LOKACINE

86 3 1
                                    

6

Jiki a sanyaye yafito yama rasa meke mishi dadi hakika umma mahaifiyarshi ce yana kaunarta kuma yasan itama kauna ce tasa take abinda takeyi to amma kuma,tunda yace bayaso sai ahakura mana shi aganinshi ai yakamata ace albarkacin kaunar datake mishi tunda yace bayason abinnan ai yakamata ace tabawa zuciyarta hakuri,takuma tausaya mishi,ta janye wannan magana,yakuma tambayeta sau ba adadi ko wani laifi Bilkis din tamata dukda dai yasan babu amma dai wai sanin halin dan adam akoda yaushe saidai tace babu laifin data mata rashin haihuwarta ne kawai laifinta.
Wani in yaji zancen sai yazata rashin ilimi ne yake dawainiya da umman,mai karatu babu wani rashin ilimi  da iliminta sarai takuma san metake shidai Adnan yabarwa zuciyarshi cewar kawai Bilkis dince tadainaso tunda kuwa ai kafin ya aurota dabayan aurensu tana nuna mata tsantsar kauna da ita da duk sauran yanuwanshi abin dayaje daure mishi kai akoda yaushe shine  to meyasa komai zai chanja?.

Wai Wacece lubnah?

Lubnah dai yace daya tilo a wajen mahaifiyarta wadda takasance aminiyar umma,don tun yarinta suke tare ga gida ga gida,yayyenta maza hudu sai ita ta karshe kuma mace daya tilo kafin haihuwarta babu irin buri da addua da kwallafa rai da mahaifiyarta batayi ba akan ganin tasamu ya mace saboda tana tsananin kaunar haihuwar mace ganin aminiyarta ummansu adnan ita kuma Da mata tafara tunda saida tayi mata biyu sannan tayi adnan sannan takaro wasu biyun,to so da kauna datake nunawa akan yayan aminiyartata abin sai wanda yagani,ni kuwa nace Allah daya gari banban,wasu suna cen kamar zasuyi me akan Allah yabasu yaya maza,wasu kuma matan sukeso,Allah mai iko Ashe dai kowa da abinda ya dameshi.
Allah buwayi gagara misali cikin ikonshi ya azurta ta da lubnah farincikin data tsinci kanta ciki abin sai wanda yagani don bazai fadu ba cikin wannan dan rubutun,hakan yasa ta dauki kaunar duniya ta dorawa yarinyar, yasa ta taso cikin shagwaba,ba kwaba tunda mahaifiyarta bata mata fada kuma idan tana nan bawanda ya isa ya tsawatar mata,kaf yayyenta bawanda take shakka ko tsoro wanda kuwa gabaki dayansu babu wanda yabata kasa da shekaru biyar amma duk ta rainasu saboda tsamu goyon bayan mahaifiyarta hakan neyasa take abinda taga dama bawanda ya isa yayi wani abu saidai idan mahaifiyar tasu batanan su samu su dan kwadeta suyi amfani da damarsu amma fa idan Taji labari ranar mutm yashiga uku don har furuci tayi akan duk wanda yasake taba mata yarinya cikn yayyen nata Allah ya isa.
mahaifin lubnah shima yana tsananin kaunarta amma ba kauna irin ta mahaifiyarta ba don shi mutum ne jajir tacce mai kuma son horo da ladabtarwa hadeda ganin yayanshi sun sami tarbiyyah tagari,akoda yaushe yakan jawa matar Tashi kunne akan tarbiyyar yarinyar dubada yadda take sakaka babu kwaba tunda daga baya data fara girma ya fuskanci kanta na rawa,dole ya tashi tsaye akanta yadaina mata wasa don karta lalace,har takai ga yafara dukanta wanda ba dabiarshi bace,saida yayi maza har hudu kafin ita bai taba dukan kowa cikinsu ba saboda idan ya tsawatar sunaji amma ita babuwanda ya isa taurin kai da gardamar masifa,da sannu tafara jin tsoronshi tafara saituwa bata shayi ko kunyar yin rashin kunya agaban kowaye amma dataga dagaske yake jikinta yafara gayamata nutsuwa tafara saukar mata,hakan ba karamin sabani ya janyo ba tsakaninshi da mahaifiyar tata Aisha ba,inda tadinga ikirarin lallai bayason yarinyar tunda ya ke matsa mata,har in yana mata fada ko dukan tadinga kareta,sai yazamto cewar idan yana nan batayin shegantaka in aka ganta kamar ba ita ba,amma duk ranar daaka ce yasa kafa yabar gari kasancewar shi mai tafiye tafiye to fa sai Yanda Allah yayi,har cewa take dama tasan duk duniya kowa ya tsaneta mahaifiyarta ce kawai take kaunarta.

