Dicisively

234 10 7
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2021.


*♡KALLO YA KOMA SAMA¸.•💥*
_((SHAHO YA ƊAUKO GIWA))_

'''#ƊAN MACE AGAIN'''



*HAWWA MUH'D USMAN.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*WATTPAD LINK:* https://www.wattpad.com/story/231697613?utm_medium=com.whatsapp&utm_source=android&utm_content=story_info

*FREE PAGE*

03

#Decisively

Jinjina kai Gimbiya Habibah tayi tace "Yaro² ne.. Da Gimbiya Habiba kake magana,da sannu zan mayar da rayuwarka abun tausayi" then ta wuce ta nufi apartment ɗinta,clearly Jay yaji abunda ta faɗa sai dai bai tanka ta ba. Washe gari da safe wata baiwa daga ɓangaren Hjy Babba ta shigo apartment ɗin Mami,sanda ta gaisheta respectfully ta sanar mata Hjy Babba tana neman Jay,Mami tace "idan ya tashi zan sanar masa in sha Allah" baiwar ta yi godiya ta tafi,lokacin Jay yana shirin fita,bayan sun gaisa da Mami,ta kalleshi tace "ka samu saƙon Hjy?" Ya girgiza mata kai a hankali yace "a'a" tace "okay! Kaje tana son ganinka" yace "toh! Idan na dawo zan je" tace "yanzu ina kake shirin zuwa?" Yace "zanje gidan gona ne Mami" kallonsa ta dunga yi kafin tace "gidan gona kuma?" Yace "Ehh" fuskarta ɗaure tace "yau kuma me za kaje kayi Mujaheed? Kullum ka fita ba ka da gurin zuwa sai can?" Zai yi magana tace "yau kam babu inda za kaje,ka wuce kiran da Hjy tayi maka,daga can ban amince ka fita daga gidan nan ba" yace "but Mami" saurin ɗaga masa hannu tayi ta nuna masa ƙofar fita tace "fita ka ba ni guri" babu musu ya wuce,sanda yake shiga ɓangaren Hjy yayi sallama,Hjy dake zaune ta amsa masa fuskarta da wani irin murmushi,ya ƙarasa ya zauna gabanta,shima fuskarsa ɗauke da murmushin yace "barka da safiya Hjyrmu" tace "Mujaheed! Mun tashi lafiya?" Yace "alhamdulillah!" Suka yi shiru,a hankali Jay yayi breaking silence ɗin yace "Hjy ance kina kira na?" Tace "ehh! Dama ba wani abu bane,mun yi magana da mahaifinka jiya,na sanar masa na yi maka mata,ba kuma wata bare bace,Atika ce ƴar wajen baffanka.. Sai ka samu lokaci ka shirya kaje kuyi magana da ita,yanzu haka ma mun gama magana da mahaifinka da shi baffan naka" wani kallo yake yiwa Hjy tunda ta fara maganar,a zuciye bai jira ta gama faɗar abunda za ta ce ba yace "wane irin magana ne wannan? Ni na saki ki nemo min mata? Ko munyi dake na ce miki ina son yin aure?" Baki sake Hjy take kallon Jay,tace "ni kuma kake faɗawa haka Mujaheed?" Bai amsa ba yace "akan wane dalilin za ki haɗa ni da Atika? Ko auren zan yi kuma sai na rasa wanda zan aura sai bazawara wanda ta haihu a wani gida?" Hjy Babba tace "ba ƴar uwarka bace,mene ne laifi dan ka aureta tana bazawara?" Girgiza kai kawai yayi ya miƙe yace "ko aure zan yi bazan taɓa auren Atika ba,kin fi kowa sanin ba jituwa muke ba,infact ma bazan iya auren matar da ta girme ni ba,because ita za ta juya ni,bazan faɗa mata taji ba.. Ta kashe aurenta ba tare da dalili ba shi ne za ku liƙa min,ku nemi wani ku bashi,ni ban shirya yin aure a yanzu ba.." Yana faɗa yasa kai ya fita,dai² lokacin Gimbiya Habibah ta shigo tare da wata kyakkyawar budurwa,bai kallesu ba ya nufi hanyar barin apartment ɗin,Gimbiya Habibah da ta bisa da kallo tayi wani murmushi mai sauti saboda yanda ta ga ɓaci rai a fuskarsa,a zuciya