Perplexed

133 11 1
                                    

💠💠💠💠💠
©®AS-2021.



      *♡KALLO YA KOMA SAMA¸.•💥*
        _((SHAHO YA ƊAUKO GIWA))_

'''#ƊAN MACE AGAIN'''
         
            

   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*FREE PAGE*

                            06

#Perplexed

       "Mun sani zuwa yanzu duka da muke zaune a nan,babu wanda zai ce bai samu labarin abunda ke faruwa cikin wannan na mu ba,daga daren jiya zuwa wayewar gari,haka ne?" Wasu cikin occupants ɗin dake parlon suka amsa da "haka ne ranka ya daɗe" yace "maa sha Allah.. Bari mu tafi kai tsaye ga dalilin da ya tara mu.. Da farko muna bawa ɗan uwanmu kuma ƙaninmu haƙuri bisa abubuwan da suka faru,sannan muna bawa duk wanda aka ɓatawa rai haƙuri,duk da kasancewar mun yi duk wani ƙoƙari na ganin mun ƙulla alaƙar auratayya tsakanin ƴaƴan mu,sai dai Allah bai nufa ba,tunda maganar da muke akan shi yaron da akayi wannan zama dominsa tuni ya bar gida,a saboda haka muke kira ga ƴan uwanmu da suyi haƙuri,muna kuma riƙon Allah ya bamu ladar abunda muka yi niyya.. A ƙarshe kuma muna kira gare ku,idan akwai wani mai sha'awar auren ita yarinyar,ko ta samu miji a waje,mun yi alƙawarin ɗauke musu duk wasu wahalhalu na lokacin auren,fatan Allah ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali.. Wassalamu alaikum" shiru gurin yayi babu wanda ya iya yin magana,yayin da wasu ke jin haushin sarki Abduljalal,suna ganin saboda ɗansa ne yayi shi yasa bazai iya tursasa a ɗaura auren ba,daga nan sai a tura masa matar duk inda ya tafi,a lokacin kam ai bai isa yayi jayayya ba indai akace an ɗaura,can bayan wani lokaci wani kyakkyawan matashi ya ɗaga hannunsa kamar a class,mai martaba ya gyaɗa masa kai alamar ya faɗi abunda yake son cewa,sanda ya miƙe sanye da ƙananan kaya yana ɗan sunkuyar da kai yace "na gode ranka ya daɗe.. Dama akan maganar Atika ne ranka ya daɗe.." Sai kuma yayi shiru ya kasa faɗa,mai martaba yayi murmushi yace "just go on" ɗan sunkuyar da kai yayi yana murmushi,mai martaba da sauran occupants ɗin gurin sai kallonsa suke yace "muna sauraren ka Al'ameen" a hankali kamar bazai magana ba yace "idan babu mai ra'ayi cikin family" sai ya sake yin shiru,mai martaba ya jinjina kai yace "babu komai,idan mun fita ka same mu anjima,tunda kana jin kunyar faɗa kowa yaji" Al'ameen yayi godiya ya zauna yana sakin murmushi,sanda akayi addu'ah kafin sarki Abduljalal yace "za ku iya tafiya,mun sallame ku.." A ɓangaren Jay kam cikin daren sanda ya fita gidan sarautar direct hanyar Katsina ya ɗauka,da tunanin idan yaje can sai ya nemi flight da zai kaishi Lagos daga can ɗin sai yabi flight ya wuce India,da wannan tunanin yaita sharara gudu kan titin while yana kallon motocin da suke binsa a baya na masarauta,guraren 2am lokacin yana ta ƙoƙarin kiran Mami ya sanar mata matsalar da ake ciki,yana driving yake operating wayarsa,kamar daga sama lokacin ya ɗago idanunsa yana kallon hanya ya hangi wani dattijo zai tsallaka titin,cikin sauri ya ajiye wayar hannunsa yana ta ƙoƙarin riƙe steering wheel dake neman ƙwacewa hannunsa,sanda ya kauce ba tare da ya bige tsohon ba da ƙarfi motar ta kauce da ƙarfin gaske ta daki ginin da ya raba titunan biyu,a lokacin kuma tuni motocin da suka biyosa sun juya bisa umarnin mai martaba,Allah ya taimakesa babu jimawa wani mota dake bayansa can nesa ya ga abunda ya faru,sanda mai motar ya ƙaraso da sauri yayi parking ya fito,it was there ya kira police station ya basu information ɗin abunda ya faru,kafin suzo su kuma suka yi waya general