4Ko dasuka kwanta kasa bacci tayi sai juye juye take ga tunaninnika iri iri dasuka dinga zuwar mata hakika tunda dangin adnan suka fara takura mata akan lamarin rashin haihuwar nan bata taba fadawa kowa agida ba hasalima banda aminiyarta laura babu wanda yasan komai,amma yanzu lokaci yayi dayazama tilas iyayenta susan me ake ciki barin ma mahaifinta datasan yafi kowa kaunarta kuma dadin dadawa mutum ne mai jajircewa wajen ganin ya kwatarwa wanda aka zalumta yancinshi koda yasanshi kuwa ko bai sanshi ba to bare ma ita,tayi hakurin dazata iya Allah ma yasani tazata abin mai karewa ne ashe bahaka bane taso ayi komai agama bareda iyayenta sunji ba amma yanzu kam bazai yiwu ba don ta fuskanci ma alamarin harda rainin wayo aciki,to inbdanda ma anraina mata hankali ya zaayi ace zaa sata agaba ita kadai metayi? idan hakane suma itada iyayenta su saka adnan din agaba mana wannan fa bakomai bane facs zalumci da rashin gaskiya karara ance dukansu lafiyarsu kalau to meyasa zaa sakota agaba"taja dogon tsaki, "kai bazai yiwu ba tace afili tareda tashi zaune kallonshi tayi taga yana baccinshi hanian tasake kallonshi wani kishinshi ya turnuketa wato nan bada dadewa ba ake nufin zasu fara raba kwana da mijinta itada wata agaskiya duk abinda zai faru saidai yafaru hakika yau ankaita bango babu tantama itama dole tasanar da iyayenta abinda ake ciki don tayi karar iya yinta Allah ma yasani duk hakurin datakeyi baa gani don haka bazata iya kashe kanta da bakinciki ba ciwon zuciya yakamata abanza ta mutu acigava da rayuwa.
Tashi tayi tashiga bandaki tayo alwala ta tada sallah domin neman saasauci akan lamarin don wannan dabiarta ce aduk sanda tashiga damuwa kowani kunci,kukan data dingayi tana sallar dakuma bayan ta idar abin saiwanda yagani farkawa yayi yaganta kan abin sallar tana adduar dabaisan metake fada ba yadai hango hawaye kawai yi yayi kamar baigantaba yajuya saboda bayaso ya mata magana gudun kada ranta yacigaba da baci don baimasan mezaice mata ba.
A kan abin sallar bacci ya dauketa."Don Allah don Annabi ki saiki ranki wall..."wane ran zan saka wai?don Allah don Annabi ka barni naji da abinda yake damuna "ta katseshi,"don Allah babe kiyi hakuri wallah duk abinda bakyaso nima bakincik nake dashi h..."nazata mungama maganar nan abar tado da zance kawai"tace don ganin anbar maganar don tasan yanzu saiya fara koke koke itama datake shirun fita sai yasa tafita arikice.
Ai koda ta fita ba aikin ta tafi ba gida tayi karo na farko tunda sukayi aure data taba zuwa gida baisani ba takuma yi hakan ne saboda gudun abinda zaije yadawo don tasan muddin idan ta fada mishi zata gida to bazai bari ba don yasan dole kararshi zata kai.
""Mai gado lafiya dai ko irin wannan shigowar sassafe haka kuma ranar aiki?"cewar mahaifinta Daddy wanda ya kasance tsohon maaikacin gwamnati daya rike mukamai da dama sannan mutum nagari mai taimakon jamaa a halin yanzu yana hutawa ne agida sakamakon ritaya dayayi sunan mahaifiyarshi ce da ita bikisun kasancewarta yarshi mace daya tilo yayyenta hudu maza kannenta biyu maza shiyasa yake kiranta maigadon zinari atakaice kuma maigado hakika yana matukar ji da ita kai bashi kadai bama kowa nagidan saboda kasancewarta mai kirki da nutsuwa hasalima bazaku tabaji ance tayi fada dawani ba batada abokin gaba.
