Shameful

96 13 4
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2021.


      *♡KALLO YA KOMA SAMA¸.•💥*
        _((SHAHO YA ƊAUKO GIWA))_

'''#ƊAN MACE AGAIN'''
         
            

   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*WATTPAD LINK:* https://www.wattpad.com/story/231697613?utm_medium=com.whatsapp&utm_source=android&utm_content=story_info

                            08

#Shameful

        Sanda akayi wani flashlight mai mugun haske,ya sake haska fuskar mutumin,idanun Aslam suka sauka kan kyakykyawar fuskar mutumin mai cike da kamala,kwarjini,hasken musulunci gami da dattako,a hankali Aslam ya lumshe idanunsa ya buɗe yana sauke numfashi,zuciyarsa yana bugawa da ƙarfi saboda tsoron da yaji sanda ya fara kallon mutumin,sai yake ganin kamar ya san mai irin kamarsa somewhere,a ruɗe mutumin da ya dafa Aslam yace "Yaro! Ka taimakeni saboda Allah,bina suke za su kashe ni.." Aslam ya kalli mutumin kafin ya waiwaya ya kallo farkon line,ganin bai ga alamun mutane suna zuwa ba,though furucin mutumin ya jefa shi cikin ruɗani ya daure yace "Uncle! Su wane ne suke binka? Su wane ne za su kashe ka?" Footsteps sound a dai² line yasa a kiɗime mutumin yayi saurin faɗawa soron gidan ya fizgo Aslam ciki,then ya mayar da ƙofa ya rufe,Aslam zai sake magana mutumin ya masa alamar "shhiii!" A wani irin birkice Aslam ya dunga kallonsa ya kasa gane komai,har sanda mutanen suka zo suka wuce,suna barin gurin mutumin ya fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya,Aslam dai ya zuba masa idanu,zuciyarsa tayi wani irin weak,tsoro ƙarara a fuskarsa ya kai hannunsa ya dafa shoulder mutumin yace "kayi haƙuri ka daina kuka,komai sai Allah ya nufa yake kasancewa ga bawa.. But su waye su? Mene ne dalilin da yasa suke binka?" A nutse mutumin ya ɗago kansa,yana kallon Aslam yace "ban san su ba,ban san waye ya turo su ba" ajiyar zuciya Aslam yayi,a hankali yace "mu shiga ciki,zan sanarma mahaifiyata sai ka kwana a nan,kafin safiya idan basu ganka ba ai za su haƙura ko?" Mutumin ya gyaɗa kai ya dafa kan Aslam,yace "na gode sosai Yaro,Allah ya yiwa rayuwarka albarka,ya kareka sharrin maƙiya mahassada" Aslam ya amsa yana yiwa mutumin murmurshin ƙarfin hali,sanda ya wuce forefront mutumin yana binsa a baya,suka shiga cikin gidan. Ƙofar ɗakin Nani ya tsaya yayi knocking,da sauri Nani dake zaune tana lazimi tace "waye nan yake buga min ƙofa? Baka ga ana iska ba?" Aslam dake tsaye yace "Nani! Ni ne" Nani ta harari ƙofar tace "a'a bazan buɗe ba,yi tafiyarka ka kwanta sai da safe" yayi murmushi yace "tou! Sai da safen" tace "Allah ya ba mu alkhairi" ta ci gaba da laziminta,juyawa yayi ya kalli mutumin yayi ƙasa da murya yace "muje ɗakina Uncle,da safe sai nayi musu bayani" mutumin yace "toh na gode." Aslam ya buɗe musu ɗakinsa suka shiga,babu komai cikin ɗakin fa-ce ƙatuwar katifa da aka rufeta da bedsheet mai kyau,sai drawer da bai wuce na ajiyar kayan mutum ɗaya ba,Aslam ya nuna masa bakin katifa yace "ga guri ka zauna" mutumin yayi masa murmurshi yace "na gode sosai Yaro na" Aslam ya mayar masa murmurshin yace "babu komai Uncle" suka yi shiru,Aslam bai zauna ba har lokacin,zuciyarsa tana tunanin maganganun mutumin,a hankali mutumin ya ɗago ya kalleshi yace "ya ya ne sunan ka?" Ɗan murmurshi Aslam yayi yace *"ASLAM JAHEED"* mutumin ya gyaɗa kai yace "maa sha Allah,na gode sosai Aslam,Allah ya saka maka da alkhairi.." Aslam ya amsa,mutumin yana kallon