LOKACINE

203 5 3
                                    

LOKACINE

5

Koda suka taho hanya rasa ma mezaice mata yayi tunda daddy cewa yayi yatasata agaba su tafi daya daga cikin kannenta zai taho mata da tata motar anjima,hakika yasan bashida ikon jin haushi don yasan dole ta rasa yadda zatayi ne shiyasa tafada agida tunda bata tabayin hakan ba,yasanta macece mai juriya wadda bata kaunar taga mace tana bata mijinta wajen mutane to amma yazatayi?Yasan dolene yayi hakuri don kuwaanmata laifi,suda sukayiwa junansu alkawari tun kafin aure bazasu taba kai karar junansu wajen iyaye ba duk rintsi kuwa komin damuwar dazasu shiga zasu sasanta kansu,amma  sai gashi yau  saboda abubuwa sunyi tsanani an karya alkawari tabbas yauda gobe bata bar komai ba.

Bawanda yace da kowa komai duk sunyi shiru ita ta kalli window tana kallon duniya tana tunannika kala kala sautin karatun alqurani ne kawai yake tashi a motar.
"Kinason cin wani abu ne babe?"yace lokacin dasuke gab da wani Restaurant dasuke zuwa hakika yasan tana matukar son abincinsu,girgiza kai tayi alamun aa,"kiyi hakuri habibty ko shawarma ce in karbo miki nasan kinaso"batareda yajira ansarta ba yayi parking yafita,baijima ba yadawo suka wuce gida.

Washegari ma kasa fita tayi haka kawai takejin babu dadi ba abinda yake mata dadi komai ya fitar mata arai hakika tana cikin damuwa Shiryawa tayi ta tura mishi text akan ta tafi gidan laura don zaman ya isheta tunda ko aikin ma takasa zuwa,"Allah ya kiyaye hanya adawo lafiya"yaturo mata da reply don baya taba iya hanata fita bugu da kari yanzu lokaci ne daya zama tilas ya kara tarairayarta dakuma lallabata kuma yasan ita din bama mai yawon bace indai ba aiki ba ko gidansu saiko gidan lauran sune wuraren zuwanta.

