War zone

169 12 2
                                        

💠💠💠💠💠
©®AS-2021.




      *♡KALLO YA KOMA SAMA¸.•💥*
        _((SHAHO YA ƊAUKO GIWA))_


'''#ƊAN MACE AGAIN'''
         
            

   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

                            04

#War zone

        Kiran da aketa yiwa wayar Gimbiya Habibah for about 5 minutes,ganin mai kiran bai gaji ya daina ba,yasa ta tashi bayan ta sallami kuyanginta ta wuce bedroom ɗinta da wani irin speed,tana shiga ta mayar da ƙofar ta rufe tana buɗa idanuwanta akan sunan da ta gani saman screen ɗinta,da ƙarfi ta furta "kai kuma kake kira na? A irin wannan lokacin" Hannunta har rawa yake ta kira back,yana ɗauka yace "ina kika shiga nake kiranki ba kya ɗauka? Da alamu kina son kawo mana matsala a tafiyar nan" Gimbiya Habibah cikin firgici tace "kamar ya?" Yace "kamar yanda kika ji.. Duk ba wannnan ba,yanzu kin san abunda yake shirin faruwa?" Tace "a'a sai ka faɗa" Devil dake saurarenta yace "Yaron nan yana daf da sanarwa iyayensa maganar matar sa" a firgice Gimbiya Habibah tace "whaatttt? How?" Devil yace "don't know,but kafin yayi hakan ya kamata mu tsayar da shi" Gimbiya Habibah tace "tabbas! Dan idan ya sanar da uban to fa duk wasu shirin mu akansa sun rushe kenan,and babu abunda zai hana bai yi mulkin garin nan ba,ni kuma baƙin cikina kenan,ko don haushin ban haifi namiji ba ai na yi duk yanda zanyi,muddin ya hau kujerar uban sai abunda muka gani,shi kenan ƙarshen zamanmu a gidan ya zo.." Devil yace "u don't have to worry.. Daga lokacin da yaje zai sanar musu komai zai faru,and bazai taɓa samun hanyar kuɓuta daga sharrin mu ba.. I'm telling u this" cike da farin ciki Gimbiya Habibah tace "na sani na kuma tabbatar,komai za ka iya yi.." Daga haka suka yi sallama. Sanda Jay yayi nocking ƙofar bedroom ɗin kafin yayi sallama ya shiga,zaune gefen gado ya tarar da Mami,ta amsa looking at him with suspicion tace "daga ina kake yanzu?" Ɗan kallon Mami yayi da idanunsa da suka yi wani mugun jaa,then ya zauna ƙasa kusa da ƙafafuwanta,slowly ya ɗora kansa saman thighs ɗinta ya lumshe idanunsa,Mami tana shafa curly hair ɗinsa,calmly tace "what happened Mujaheed? Maza ka sanar da ni.." Yana sauke ajiyar zuciya yace "Mami! Me yasa Mai martaba yake son yi min auren dole?" Mami dake saurarensa tace "auren dole kamar yaya? Maganar Atikan dai ne har yanzu?" Ya gyaɗa mata kai,ta sauke numfashi tace "dama wannan ne matsalar? Ita okay! Kada ka tada hankalinka,in sha Allah zan yi magana da shi,tunda ba ka so mene ne amfani dagewan sai an haɗa ka da ita?" Yayi shiru bai ce komai ba,tace "kayi haƙuri ka ji?" Calmly yace "tou Mami,but i want to go back to india,i need some rest" tace "hutun naka ya ƙare ne?" Yace "no! Ina dai son tafiya,ba na jin daɗin zama nan,ban san me nayi musu suke son saka ni cikin damuwa ba,i want to go and give them space" wani kallo Mami take masa cike da tausayinsa tace "shi kenan son,amma idan ka tafi kada ka sake jimawa baka zo ba" yace "tou Mami! I won't do it again" tace "it's okay! Allah ya maka albarka" sosai gabansa yake faɗuwa lokacin,can ya tashi yace "Mami kaina na ciwo" wani irin kallon tausayi kawai take binsa da shi,yace "Mami bari naje