har ya juya with intention of ya karanta mata gangancin da take shirin aikatawa sai kuma ya fasa,hurriedly ya juya ya wuce apartment ɗinsu,yana shiga ya samu Mami zaune wata baiwarta tana mata massaging ƙafafuwanta,saboda yanda idanuwansa suka rufe bai ko kula da hadimar ba,cikin ɗagawar sauti yace "Mami wai me na tarewa matar nan da take son lallai sai ta dunga shiga hanya ta? Ina ruwanta da rayuwata da zata kaiwa Hjy maganata?" Da kallo Mami ta bisa kafin ta yiwa baiwar alamar ta basu guri,sanda ta ya fitosa alamar yazo while tana cewa "wani abu ya faru? Kai da waye?" Jijiyoyin kansa sun yi wani irin fitowa tsabar ɓacin rai yace "ni ban san me take nufi da shiga al'amurana ba.. Ina ruwanta idan ma cewa nayi bazan yi aure ba? Ita za ta zauna min da matar? Lokacin da najewa Abba maganar ina son yin aure har da ita cikin wanda suka zugasa,even though ya san matsalar da nake going through,haka baisa ya duba damuwata da halin da zan iya shiga ba,yanzu kuma ta fara min shishshigi,na je Hjy tana cewa wai za'a haɗa ni da Atika,yarinyar da kowa ya san tun muna yara ba ma jituwa.. Tun yanzu Mami ki shiga maganar nan kafin nayi abunda zai tada hankalin kowa a gidan nan" kasa magana Mami tayi sai kallon Jay kawai take hankalinta a tashe,da ƙyar ta daure tace "calm down son,zo nan.. Zo ka faɗa min abunda ya faru" ƙarasawa yayi kusa da mahaifiyar tasa ya zauna zuciyarsa sai tafarfasa take,tace "uhmn! Maza sanar min abunda yake faruwa" cikin ƙunar rai ya fara sanar mata yanda suka yi da Hjy,da abunda Gimbiya Habibah ta faɗa rannan lokacin da take wucewa,girgiza kai kawai Mami take tana kallon yanda Jay yake gritting tooth ɗinsa yana bubbuga dugaduginsa a ƙasa,jikinsa banda wani shivering babu abunda yake,a hankali Mami ta kai hannu ta janyoshi jikinta ta kwantar da kansa saman thighs ɗinta tana shafawa cike da son kwantar masa da hankali,lumshe idanunsa Jay yayi yana sauke numfashi,calmly Mami tace "kafin ka aikata abunda zai janyo min ɓacin rai,ka bari zan yi magana da Mai martaba,ka ji?" Jay yayi shiru bai sake magana ba,sai can ya miƙe da sauri,Mami tace "Mujaheed!" Yace "Mami i'm coming" har yana haɗawa da sassarfa,tace "ina kake shirin zuwa kake sauri?" Yace "Mami mantuwa nayi ina zuwa" hankalinta a ɗan tashe saboda bata san ina zai je ba tace "Mujaheed ka rufa min asiri kada kaje ka nemo rikicin da zai fi ƙarfina" instead of taga ya fita sai ya nufi hanyar ɗaya parlon,a tunaninta ko da taga yana sauri she just thought fita zai yaje apartment ɗin gimbiya Habibah,sanda yake wucewa ɗaya parlon ta sauke wani ajiyar zuciya sai kuma bata sake magana ba sai addu'ar data fara underneath,Jay kam daga nan direct part ɗinsa ya nufa,da sauri ya dunga tsallaka stairs ɗin ya sauka,yana shiga parlonsa ya wuce bedroom,wayoyinsa ya kwashe ya fito da car keys a hannunsa,sanda ya fito yana wucewa yace "Mami na fita.." Bai jira yaji me za tace ba yayi saurin ficewa daga part ɗin. Da dare lokacin Mai martaba yana part ɗin Fulani yake sanar mata maganar da suka yi da Hjy Babba akan Jay,Fulani tayi shiru bata ce komai ba,yace "mene ne shawararki?" Fulani ta nisa tace "ina ganin ya kamata ka fara yin magana da shi da mahaifiyarsa kafin kayi involving namu a cikin maganar" Mai