"Ki saki ranki Bilkis ki kwantar da hankalinki h...."nifa ba wai sakar ran ba Laura wallahi inda ace inada da ko ya don Adnan yace zai kara aure ke kanki kinsan nice mai karfafa mishi gwiwa kinsan banida irin wannan tunanin nawai don miji zai kara aure in tada hankali in haukace wallahi kwata kwata bahaka nake ba aikinsanni,wannan baya cikin tsarina kawaidai  bakincikina laura ace wai yau mijina kara aure zaiyi saboda na gaza tawanni fanni na rayuwa,saboda na kasa bashi da ko 'ya ke bakya hango irin bakincikin dazan shiga nan gaba?"da wannan da wannan"cewar laura tareda gyara zama,"ke Nifa shawara ma nakeso nabaki kawai dai nasan halinki ba lallai ki dauka ba don wani lokacin baa miki gwaninta"takara,"menene don Allah fada min wallahi laura hankalina a tashe yake ina tsoron adnan ya wulakanta ni in zama bora ki fadamin inji"tace a kage tana jiran taji mai lauran zatace,"to bawani abu bane illa kibari wani  abu ya shiga tsakaninku ina nufin na muammular aure yau dinnan ko gobe  sai a nemeki arasa h..."anemi arasa kuma?ta yi saurin katseta"kash ki bari inkai aya mana iins nufin  nekitafi wani wajen yadda adnan din bazai dinga ganinki ba bama shi kadai ba kowa ma sai bayan kamar wata biyar haka sai kidinga ciko akwai irin cikin robar nan da yan film suke amfani sai kowa yazata ciki ne bayan wata 9 saiki dawo amma kafin nan zamuje gidan marayu mu nemi dan jariri mace ko namiji wanda dai  duk kikeso kodayake kinsan sai anyi booking wai, inyaso ana kawowa sabon jaririn  ko jaririyar sai muje mu karba saiki cire cikon dasunan kin haihu h...."mtsw meye haka laura mekike cewa ne?zancen ya isheni haka don ni banma fahimci wannan wace irin gurguwar shawara bace mara amfani dakikeson bani wani in gudu inyi waye to mekenan akayi kafin indawo na tabbata yayi aurenshi har matar ta haihu sai me yayi saura kuma?,"to arage ace yanzu kinada cikin har yayi wata biyar kinga wata hudu kawai zakiyi ki dawo don kinsan ciki kala kala ne cikin Rufaida(babbar yarta),saida nakusa wata shida yafito k......"ke kanki kinsan wannan tatsuniya ce ba abu bane maiyiwuwa babu abinda na tsana kamar adopting yaro inda zanyi ai da tuni nayi bawai ina bakinciki bane inyi adopting inkula da marayu su zama wani abu nima insamu lada a a sai don labarin da mummy tabani na wahalar da makociyar mu tashiga, itama shekaru tashafe bata taba haihuwa ba suka yanke shawarar adoption itada mijin kasancewarshi mai kudi tunkafin fa a haifemu abin yafaru,wallahi laura sai lokacin da mai gidan yarasu akazo rabon gado,shi  yaron bai taba sanin ba babanshi bane anyi anyi dasu su fada mishi tuntuni sukaki saboda gudun kada yashigahalin damuwa da tashin  hankali saboda kaunar dasuke mishi wallahi  yaron nansaboda yaganshi shi kadai agidan nan yazata shi kadai ne dansu saida akazo rabon gado aka fayyace mishi komai ke bakiga tashin hankali ba abu yayi abu yaro kamar ya haukace dole sai anbashi gado gashi irin mayen kudin nan ne da abin duniya akace zaa bashi wani abu aciki kasancewar yanuwan mutumin maza suna nan kuma sunada yawa ya kwantar da hankalinshi yace bai yarda ba dole abashi komai duk yadda akayi akan ya fahimta yaki dole aka daukeshi aka kaishigidan marayun da aka daukoshi aka budo mishi record dakomai yagani yayi kamar ya hakura ke yadinga lallabowayana yiwa matar da yanuwan mutumin barazana saiya kashesu ita fa marikiyar tashi datayi wahalarshi tun yana jariri amma yamanta dakomai saboda kudi idanunshi sun rufe  dakyar aka samu aka kamashi aka kulleshi tunda har ya zama rikakken dan
Taadda,hmmm haka in macen cema kika dauka sai ahankali wasu haka suke girma suyita duniyanci tunda wasu gado sukayi to yara ne wasu tsintosu ma akayi uwar ta yar a shara ko kwata  kinga history din yaro akwai tashin hankali  to gaskiya wannan abin dawasu  labarun ma damukaji daga ni har adnan din shiyasa adoption yafita a ranmu dukda dai baduka mutane suka taru suka zama daya ba amma dai to be on the safest side dole muka hakura don haka nagode amma wannan bama shawara bace ki kawo wata yar rainin wayo" tace tareda watsa mata harara irin tasu ta kawaye,"tab lallai  an sha tashin hankali kodayake haka yan adam suke dama wasu kayi musu rana sumaka dare Allah dai yakare" nariga  na fawwala komai ga Allah Allah ne zai kawo min mafita tunda dai ance zaa raba gida shikenan Allah yabanidangana kowacce da halinta zata zauna ni ban iya tashin hankalinba kowa ma yasani."