ɗakin yana sauke numfashi da tasbihi ga Allah,ya sake ɗago kansa ya kalli Aslam yace "please! Zan ɗan samu ruwan sha Aslam?" Aslam yace "ehh! Bari na kawo maka" ya juya ya fita ɗakin,bakin ƙofar ɗakin Mommie yayi knocking then yayi sallama,daga ciki Afnan ta amsa tace "Aslam bhai!" Aslam yace "behen! Akwai ruwan sha a nan gurin ku?" Tace "ehhh! Akwai" yace "taimaka ki miƙo min" tace "tou! Har abincinka zan miƙo maka?" Yayi ɗan jim bai ce komai ba,sai da ta sake maimaitawa,yace "ehh! Kawo har shi" tace "toh!" Yana tsaye ta buɗe ƙofar,dai² lokacin aka fara yayyafi a hankali,da sauri ya karɓa yace "dhanyawaad! (Thank u)" Tayi dariya tace "shubh ratri.. (good night)" yace "in sha Allah.. Mommie fa?" Tace "sallah take yi" yace "idan ta idar kice ina mata sai da safe" tace "toh" then ta mayar da ƙofar ta rufe,hurriedly ya juya ya nufi ɗakinsa saboda yanda ruwa ya fara ƙarfi. Kamar jira ake yana shiga ɗaki aka tsuge da wani irin ruwa mai ƙarfin gaske,yayi sallama ya mayar da ƙofa ya rufe,yana sauke numfashin sassarfan da yayi yake faɗin "allahumma thayyiban nafi'an.. (O Allah! Bring beneficial rain clouds)" kallonsa mutumin dake zaune bakin katifa yayi ya masa sannu,saboda yanda yaga ya shigo da hanzari,a nutse Aslam ya ƙarasa kusa da shi,ya ajiye masa medium food flask mai kyau da pure water biyu,yace "Uncle ga ruwan" mutumin ya miƙa hannu ya ɗauki ɗaya ya fasa nan take ya shanye,ya ɗauki na biyun zai sha Aslam ya katsesa yace "Uncle! Ai da abincin ka fara ci" da sauri mutumin ya kalli Aslam yace "abinci?" Aslam ya gyaɗa masa kai yana murmushi yace "ehh Uncle! Ga shi nan na kawo maka" haka kawai mutumin ya zubawa Aslam ido yana kallonsa hawaye cike a idanunsa,jikin Aslam ya yi sanyi ganin irin kallon da yake masa da sauri yace "I'm very sorry Uncle,idan ba ka son abincin shi kenan,ba sai ka ci ba ka kwanta ka huta" murmushi mutumin da har lokacin bai faɗawa Aslam sunan sa ba yayi yace "babu komai son na gode maka sosai,yanda ka taimake ni a yau,Allah ya kawo wanda zai taimaka maka har ƙarshen rayuwarka" a hankali Aslam yace "ameen yaa Allah" daga haka ya tashi daga gaban mutumin yana riƙe da pure water ɗaya a hannunsa,can ƙarshen katifar ya zauna yana jin yanda ake kwaɗa tsawa,ya fara karanto addu'ar da ake yi lokacin da ake thunder storm,mutumin sai kallonsa yake,lokaci ɗaya yaji Aslam ya kwanta masa a rai,yayi murmushi lokacin da yake buɗe flaks ɗin gabansa,yaga lafiyayyar wainar shinkafa da miya,sanda yayi murmushi ganin favourite ɗinsa then ya ɗago yana kallon Aslam yace "toh son! Ai da zuwa kayi muka ci tare,ina zan kai wannan abincin ni kaɗai?" Aslam yayi murmushi yace "a'a Uncle ka ci tukuna idan ka rage sai na ci" da sauri ya girgiza masa yace "no! Taso kazo muci tare,nima ba na iya cin abinci ni kaɗai.. Taso ka sa hannu muci tare" shyly kamar wani mace Aslam ya taso ya zauna,mutumin ya sauko daga kan katifar yayi flexing legs ɗinsa haɗe da yin bismillah a fili yasa hannunsa cikin flask ɗin,sanda ya fara fitar da hannunsa then Aslam ya saka nasa,a haka suka dunga ci har suka gama,mutumin bai sake magana ba,shima Aslam haka,suka wanke hannu suka dawo kowa ya zauna yayi shiru,can mutumin ya sauke numfashi ya kalli Aslam for the countless time yace "son! Can i ask u something?" Da sauri Aslam da zuciyarsa ta tafi tunani ya ɗago yace "why not Uncle! Just asked me whatever u want to" ya ƙare maganar da murmushi,a hankali mutumin yace "a tunaninka