Ai kuwa an sosa mata inda yake mata kaikayi take ta fashe da kuka "aa subhanallahi"cewar daddy tareda ajiye kofin shayinshi,"ina fatan dai bawani abu bans yasamu adnan din ko?girgiza kai kawai take alamun babu komai juyin duniyar nan taki magana sai kuka mahaifiyarta yaje ya kirawo don yakai kololuwa wajen rikicewa,ai tana ganinta ta tashi ta rukunkumeta ta cigaba da kuka saida akayi rarrashi iya rarrashi sannan aka samu tafadi komai tundaga farko har karahe "amma shine duk tsahon lokackn nan kika zauna kina shanye wannan abin?haba maigado "cewar mummy "wallahi hakuri kawai nake dasu mummy shi adnan din bashida matala mamanshi da yanuwanshi ne wallahi "duk bama wannan ba ni rashin adalci da sanin yakamata na tsana a raywata wallahi wato shi shine dan so koo?ko ke cemusu akayi daga sama kika fadi?shi akafi damuwa aga nashi yayan mu bamason muga jikanmunko? Shiyasa har zaa aura mai wata to indai hukuncin dasuka yanke kenan nacewar saiya kara aure akan matsalar dabatakiba ke kadai bakuma ke kika dorawa kanki ba to tabbas kema saidai ki sake wani auren ki auri wani namijin sai mugani idan da dadi zancen banza ma kenan"cewar mummy cikin fadaa "aa nafisa bazayi haka ba yaduk zamu taru muzama daya ne mu aikata shashanci? wannan ba daidai bane ai,karmu nemi mu haramta abinda Allah ya halarta,tunda dai su sun nuna basu san kaddara ba basu kuma yarda da ita ba baikamata mu ma mu biye musu ba indai mai gado tanada rabon haihuwa a duniya komin daren dadewa zata haihu duk agama jeka kadawo din ni na yarda komai lokacine kuma mahakurci mawadaci,"amma daddy fa wannan zalumci ne don bakaga irin abinda sukemin ba musamman idan taro ake k...."shi mijin naki yana miki?ko ba yanzu kika ce babu ruwanshi ba shi?"daddy ya katseta shiru tayi ta kalli kasa,"nace shi Adnan din shima ya juya miki bayan ne?"fashewa tayi da kuka,tana girgiza kai alamun aa"to kinga mijinki yana kaunarki kuna zamanku lafiya umarni ne na mahaifiyarshi dabayaso ya kaucewa saboda ba sabon Allah bane donhaka kiyi hakuri zama da abokiyar zama bawani abin tashin hankali bane kowacce da halinta zata zauni kuma kinsanni dai inda yana zalumtar ki shi dakike zamanshi da bazan bari ba amma tunda shi ba matsalarshi bace ta mahifiyarshi ce kiyi hakuri komai mai wucewa ne h..."amma shikenan haka zaa zuba ido acuci yarinyar nan g...."Nafeesa ya kikeso muyi?so kike muce yasaketa akashe auren ta auri wani dabamu da tabbas akan nashi halayen ko na iyayenshi? what if ta auri wanin shima akazo bata haihun bafa sukuma sunmafi wayannan din kwazzabawa"dukda haka dai Alhaji ni abinda nake cewa shine tunda dai shi da iyayen nashi basu yarda da kaddara ba kuma dadin dadawa bacewa akayi yarinyar nan tanada wata matsala ba kowa yasani to meyene zaa ce dole ita saita jure zaman gidanshi har ya auro mata wata da Yarinyar nawa take da har zaa mata kishiya?mummy tace cikin fada,"kiyi hakuri nafeesa na fuskanci komai mu dauki wannan abin a matsayin jarrabawa abu dayane bazan yarda dashi ba shine ace an auro wata tazo ta kuntata wa yata data samu acikin gida wanan ne bazan dauka ba "to indai hakane kuwa yazama dole ka kirashi kaja mai kunne ko a zauna damu da nashi iyayen ayi yarjejeniya kuma dole arabamusu gida ehe in...."abin baikai nan ba basai an zauna dasu ba amma zan zauna dashi mijin nata kiyi hakuri,"mamana ko daina son mijin naki kikayi kinji dai irin hukunci da mahaifiyarki takeso mu zartar ya kike gani?,"Daddy ni basonshi bane banayi kawai dai auren daakace yayi ne akan laifin daba nawa ba banaso tunda nima ba laifina bane"tace cikin kuka "kiyi hakuri ki dauki abinda ke shirin faruwa dake a matsayin kaddara b..."Alhaji bawai ina katse ka bane tunda kace tayi hakuri zata yi hakuri akma fa ka kirashin kamar yadda ka fada ku zauna ayi yarjejeniya don babu zancen hada gida yarinyar nan da gatanta itama muna son kayarmu don mafi akasarin tashin hankali da rigima na auren mace biyu dalilin shi shine hada gida idan kuwa kowacce gidanta daban g..."tom nafeesa zan mai magana inahaallah adinga bin rayuwa ahankali"dahaka dai daddy yadinga kwantar mata da hankali yana nuna mata komai bakomai bane atakaice dai bataje aikin ba kuma bata bar gidan ba har saida ya kira Adnan din sukayi maganar akan araba gida kuma yayi adalci yakuma ce yaji ya amince .