na kwanta ko zai min sauƙi" tace "sannu! Allah ƙara sauƙi,ka sha magani sai ka kwanta" yace "tou Mami" slowly yake tafiya Mami ta bisa da kallo har ya fita,ta girgiza kai cikin wani tashin hankali tace "bazai yiwu ba.. Dole na ma tufkar nan hanci kafin ya zame min babban matsala.." Da sauri ta tashi,alkyabba ne jikinta ɗan ubansu mai mugun kyau kalar atamfar jikinta,sanda ta fito parlor ranta a ɓace ta wuce ta fita part ɗin,tana forefront kunyanginta suna binta a baya,direct part ɗin Gimbiya Habibah ta nufa,bata jira neman iso ba ta shiga bayan ta sa kunyangin sun tsaya waje,sanda tayi sallama fuskarta babu annuri,Gimbiya Habibah dake kishingiɗe ta ɗago kai ba tare da ta amsa ba ta gyara zama tana kallonta a wani iri tace "dame kike tafe?" Mami bata kula da ita ba sai da tayi magana,ta juya tana kallonta direct in the eyes tace "i just come to warned u,ina so ki fita hanyar yarona,idan ba haka.." Ta kaɗa mata hannu tana jinjina kai,Gimbiya Habibah tana mata wani kallo tayi dariya tace "kou? Yanzu nan kin zo ki min warning? Ke kanki ai baki isa ba bare ɗanki,me akayi² sa?" A kausashe Mami tana nuna ta tace "na gaya maki ki dakata haka,duk abunda kike yi ina sane,so ki dakata haka nan,wanda kika yi a baya ya isa,idan kika ce za ki cutar min yaro a yanzu,wallahil'aziim zan nuna maki true colour ɗina,duk abunda kike taƙama da shi na wuce da saninki.. And ba wai ina nuna miki zan yi irin abunda kike yi ba,no ni ba taɓaɓɓiya bace,ina kuma roƙon Allah akan hakan,shi kaɗai muka riƙe muke kaiwa duk kukanmu,mun yi imani da shi mun san shi yake da iko akan komai saboda shi ne isasshe,da sannu zai share mana hawaye,saboda haka nake sake jadadda maki wannan maganar ya tsaya iya nan between ni da ke,kada kiyi kuskuren shiga hurumin da ba naki ba,don akan Mujaheed babu abunda ba zan iya ba.." Daga haka ta juya ta fita apartment ɗin without giving her any chance na cewa wani abu,gumine ya dinga ketowa Gimbiya Habibah saboda yanda Mami tayi mata magana ya mugun bata tsoro,sanda ta waiga ta shiga ƙarewa parlon kallo to make sure babu wanda ya jisu,ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya ta tashi da sauri ta wuce bedroom ɗinta,cikin tsananin tashin hankali ta cire alkyabbar jikinta tayi jifa da shi,ta shiga zarya wall to wall,underneath take jujjuya maganganun Mami,a fili ta shiga magana ita kaɗai "what the hell is this.. Ta shigo min har nan ta gaya min magana bata jira na mayar mata ba ta fita ta barni.. Kamar ni Gimbiya Habibah,ni wannan abar za ta zo har apartment ɗina tace ta zo tayi min warning? Tou za mu gani.. Daga ke har ɗan naki zan ga wanda ya isa ya sha a hannuna,da sannu zan mayar da ku abun tausayi ababen kwatance.. Sai na zame muku matsalar da baku isa ku gane kanta ba,zan tarwatsa rayuwarku na tarwatsa farin cikinku,na lashi takobi sai na yi nasara ko ta wane hali.. Sai dai idan ban amsa suna na Habibah ba" ta ƙarasa maganar tana wani huci,kafin ta koma bakin gadonta ta zauna daɓas ta shiga kiran abokin makircinta. Jay kuwa lokacin yana barin ɗakin Mami part ɗinsa ya wuce,a palour ya kwanta saman kujera dafe da kansa dake mugun sarawa,a hankali yake matsa forehead ɗinsa yana karanto addu'oi,sanda kan ya ɗan masa sauƙi