Akwana atashi har takai matakin senior secondary school tanata rawar kai dai sama sama idan baban bayanan saboda tasan tanada goyon bayan mahaifiyarta har ila yau kuwa yayyenta kullum mahaifiyar nuna musu take basu isa ba,Allah cikin ikonshi tana matakin karshe na karatun sakandire Allah yayiwa baban rasuwa,mai karatu kuwa yasan abinda zai cigaba da wakana domin kuwa dai takoma cin duniyarta ne da tsinke tanata abinda taga dama makarantar ma so tayi ta daina zuwa ana gab da fara waec,ga mugayen kawaye datake tarawa harda maza babu abinda yadameta.

Saboda rashin maida hankali wajen karatu tasa sharholiya azuciyarta da holewa zancen danake muku yau shekarun lubnah uku da kammala karatun sakandire amma fa bata cigaba ba saboda takasa cin jamb,kuma baba yabar wasiyya ko bayan ranshi bai yadda Abari tafita kasar waje ba dasunan karatu,kamar sauran yayyenta,dole aka hakura dukda dai mahaifiyar tata taso fatali da wannan wasiyya ganin cewar yar tata yakamata ace tasamu ilimi koda zuwa matakin degree ne kawai,amma kasancewar kabir babban yayansu lubnan dashi akayi zancen shiyasa aduk sanda umman ta taso da zancen yake kokarin dakatar da ita yake kuma nuna mata girman wasiyya dakuma abinda take shirin aikatawa sanin halin lubnah.
Tanada kimanin shekaru 20 yanzu,amma takasa cin jamb,waec da neco ma umma biya tayi aka bata,jamb dince dai ta gagara,islamiyyah kuwa koda yan ajinsu suka tashi sauka cire sunanta akayi saboda malam ya tabbatarda bata zuwa makaranta,atakaice dai inta taho islamiyya yawonta take tafiya,sai sanda taga dama,idan aka ganta sai arantse  wata yar shekaru 28 ko talatin ce, saboda yanayin jikinta tunda ba karamin jiki bane da ita,kirjin nan acike tap,haka bayan shima,kyakkyawa ce ba laifi hakan nema yasa take saurin sace zuciyar duk namijin data hadu dashi musammamn dan sharholiya irinta.

To kuma wai umma tana sane da duk wayannan munanan dabiu na lubnah,shine take so tahadata da Adnan wanann abinne yake cimishi tuwo a kwarya,bayan yarinyar tazama
celebrity ta fannin rashinji da rashin mutumci kowa yasanta,in tana rawa da waka a tiktok kuwa kamar tarasa mafadi,waye zaiso ya auri ballagaza wadda batasan ciwon kanta ba?wannan ce mutum zaiso tazama uwar yayanshi?.

"Waini Adnan dinnan meyake nufi ne dani Mama kunce kun gaya mishi zaa mana auren nan  nan da dan lokaci kadan amma bantaba gani yazo wajena dasunan zance ba meyake nufi ne ko bayaso na ne?tace cikin shagwaba tanata danne danne a wayarta kan akan cinyar mahaifiyar tata,"wane irin bayasonki baby? (yadda mahaifiyar ke kiranta)waye zai ganki yace baya sonki?zan kira Labiban(umman Adnan)dai naji meyake faruwa don tun rannan tacemin zaizo amma banganshi ba.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 26 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

LOKACINEWhere stories live. Discover now