martaba yace "shi kenan! Wannan ma shawara ne" daga haka suka bar maganar,almost 3 days kullum Jay ba ya zaunawa a gidan,kullum idan ya tashi da safe zai fice,ba shi zai dawo ba sai dare. A gefen Gimbiya Habibah kuwa,tun wancan ranar da tajewada Hjy Babba maganar Jay take monitoring duk wani motsinsa a gidan,sanda tasa aka kira mata wani amintaccen bawan da yake masa gyaran ɗaki,tana kallonsa da izza tace "Mudi! Kasan dalilin da yasa nace a kira min kai?" Yace "a'a ranki ya daɗe" Gimbiya Habibah tace "aiki nake so zan sa ka" jikinsa har ɓari yake yace "ki faɗi ko wane irin aiki ne ranki ya daɗe,da yardar Allah za ki same ni mai cika umarnin ki" Gimbiya Habibah tayi wani murmushi tace "maa sha Allah! Mudi" yace "na'am! Allah ya taimake ki" tana gyaɗa kai tace "wasu bayanai nake son sani,and na tabbatar babu gurin wanda zan same su idan ba kai ba" yace "akan mene ne ranki daɗe?" Strictly tace "akan uban ɗakinka ne,ina son ka ba ni wasu bayanai akansa,abubuwan da yake yi da wa yake mu'amala tun zuwansa,ina yafi zuwa?" Shiru Mudi yayi da farko saboda ya san dokar gidan akan bada bayanai kan wani,Gimbiya Habibah dake masa wani kallo tayi murmushi cikin hikima tace "Mudi!" Kansa a ƙasa gumi yana yanko masa yace "na'am ranki ya daɗe" tace "kada ka damu,ka sanar min duk abunda ka sani,ka gane kou.. Nima ko da kaji na maka tambayar nan Mai martaba yasa na tambayar masa,saboda ana zuwa ana sanar masa wasu maganganu akan Mujaheed,so hakan ba ya masa daɗi,a matsayinsa na only child ɗinsa namiji wanda zai gajesa,shisa yake son yima tufkar hanci ba tare da ya sani ba.." Ajiyar numfashi Mudi yayi yana gyaɗa kai yace "tabbas ranki ya daɗe da farko hankalina ya tashi ko da kika ji na yi shiru ban ce komai ba,amma tunda Mai martaba ya buƙaci hakan zan sanar miki komai" Gimbiya Habibah ta gyaɗa kai cike da farin cikin tarkonta ya kama kurciya,tace "kai nake saurare" Mudi ya gyara zama cike da zumuɗi yace "ranki ya daɗe abunda na sani wanda zan iya faɗa,kullum na shiga ina ganinsa yana waya,amma da harshen nasara ne,to da yake ni ba jin nake ba shisa ba zan iya cewa ga abunda yake faɗa ba,amma daga dukkan alamu da mace yake wayar nan,wani lokaci ma har kamar da ƙaramin yaro ina ganin suna magana.." Gimbiya Habibah tayi shiru tana sauraren bayanin da Mudi yake gabanta sai faɗuwa yake,sanda ya gama ta gyaɗa kai tace "shi kenan iya abunda ka sani?" Yace "haka ne ranki ya daɗe" ta gyaɗa kai tana biting lips ɗinta tace "na gode Mudi da wannan bayanin,sai dai ina son sake baka wani aikin,ka gane kou? Ina so ka kasance cikin shiri,a kowane irin lokaci zan sake neman ka.." Ya gyaɗa kai yace "in sha Allahu ranki ya daɗe duk abunda kike nema daga gare ni zan sanar miki gwargwadon iyawata,ai aikin taimako ne" Gimbiya Habibah ta gyaɗa kai tana wani murmushi,tace "ka jira na fito" ya amsa respectfully,ko da ta fito 50k ta basa bayan ta karɓi digiri ɗinsa saboda buƙatar hakan zai iya tasowa a kowane lokaci then ta sallamesa,yayi godiya yana ta zuba mata addu'ah,bayan fitarsa ya tsaya ya lissafa kuɗin yana juyasu da mamaki yace "wannan kuɗin kam in dai zan na samu suna shigo min ai ko akan Mai martaba kika tambayeni zan sanar miki" gaba ɗaya ji yake kamar an gafarta masa,sanda ya