ya tashi ya wuce bedroom ya kwanta,babu jimawa bacci me nauyi ya ɗaukesa,cike da wasu irin mugayen mafarkai masu cike da ruɗani,can cikin bacci lokacin ya haɗa wani uban gumi,duk da AC da suke aiki bedroom ɗin,a hankali ya fara jiyo sautin ring ɗin wayarsa,a ɗan firgice ya buɗe idanunsa saboda wani mafarkin da yake kan yi,sanda ya fara ƙarewa bedroom ɗin kallo kafin yaja numfashi ya sauke haɗe da sauke ƙafafuwansa ƙasa ya dafe kansa da ya sake sarawa sakamakon farkawar da yayi ba'a dai² ba,then ya tashi da sauri ya nufi wayar da har kiran ya katse,sunan Khaniiy ne saman screen ɗinsa,haka nan ya zubawa wayar idanunsa kamar mai nazari,ba tare da ya kira ba ya ajiye wayar ya wuce bathroom,ruwa ya fara watsawa jikinsa then ya fito sanye da farin bathroom,dai² lokacin wani kiran ya sake shigowa,a hankali ya saki siririn tsaki yayi wucersa ya shirya cikin ƙananan kaya ya fita ba tare da ya ɗauki wayar ba. Tashin hankalin da Khaniiy ta shiga lokacin ganin tana kiran Jay ba ya ɗauka for almost 1 hour yasa ta fashewa da wani irin kuka,a hankali Aslam dake kwance jikinta ya ɗago kai yana kallonta idanunsa sunyi rau² yace "yeh kya hai Mommie? What happened to u? Why are u crying?" Rungumeshi ta sake yi sosai tana kuka,ganin haka shima ya fashe da kuka,suka ci gaba da rera abunsu tare,can Nani ta zo wucewa ta jiyo kamar kukan Aslam,da sauri ta buɗe ƙofar ɗakin tana faɗin "Khaniiy! Me yake faruwa? Me yasa kina jinsa yana kuka kika rabu da shi.." Kalmomin tane suka katse lokacin da tayi arba da Khaniiy ta tusa Aslam suna kuka tare,da sauri ta nufosu tana faɗin "Subhanallah! Khaniiy! Me yake faruwa?" Kuka mai tsanani Khaniiy take tana jan zucuya tace "Ammi Jay nake kira tun ɗazu ba ya ɗaukan wayata,ban san me yake faruwa ba,gabana yana faɗuwa sosai Ammi taɓa kiji,i'm too scary Ammi,idan Jay ya barni zan iya rasa raina,Ammi kiyi wani abu akai kafin ki rasa ni" uwa da ɗa sai Allah,nan da nan hawaye suka cikawa Nani idanu,da sauri ta kai hannu ta share,tana dafa kafaɗar Khaniiy tace "kiyi haƙuri Khaniiy,in sha Allah nothing will happen,ki ci gaba da addu'ah nima ina yi miki kin ji?" A sanyaye ta gyaɗa kai tace "but I'm scared Ammi" Nani ta girgiza mata kai tace "u should not.. Kiyi haƙuri babu abunda zai faru" slowly ta sake gyaɗa kai,Nani ta kai hannu ta ɗauki Aslam dake cinyarta tace "stop crying beta it's okay.. Itama Mommie ta daina" waigawa yayi yana kallon Khaniiy dake share sauran hawayenta,a hankali da muryar kuka yace "i want to see my Daddy.. Nani ki tafi dani gurinsa" Nani ta rungumeshi tana shafa bayansa tace "it's okay! Zan kirashi yazo maza ya tafi da kai" da ƙyar ta samu ta lallaɓasa yayi shiru,sanda ta fita da shi ta zaunar da shi tana karanta masa story books sannan ya ware ya shiga wasanninsa. Almost 2 days tsakani sam Khaniiy ta kasa samun nutsuwa,kullum sai ta kira Jay,wayar yana shiga ɗauka ne kawai ba'a yi,wani lokaci kuma idan ta kira² sai taji an kashe wayar ma gaba ɗaya,haka za taita kiran tana kuka tana roƙonsa ya ɗauka kamar yana gabanta. A ɓangaren Jay kuwa lokacin haka nan yake jin ba ya son magana da kowa,ba kuma saboda ya manta wace ce Khaniiy ba sai don damuwar da yake ciki dake neman fin ƙarfinsa,ya san idan ya faɗa