me zai sa haka kawai abi mutum ace za a kashesa?" A nutse Aslam ya fara gyara zama yace "think ƙiyayya zai iya sawa,ko idan ka fi mutum da wani abu,so idan yaga bai kaika ba wannan ma yana iya sawa hassada yasa shi jin idan ba kasheka yayi,bazai huta ba saboda ɓakin ciki" cike da gamsuwa mutumin ya gyaɗa kai yace "absolutely right! But ko da mutumin yana taimaka masa zai iya kashe shi kenan without feeling any guilt?" Aslam ya gyaɗa kai yace "haan! Uncle" shiru mutumin yayi yana tunanin a duniyar nan waye zai iya aiko da team of 5 to 7 men su taresa a hanya har su shaida masa kasheshi aka turo suyi? Ya ɗaukesa lokaci mai tsayi yana tunani kafin ya sauke ajiyar zuciya yace "Allah ya kyauta" Aslam yace "ameen" wani tunani mutumin yayi sai kawai yayi murmushi yace "i know who's behind all this.." Ya gyaɗa kai ya gyara zama yana sake zurfafa tunaninsa kan abunda yake zargi. Da asuba ko da Nani ta fito ta ƙwanƙwasa ƙofa tana kiran Aslam ya tashi,ya juya yaga mutumin tsaye kan abun sallah yana sallah,yayi addu'ah then ya tashi ya buɗe ƙofa ya fita,sanda yayi alwala kafin ya fita sai da ya leƙo ɗakin,lokacin mutumin ya idar da nafila,a hankali Aslam yace "Uncle! Zan fita masjeed,kayi sallah a nan kawai,tunda bamu sani ba ko sun tafi" mutumin yayi murmushi yace "nima abunda nake tunani kenan" Aslam ya juya ya fita,sanda aka idar da sallah a masallaci,da ya shigo gidan ɗakin Mommie yaje ya yi mata bayanin komai,tayi shiru tana juya al'amarin a ranta,can ta sauke numfashi tace "Allah ya kiyaye.." Ya amsa then ya tashi ya tafi. Da safe around 7am duk mutanen gidan suna bacci banda Mommie dake aikin abincin safe,aka fara buga ƙofa kamar za'a ɓalleta,sanadin da ya farkar da sauran mutanen gidan,da hayaniyar dake tashi ƙofar gida,Nani ta fito ɗaki sanye da hijabinta da tayi sallah ta nufi ƙofar tana tambayar "waye yake mana bugu da safiyar nan kamar mun ci masa bashi?" Tana buɗe ƙofa taga cincirindon mutane manya da yara,har ma da matan aure maƙota da suka fito kallo,Nani ta tsaya tana kallon mutanen dake tsaye ƙofar gidan na su cikin faɗa tace "lafiya! Kuke mana bugu kamar ance gari bazai waye ba? Bashin nawa muka ci muku da za ku tado mu tun rana bai gama isa wasu sassa a duniyar ba?" Mutumin dake kallon Nani yace "mai gari ya aiko mu sanar muku ana nemanku ƙofar fada" Yaawo da hayaniya ya kai mata saƙon ba lafiya ta fito da mayafi a hannu,sanda ta ƙaraso ƙofar gidan tace "ka ji wani bala'i kuma da sanyin safiya.. neman me ake mana a gidan mai garin?" Mutumin yace "nima dan saƙo ne ban sani ba,idan kunje kwa ji dalilin kiran" Nani ta taɓe baki tace "toh! Tunda ka isar da sako kana iya komawa ka shaidawa mai garin idan mun gama uzurorin mu za mu zo" daga haka ta juya ta nufi cikin gida tana mita,Yaawo ta biyota a baya itama tana sababi,Mommie ta fito ɗaki tana kallon Nani cikin yaren hindu tace "me yake faruwa Nani?" Nan da nan Nani ta juya baki ta fara zazzago mata bayani,Aslam dake fitowa daga ɗaki yaji gabansa ya faɗi da sauri ya koma ya zauna ya riƙe kai,a hankali fuskarsa tana bayyanar da damuwa ya furta "yeh kya hai? (What is this?)" Ta baya yaji an dafasa,da sauri ya ɗago kansa ya kalli mutumin dake kallonsa da wani kallo kamar na tuhuma,yace "do u have any relationship with Hindu?" A hankali Aslam ya gyaɗa masa kai,mutumin da ke sauraren hayaniyar da Yaawo da Nani suke yi yana sake kallon Aslam yace "tell me what's happening? Hayaniyar mene ne ake