fita Gimbiya Habibah tayi wani murmushi a fili ta furta "da sannu zan cika burina akan ka Mujaheed.. Zan yi amfani da wannan damar na mayar da amintaccen bawanka spy ɗina.." Da dare lokacin Jay ya shigo part ɗinsa yana waya da Khaniiy,hira suke cike da farin ciki yana tambayarta Aslam da Nani,sanda suka gama hira ya tashi ya shiga wanka,Mudi dake laɓe waje tun shigowar Jay ya shigo da sauri yana bincika ɗakin,dai² lokacin Jay ya buɗe ƙofar ya fito saboda motsin da yaji,yana buɗe ƙofar ya tsaya between door way,fuskarsa ɗaure yana kallon Mudi da bai kula da fitowarsa ba cikin tsawa yace "me kake nema a nan gurin? Ka ajiye wani abu ne kake min bincike?" A rikice Mudi ya juya yana kallonsa,bakinsa da jikinsa suna shivering yace "yyy.. Yallaɓai.. Barka da yamma" kallonsa Jay yake yana tsaye doorway yace "yamma?" Yana masa kallon tuhuma,a rikice Mudi yace "afuwaan! Dare zance" Jay yana kallonsa ba tare da ya amsa ba yace "me kazo yi ne?" Mudi yace "Ƴallaɓai! Na ɗan manta abu ne nazo ɗauka" Jay yace "wane abu ne?" Mudi yace "Radio ce na bari ɗazu da nazo gyaran ɗaki" tsaki Jay yayi yace "ɗauki ka fita" Mudi yace "godiya nake ranka ya daɗe.." Ta gefen idanunsa yake kallon Jay da ya tsaya yayi folding hannuwansa,sanda ya wuce ya ɗauki ƙaramin radio daya bari ya yiwa Jay sai da safe ya fita,tsaki Jay yayi ya wuce ya kulle part ɗinsa then ya wuce bathroom. Sanda Mudi ya fito direct apartment ɗin Gimbiya Habibah ya wuce,after ya nemi izinin shiga,ya tarar da Gimbiya Habibah zaune parlonta ita kaɗai duk ta sallami bayin da suke gurin,Mudi ya gaisheta,tana kallonsa ba tare da ta amsa ba tace "ya akayi Mudi?" Mudi yana wani murmushi yace "ranki ya daɗe wani abu na kawo maki,na san tabbas kika ji za kiyi farin ciki" Gimbiya Habibah tana kallonsa tace "mene ne Mudi?" Radion da ya ɗauko a ɓangaren Jay ya fito da shi daga aljihunsa,sanda ya cire memory card daya sa ya miƙa mata yace "ki saurari wannan ranki ya daɗe duk bayanin da zan miki yana nan a ciki" tayi murmushi tana kallonsa tace "Mudi ashe kana da wayo har haka?" Yace "ranki ya daɗe ai duk cikin zama da ku ne muke koyon wani abun" ta jinjina kai tace "lallai Mudi kace za mu iya tafiya da kai" cikin jin daɗi yana sunkuyar da kai yace "Allah ya taimake ki" tace "shi kenan Mudi kaje zan nemeka da safe" yace "an gama ranki ya daɗe" ya tashi yana zabga mata kirari,a ransa yana ta kisima irin kyautar da za tayi masa idan abunda yayi ya karɓu. Sanda ta shiga bedroom kasancewar ba ɓangarenta Mai martaba yake ba ranar ta saka memory card ɗin da ya bata cikin wani ƙaramin waya da bata amfani da shi ta fara binciken abunda yake kansa,only recording da ta gani wani folder ta kunna,da farko shiru taji sai daga bayan ta fara jiyo alamun footsteps then maganar Jay cikin tsadadden turancinsa suna hira da Khaniiy,jikinta har wani ɓari yake sanda taji yana magana da Aslam,ta gwalo idanuwa jikinta yana wani vibrating tace "whatttt?" Sosai sanda ta gama sauraran recording ɗin hankalinta yake a tashe,ta rasa me yake mata daɗi cikin duniyar,ko minti biyu bata ƙara ba ta ɗauki wayarta ta kira wani number da tayi saving da *DEVIL* bugu ɗaya aka ɗauka,cikin rawar murya Gimbiya Habibah ta furta "taɓewa da asara ya gama tabbata akan