mata za ta fishi shiga tashin hankali,shisa wani lokacin yake kashe wayar ko ta kira baza ta samu ba,a tunaninsa hakan wani mafita ne ya samarwa kansa,duk sanda ya koma sai ya rarrasheta. A ranar sanda Gimbiya Habibah suka gama ƙulle²nsu ta samu Hjy Babba tana kuka afujajan ta sanar mata Mami ta je har apartment ɗinta ta ci mata mutunci akan Mujaheed,har tana mata gorin haihuwa,Hjy tayi mitsi² da ido tana kallonta fuskarta ɗaure tace "wane irin gorin kuma,in ji dai kema kin haihu? Kuma ba ɗaya ba,ba biyu ba?" Gimbiya Habibah tana matsar ƙwalla tace "Hjy sai kin ji maganganun da ta farfaɗa min,wallahi kare bazai ci ba,saboda taƙamarta ta haifi Mujaheed,ni kuma duka nawa mata ne.. Yanzu dan na bada shawarar haɗa Mujaheed da Atika sai ya zama laifi? Shi kenan sai aga baƙi na? Ganin da nayi ai duka gida ne kou?" Hjy ta gyaɗa kai tace "shi kenan yi shirunki Habibah,ki kwantar da hankalinki,in dai ni na haifi uban Mujaheed yau dole ma yasa shi yayi min biyayya,me akayi² wata mata da har dan ta haifesa za tace za ta fimu iko da shi? Ita a wa? Ita ɗin banza ita ɗin wofi" Gimbiya Habibah tayi ƙasa da kai tana share hawaye kamar gaske,wani irin farin ciki ya cika mata zuciya,a duniya bata ga abunda ta ƙi jini irin Mujaheed ba,tun da aka haifesa take dakon ƙiyayyarsa,dai² da sau ɗaya bata taɓa jin ƙiyayyarsa ya ragu a ranta ba,ko wane lokaci farautarsa take tana neman damar da za tayi amfani da shi ta salwantar da shi,sai dai ta yi rashin sa'a,gaba ɗaya shi ba mai yarda da mutane bane,tun tashinsa idan ba Mai martaba ne ya fita da shi ba tou sai dai ko Maminsa,sai Hjy Babba,da su kaɗai yake yarda,sai daga baya da yake zuwa gurin Fulani,a haka har lokacin da ya gama primary school,lokacin da zai tafi secondary School wani al'amari ya faru,daga nan ne Mai martaba ya ɗaukeshi daga gidan ya kaishi boarding school,sanda ya gama ya tafi India,a can yayi karatunsa har PhD ya nemi aiki,cikin hukuncin Allah kuwa ya samu a wani bank,kasancewar banking and finance yayi. A daren sanda Hjy tasa aka kira mata Mai martaba ta sanar masa komai,kamar yadda Gimbiya Habibah ta sanar mata,sosai ran Mai martaba ya ɓaci,yace "yanzu abunda Mariya za tayi min kenan? Dole sai an nuna min ban isa ba kenan?" Ya jinjina kai yayi shiru,Hjy tace "ai zancen ɓacin rai duk bai taso ba,abu ɗaya ya kamata kuma ya rage,shi ne ka tursasawa Mujaheed auren Atika,idan akayi haka shi kenan an karya lagonta,har ma da ƙarfin da take ganin tana da shi.." Mai martaba yayi shiru bai ce komai ba,Hjy Babba tace "da kai fa nake magana Abduljalal kayi min shiru baka ce komai ba,ko dai matarka da ɗanka sun fini matsayi a gurinka ne?" Ya girgiza kai yace "ko ɗaya Hjy" Hjy Babba tana masa wani kallo tace "idan ba dai kana son nuna min ban isa da iyalinka ba,wannan ɗan abun dana nema ne har kake tunani akansa?" Yayi shiru bai amsa ba,cikin ɓacin rai tace "ai shi kenan sai ka tashi kaje,salamamme wanda bai fi ƙarfin gidansa ba.. Ai ni dama banga dalilin da yasa ubanka ma ya ɗauki mulkin nan ya maƙala maka ba,duk tarin ƴaƴansa ya rasa wanda zai zaɓa ya bawa sai kai,mutumin da bai isa da iyalinsa ba ta ina zai iya ji da al'ummar da suke ƙarƙashin sa?" Sosai mitar da Hjy Babba take yiwa Mai martaba