yi da safen nan?" Idanuwan Aslam har sun fara sauyawa a hankali ya shiga yi masa bayanin duk abunda ya faru tun daga jiya da yamma har wayewar garin,mutumin dake kallon Aslam lokacin da yayi shiru,ya sauke ajiyar zuciya ya bubbuga kafaɗarsa yace "u don't need to worry,maza yanzun kaje ka ji what's happening?" Calmly Aslam ya gyaɗa masa kai then ya tashi ya fita. Kafin 8am an yo aike daga gidan mai gari ana kiran su Nani ya fi biyar,Nani kuma ta rantse ta ce wallahi baza taje ko ina ba sai ta karya kumallo ta shirya a nutse,duk irin magiyar da Yaawo ta dunga mata bata saurareta ba tana zaune kan tabarmar da tasa Afnan ta shimfiɗa madaidaicin tsakar gidan mai ɗauke da ɗakuna uku ginin zamani,around 8:15am suna zaune suna karyawa dukansu har Yaawo da Naina,suka ji sallamar mai gari a tsakar gidan,da sauri Nani ta kalli bakin ƙofar shigowa tayi mitsi² da idanuwa,lokaci ɗaya ta ɗaure fuska ta miƙe tana kallon mai gari da suka kunno kai cikin gidan tace "wane irin kafirci ne wannan ɗin za ku shigo mana gida kai tsaye babu jiran a baku izini?" Yaawo ta zaro idanu tana taɓa Nani da mata alamar tayi shiru,cikin faɗa Nani ta hayyaƙo mata tace "rabu da ni in faɗa musu,nan garin musulunci muke ba kafirawa ba,taya dan yana taƙamar shugabanci a wani mitsitsin ƙauye zai shigo mana har tsakar gida,haka dokar Allah tace? Idan baku da ilimi mesa kuke mulki? Ko kuwa salon na ku mulkin ne haka? Ku dunga danna kai gidan mutan aure sakaka kamar dabbobi ba tare da kun nemi izini ba?" Mai gari da ya shigo da shirin sauke musu ruwan bala'i,yanda Nani take yi kamar za ta bigesu yasa shi yin ƙus kamar ruwa ya cinyesa,duk haƙurin da Yaawo take bawa Nani,bata yi shiru ba sai da ta tsigalesu tas,Yaawo ta juya tana kallon Mommie tace "Fatima maza zo kinji" Mommie da ta sunkuyar da kai ƙasa tun shigowarsu cike da fargaba,tayi saurin tashi suka janye Nani zuwa ɗaki,still bata haƙura ba sai leƙowa take tana musu tofin ala tsine,Mai gari yana ganin haka ya zare jikinsa yace da mutanensa su koma,wani dogari ya matsa kusa da shi yace "Allah ya baka yawan rai! Shi kenan haka za mu koma?" A little bit angry mai gari yace "me za mu yi musu?" Dogari yana ganin haka yaja bakinsa yayi gum,suka fice daga gidan jiki babu ƙwari sai tarin kunyar da suka ciko manyan rigunansu da shi,suna fita ƙofar gida mutanen layin suka sa musu dariya,ƙananan yara kuwa ƙofar gidan mai gari suka bisu suna musu ihu. Ranar maganar da yaita trending kenan a garin,mai gari ya je gidan Nani ta fatattakesa da masifa,kuma bai iya ya mata komai ba,duk bala'insa yau an samu wanda ta mayar da shi magen lami,kowa sai dariya yake a garin,mai gari saboda tsabar kunyar da ta addabesa ranar kasa zama yayi ƙofar gida,tsabar yanda mutane suke wucewa suna kallonsa da yi masa dariya,da farko bai gano kan al'amarin ba sai da ya tambayi dogarinsa ko lafiya mutane suke sintiri a ƙofar gidansa? Na-barau yace "Allah ya baka yawan rai ai abunda ya faru ɗazu da safe ne,duk garin nan babu wanda bai samu labari ba,yanzuma da kake ganin mutane suna wucewa ba komai yake kawo su ba sai gulmarka da suke yi" babu shiri Mai gari ya wawwaiga da sauri sanda ya faki idanuwan mutane ya faɗa gida....

    *This book is not for free,it's #300 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ku iya tuntuɓar wannan number +22770766074.*

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

KALLO YA KOMA SAMA!Where stories live. Discover now