Haka rayuwa tacigaba da gudana cikin lokacin da Umma  ta dibar musu har watanni biyar sun shude amma shiru babu wani labari na ciki duk wata saita tambayeshi yaya ake ciki an dace?sai yace har yanzu dai Allah bai nufa ba,shiyasa ma tafara shirin biki ba kama hannun yaro,gameda rayuwarshi kuwa shida bilkis babu abinda ya chanja don ko kadan bata chanja mishi ba kyautatawarta agareshi sai abinda ya karu hakika ta tabbatar mishi dacewar mace ce tagari dukda dai wannan abune daya dade dasani,a kullum cikin kara kwantarwa da juna hankali suke,hadeda rarrashin kansu gameda irintasu kaddarar ga salo da umman  ta dauka na dole saiya hada musu gida,duk kaffa kaffan dayake akan lamarin nan bayaso tayi wata magana akan alamarin gidan nan amma saida tayi, shi kanshi yasan  zaman lafiya yafi samuwa idan gida ba daya ba don yawancin mutane suna samun matsala ne idan mata ahade suke waje daya,bugu da kari wasu sunahada matansu waje dayane hujjarsu kuwa saboda hada kan yaransu kada kan yara yarabu ita kuwa bilkisu wane yaro ne da ita?tsakani da Allah indai zaa mata adalci wannan hukuncin ai yamata tsauri bayan mahaifanta basu ce komai ba gameda lamarin auren sun zuba ido alfarma daya suka nema na ya raba musu gidan kuma yace zaiyi to yanzu idan suka ji wannan zancen dawane ido zai kallesu zai zama kenan yamayi musu alkawari yasaba zaikasance mai baki biyu mara tsayayyiyar magana daya kenan yazama makaryaci ya salam.

"Lokaci yayi fa daya kamata wannan apartment din nacikin gidanka kafara gyarashi don dai ni a iyaka sanina nasan baa karasashi  ba"tace tareda kafe shi da ido "eh hakane baa karashi ba,amma ni wai da Ganinake gwara ita bakuwar(lubna) in ajiyeta a gidana na cen ungu....."ka ajiyeta a ina?saboda tsananin zalumci?ah lallai wato ka wancakalar da ita ka kama gabanka katafi wajen wannan kalatacciyar matar taka data gama dakai ko?to bazai yiwu ba ba zaa zalumci yarinya ba wallahi,kuma kar in sake jin wannan kalmar da bakuwa tafito daga bakinka ai kasan sunanta sarai banason rainin wayo,zancen raba gida kuma ai  munyishi dakai kwanaki anan wajen nace banyarda ba,shine kasake tado dashi wato,ban isa infada ba aji to bazaa raba gida ba idan ita matar taka (bilkis)taga bazata iya zama ba saita kara gaba mtsw"umma Don Allah don Annabi kidinga kyautatawa Bilkis zato wallahi bata cancanci duk iri wayannan kalaman ba hasalima nafada miki duk yadda mukayi da iyayenta akan zancen raba gida don Allah umma kiyi hakuri araba gidan nan kar a ingizasu a tabosu,kinga alamarin nan fa sun rungumeshi a matsayin kaddara sunyi hakuri bilkis fa kullum nauyinta nakeji saboda nasan ban kyauta mata ba itada iyayenta,kuma yar  alfarma kwaya daya dasukace amusu ta raba gidan nan sai akiyi  bayan na amince dahakan? kuma zancen na chanja kinga ai babu girma ba dadi wallahi ina matukar ganin girmansu da kimarsu mutane ne na kirki na kwarai h..."tabbas ta tabbata angama dakai nahaifawa duniya dana ban isa infada ba Adnan shine abinda kake nufi ko?"zaiyi magana ta dakatar dashi,"lokacin dakaje kagama yanke hukuncinka kayiwa mutane alkawari ka nemi shawarata?ai saboda ban isa ba ko?kaje kayi gaban kanka to nafada na kara babu wanda ya isa araba gida donshi,wanda yaga bazai zauna ba karya zauna "Don Allah umma kiyi hakuri wallahi bansan dawane irin ido zan kalli mutanen nan ba h...."hakika sunfini muhimmanci ko?su kana shakkar kallonsu nice baka shakka,to ka tashi kabani waje kafin in chanja shawara ince karabu da ita don tagama fitar min arai wallahi, "saurin mikewa yayi don yasan ha karamin aikinta bane intace zatayi tabbas zatayi"wallahi kaji ma na rantse bazanyi kaffara ba bazaa raba gida ba idan bazata zauna ba saidai ta tafi wallahi".

LOKACINEWhere stories live. Discover now