ya tunzurosa,sanda yaga ba ta da niyyar bari yace "dan Allah kiyi haƙuri ki bar maganar nan,ni fa na san abunda zanyi,ki barni kawai da su" Hjy taƙi yin shiru ta ci gaba da mitarta,Mai martaba ya sunkuyar da kansa ƙasa yayi shiru bai sake magana ba,dan kanta ta gaji a fusace sanda taga ya rabu da ita tace "tou kuma zaman me kake min a nan ne? Ka sakani gaba kamar wata taɓaɓɓiya,shirun ma baza ka iya cewa nayi ba,bare ka ba ni haƙuri?" Mai martaba ya ɗago yace "tou Hjy ya kike so nayi,na baƙi haƙuri na roƙeki duk kin ƙi bari" tace "ehhh! Saboda ga mahaukaciya shisa bari ka zuba min ido nai tayi kenan" yayi shiru bai magana ba,nan ta sake ɗorawa tana ta zazzaga masa,sanda tayi mai isarta ta koreshi,yana fita ya sauke ajiyar zuciya ya nufi apartment ɗin amaryarsa,dogarawa suna biye da shi sanda ya shiga kafin suka tafi,direct yana shiga bai kalli Mami ba dake masa barka da shigowa bare ya amsa yace "ina Mujaheed?" Mami tayi jimm tana kallonsa ganin fuskarsa babu annuri tace "ranka ya daɗe lafiya?" Yace "bai dameki ba,ɗana nake tambayar yana ina?" Ta haɗiye wani abu da ya tsaya mata a wuya tace "yana part ɗinsa" kai tsaye Mai martaba ya wuce ya barta a gurin tana masa kallon mamaki da tsoro,abunda ba ya yi zuwa part ɗin Mujaheed da kansa sai dai ko idan wani serious abu ya faru like idan Jay baida lafiya ko something else haka,hankalinta gaba ɗaya taji bai kwanta da shigar Mai martaba gurin Jay ba,da sauri ta tashi ta bi bayansa,a parlon ta samu Mai martaba saman cuition,Jay yana zaune kusa da ƙafarsa kansa a ƙasa,babu wanda ya kalleta sanda ta shigo ta ƙarasa tana kallon Mai martaba tace "wai me yake faruwa ne haka ranka ya daɗe? Ka shigo baka ce min komai ba,kuma na ga ranka a ɓace" Mai martaba bai tanka ta ba yana kallon Jay yace "ka dai ji me nace maka kou?" Calmly Jay ya gyaɗa kai bai iya amsawa ba,Mai martaba ya tashi yana kallonsa yace "ya rage naka kayi min biyayya ko ka bijire min,na dai faɗa maka matsawar kana numfashi kuma kana amsa sunan ɗana dole kabi abunda nake so.." Daga haka ya fita part ɗin ɗan nasa ya barsu zaune cikin tashin hankali,yana tafiya Mami ta kalli Jay tace "Mujaheed me yake faruwa?" Jay da ya riƙe kansa ya rasa me yake masa daɗi cikin duniyar yace "Mami Mai martaba ya rantse sai na auri Atika,i told him ba na sonta ya aura min whomever he wanted me to zan karɓa amma banda ita,shi ne yace i'd either kill myself or kill her but he won't change his mind" cikin tsananin tashin hankali Mami take kallonsa tana maimaita faɗan "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..." Bata jira jin me zai sake faɗa ba tayi saurin tashi ta fita...

   *This book is not for free,it's #300 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ku iya tuntuɓar wannan number +22770766074.*

      _Masu tura min 400 for both KYKS & IN-LAWS,dan Allah idan bamu yi dake ki tura min haka ba ina ga ki riƙe kuɗinki zai fi,na yi mistake gurin saka digit,and na rasa wanda zai min gyaran nan sai da na duba na gano kuskuren nawa ne,so na barshi a promo and ya ƙare daga yanzu,my sister idan ki shirya it's #500 both,na gode._


#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

KALLO YA KOMA SAMA!Where stories live. Discover now