mu" dariya aka fashe da shi da wani irin murya akace "me yake faruwa ne?" Gimbiya Habibah tace "tsinannen Yaron nan ashe mu ya mayar sakarkaru,ashe har Yaro ne da shi bamu sani ba" Devil dake sauroronta yace "wane irin yaro? Haramtaccen ɗa kike nufi ko me?" Gumi ya gama wanke fuskar Gimbiya Habibah cikin ƙaraji tace "wane irin haramtacce kuma,aure ne da shi a can ƙasar.. Aure yaje yayi bamu sani ba" saurin katseta akayi da faɗin "ƙarya ne!" Gimbiya Habibah tace "wallahi² babu ƙarya da kunnena naji ba wani ya bani labari ba" shiru mai maganar yayi then yace "idan da gaske kike just proove it" tace "okay² bari na turo maka evidence ɗin da nake da shi ka saurara kaji" da sauri ta katse kiran tayi masa sharing recording ɗin via WhatsApp,not too long Devil ya kirata,a lokacin kam Gimbiya Habibah ta kasa zaune,sai zarya take tana jiran kiransa,da sauri ta rarumi wayar tayi answering call ɗin,Devil yayi wani murmushi yace "hakan ma yayi,kada ki tada hankalinki,kafin ya samu damar komawa za muyi maganinsa,ki bar komai a hannuna,ke dai ki jira sakamako kawai.. In just 2 days komai zai faru.." Sun ɓata lokaci mai tsayi suna magana kafin su ajiye wayar,ranar gaba ɗaya Gimbiya Habibah bata iya samun bacci mai daɗi ba,ko yaya tayi juyi cikin dare sai abin ya faɗo mata sai tayi saurin tashi ta zauna tana goge gumi,mafarki kuwa babu irin wanda bata yi ba akan Jay. Da safe kasancewar Mai martaba yana part ɗin Fulani,Jay ya shiga after sun gaisa da Abban nasa yace "here i'm Abba" Mai martaba dake kallon Jay yace "na ganka ai" kan Jay a ƙasa yayi shiru bai sake magana ba,Mai martaba dake kallonsa yace "ita mahaifiyar tawa kaje ka yiwa rashin kunya?" gumi ne ya fara keto masa,gaba ɗaya yaji yana neman rasa nutsuwarsa,tsoro duk ya cikasa,a ɗan rikice yace "I'm sorry Abba" Mai martaba bai ce masa ƙala ba sanda zai fita yace "ka shirya abunda ba ka son har ka iya zuwa ka zagi mahaifiyata akansa,babu fashi and kafin ka koma in sha Allah za'a ɗaura aurenka" a rikice Jay ya ɗago fuskarsa yace "but Abba akwai maganar da nake son sanar maka tun zuwana" Mai martaba yana kallonsa yace "sai dai ka jira na dawo,yanzu zan fita fada" gyaɗa kai Jay yayi yace "toh Abba" a haka Mai martaba ya fita zuwa fada ya bar Jay zaune,tunda Abban nasa ya fita Jay ya riƙe kansa saboda wani damuwar da ya lulluɓesa da ƙyar ya fito part ɗin ya wuce apartment ɗinsu,bai tsaya ba yana shiga ya wuce part ɗinsa,sanda ya fara tattara belonging ɗinsa cikin luggage kafin ya fito ya wuce bedroom ɗin Maminsa,with intention of yayi mata bayani yaji me za tace,yanda yake jin zuciyarsa a yanzun tana masa ƙuna akan maganar auren da aka bijiro masa da shi akan Atika sam bazai taɓa iya yin biyayya akai ba,infact bazai iya zaunawa yana ji yana kallo a masa auren dole ba,ya shirya yin yaƙi da duk wanda zai shiga tsakaninsa da farin cikinsa,zai sanar musu maganar da ya kawo sa,ko da ace baza su karɓa ba,ya yanke zai tattara ya koma inda ya fito...

*This book is not for free,it's #300 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger zan ba ku number da za ku nema in sha Allah.*


#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

KALLO YA KOMA SAMA!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora