyasa bakyason farinciki na"yacigaba da magana shi kadai don kuwa ita tama kullo kofarta taciki kanshi akeji yasan yana tsaka mai wuya don yayyenshi mata guda biyu dasauran kannenshi duk basuda wani amfani inma yace zai fada musu don duk bakinsu daya ga yanuwan mahaifinsu duk babu sun rasu gidansu umman kuma itace babba sai kannenta suma mata duk kanwar ja ce don haka babu wajen wanda zaije yakai kukashi yadan sami sassauci,"wai wannan wane irin abu ne to kodai zai dauke bilkisun ne subar garin koma kasar gabaki daya tunda ai sai anganshi ne zaayi mai zancen auren wata lubna,"yacigaba da zancen zuci.

Yana fada mata zancen yana kuka harda shessheka zuwa yanzu itama tafara hawayen saboda tasan halin mijin nata da jarumta da dauriya ba karamin abu bane zai saka shi kuka hakika zuwa yanzu ta tabbattar  dacewar wannan aalmarin auren baya goyon bayan shi ko kadan don da tana kokonto,zancenguduwar da  barin kasar yataso mata dashi akan suje cen inda babu wanda yasansu sufara sabuwar rayuwa,"aa kayi hakuri kadauki abinda yake faruwa damu a matsayin kaddara uwa uwace kabita inshaalahu bazaka taba ganin ba daidai ba ta hango maka abinda kai ko ni  bamu hango ba shiyasa ta dage kaunace takesa uwa ta tursasa danta yin abinda takeso ka guji bijirewa umarninta ka yarda da zancen auren nan ni na fawwalawa Allah komai nasan babu dadi amma babu yadda zanyi inasonka Adnan amma mahaifiyarka tafini sonka shiyasa take kokarin nema maka farinciki fatana dai kawai Allah yasa ka kasance nai adalci a tsakaninmu haihuwa kuma Allah yabaku zuria dayyiba Amin"takarasa zancen hawaye nazubo mata itama,rungumeta yayi yafashe dakuka hakan ne yasata tsananta nata kukan itama "wallahi baason raima zanyi  auren nanba Bilkis sai don bin umarnin mahaifiya har abada ke kadaice macen dazan taba so bazan taba iyason wata mace ba inba keba"hakika tasan mijin nata ba karamin sonta yake ba don ko a inane bayashayi bare kunyar nuna hakan akoda yaushe farincikinta shine burinshi.

LOKACINEWhere stories live. Discover now