hospital suka sanar,daga can aka turo ambulance ɗin da ya ɗauki Jay aka wuce da shi hospital. Lokacin da parlon ya rage Hjy Babba da sarki Abduljalal,tana masa wani kallo tace "sam Abduljalal ban gane ma'anar abunda kayi ba yau ɗin nan,shin ɗan naka ya fi ƙarfinka ne ko bai isa a tursasa yayi abunda ake so ba? Shi ya haifeka ko kai ka haifesa da za ka yarda ka zuba masa idanu yayi abunda yaga dama?" Mai martaba ya girgiza kai yace "Hjy maganar nan tunda al'amarin ya faro da haka,ina ganin haƙuri shi ne kawai yafi alkhairi da azo babu jiƙawa abu ya lalace kowa yana jin haushin kowa,gara ayi haƙuri a bar maganar tun bai nisa ba.. Kuma tunda yanzu an samu wani cikin family ya nuna sha'awar aurenta falillahil hamd,Allah ya tabbatar masu da alkhairi ya basu zaman lafiya.." Hjy tayi shiru tana saurarensa can tayi ajiyar zuciya a sanyaye tace "tou maganar Mariya fa? Ni dai ina zargin da sa hannunta yaron nan ya gudu ko kuwa?" Saurin kallonta mai martaba yayi yana girgiza kai yace "ba na tunanin da saninta,saboda itama yanzu haka hankalinta a tashe yake.. Tun bayan da labari yaje mata,dalilin da yasa nace a barta ma kenan ba sai an kirata ba" Hjy ta jinjina kai tace "tou ai shi kenan,wannan yaro Mujaheed dai ya tozarta mu,in banda hauka daga maganar aure sai ka kama gudu ka bar gida,anya yaron nan ba wata gagarumar matsala yake tare da shi ba,muka kasa fahimtarsa.." Sarki Abduljalal yace "matsala kuma Hjy?" Tace "matsala mana,yanzu ace daga maka maganar aure shi kenan kamar an haɗa ka da maƙiyinka? Anya ba aljana ce ma ta maƙale masa ba?" Mai martaba dai ya sunkuyar da kai bai ce komai ba,Hjy tana ta magana bai tanka ba,sai can yace "koma dai mene ne zai dawo ya same mu" Hjy tace "atooohh! Gara dai a san abunda ake ciki,idan ma matsalar ne da shi sai a san abun yi akai ai" yace "in sha Allah" daga haka yayi mata sallama ya tashi,yana shirin fita aka masa waya,sanda yake dubawa yaga ɗaya daga cikin numbers ɗin Mujaheed ne ake kiransa da shi,har kamar bazai ɗauka ba kuma wata zuciyar tace ya amsa,gabansa yana faɗuwa yayi answering call ɗin yayi sallama,daga ɗaya gefen sanda aka amsa akace "don Allah da mahaifin Mujaheed muke magana?" Hankalin Mai martaba a ɗan tashe yace "eh shi ne.. Me yake faruwa? Ina Mujaheed ɗin yake?" Daga can gefen akace "muna masu ba ka haƙuri,tare da sanar maka ɗanka mai suna Mujaheed Abduljalal Yusuf ya samu haɗari a hanyarsa ta zuwa Katsina,yanzu haka yana nan general hospital katsina a nan A & E department" mummunan tashin hankalin da mai martaba ya shiga sanda ya koma ya zauna da sauri yana faɗin "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Allahumma ajirnii fii musabii wa'aklufnii khairan minha" Hjy da taga yanayinsa ya canja lokaci ɗaya tace "lafiya Abduljalal? Me yake faruwa?" Da wani murya mai martaba yace "Mujaheed ne aka kira ake sanar min yayi hatsari" idanuwa Hjy ta fiddo ta dafe ƙirji,lokaci ɗaya ta fashe da wanj kuka tana faɗin "hasbunallahu wani'imal wakiil.. A ina ne?" Mai martaba yace "a hanyar Katsina" da sauri ta tashi ta fara neman takalmi da ƴar purse ɗinta ta riƙe tana share hawaye har sannan tace "tou ai bamuga ta zama ba sai ka tashi muje kou? Wa ya sani ma ko mutuwa yayi suka ɓoye basu sanar mana ba" hankalin mai martaba bai sake tashi ba sai da Hjy tayi wannan maganar,da sauri ya tashi ya nufi ƙofa Hjy ta biyosa a baya,sanda yake wucewa part ɗin Mami yace dogarai su wuce tare da Hjy mota zai fito yanzu,Hjy tace "me za kaje yi can ɗin,ba kamata yayi ace mun wuce ba?" Mai martaba bai tsaya ba yace "Hjy yana da kyau mu tafi da mahaifiyarsa" tace "haka ne,sai ku hanzarta" Hjy da wasu fadawa suka wuce mota,while mai martaba ya wuce part ɗin Mami da sauri,yana shiga ya sameta bedroom zaune bakin gado ta yi shiru ta zubawa guri ɗaya idanu,sanda yayi sallama ta ɗago ta bisa da kallo har ya ƙaraso,a hankali ta ɗauke kanta tace "barka da safiya.." Yace "barka dai.. Mun tashi lafiya?" Shiru tayi bata amsa ba,yana kallonta cike da tausayi yace "get set za mu fita yanzu" da sauri ta ɗago tace "i've nowhere to go.." Sanda ya juyo yana mata wani kallo strictly yace "ba shawarar ki na nema ba,umarni na bayar ki tashi ki shirya fita za mu yi da sauri" kuka ta fashe da shi tace "na faɗa maka bazan je ba,mene ne amfanin dagewar sai na bika wani guri?" Girgiza kai yayi ya wuce ya ɗauko hijab zai sa mata,ta fizgesa da ƙarfi tayi jifa da shi,a fusace sanda ya mata wani tsawa yace "wannan abun da kike ba komai bane face ɓata mana lokaci,da ace kin san inda za muje ko musu baza ki iya yi min ba.. Idan kin ga dama ki biyo ni muje" a zafafe idanunta suna fitar da wani ƙwalla baƙin ciki tace "na faɗa maka babu inda zanje" girgiza kai yayi kawai ganin no way out,babu amfanin ya ci gaba da ɓoye mata maganar,a hankali yace "okay! Dama yanzu akayi min waya aka sanar min Mujaheed ya samu hatsari" daga haka ya juya zai bar ɗakin,zabura Mami tayi ta tashi tsaye tana masa wani kallo tace "wane Mujaheed ɗin? Kada kace min Mujaheed ɗina ne yayi hatsari?" Girgiza kai kawai yayi ya juyo ya kalleta ba tare da ya bata amsa ba ya juya ya fice,a razane Mami ta ɗauki hijabi ɗin ta biyosa har tana haɗawa da sassarfa,tana tafiya tana saka hijab ɗin,sanda take ƙoƙarin fita part ɗin mai martaba ya juyo yana kallon yanda take kuka cikin tsananin tashin hankali,bai ce komai ba suka fita part ɗin. Kasancewar flight suka biyo,tafiyar mintuna ya kawo su Katsina,kafin su ƙaraso har an chanjawa Jay hospital an mayar da shi wani babban private,jami'an tsaro ta ko ina sun barbazu cikin ward ɗin da yake,sanda sarki Abduljalal suke shigowa hospital ɗin tare da Governor,ƙaran siren yasa babban likitan dake kula da Jay ya fito office ɗinsa ya taho ward ɗin tare da wasu Dr's,suka taro mai girma governor,tare da sarki Abduljalal da wasu cikin fadawansa da suka zo Allah together,banda security daga government house na nan Katsinan da suke biye da su,Mami da Hjy ne kawai mata a cikinsu,zuwa lokacin kam tuni har sun gaji da kuka sun yi shiru,sanda Dr Mustapha suke gaisawa ya yi musu bayanin komai game da Jay,da ciwukan da ya samu,tunda Mami taji a yanayin da aka kawo Jay hospital ɗin take share hawaye tun ma bata ganshi ba,hankalin Mami bai ƙara tashi ba sai da suka shiga ɗakin da aka kwantar da shi,ciwuka all over his body an nannaɗesa da bandage,ƙafarsa ta hagu a saƙale saboda karayar da ya samu,Mami ta matsa kusa da gadon da sauri tana kallonsa sympathetically tana kuka ƙasa² mai cin zuciya,Dr Mustapha yace "sai haƙuri Hjy.. Allah ma ya taƙaita ai,idan da ace a yanda labari yazo da yanda muka ganshi ne sanda aka kawoshi nan,mu kanmu bamu yi zaton al'amarin zai tsaya iya haka ba" hankalin Mami sam ba ya kan abunda Dr Mustapha yake faɗa ita dai ta ɗanta kawai take,da ƙyar bayan Dr Mustapha ya gama musu bayanin komai then sarki Abduljalal ya nemi tafiya da Mujaheed gida,sanda aka gama shirya komai ambulance ɗin hospital ɗin ta ɗauki Jay zuwa airport,sarki Abduljalal ya yiwa Governor godiya daga nan suka juyo Kano da Jay. Lokacin da labarin abunda ya faru da Jay ya zo gidan sarautar,kaɗan daga cikin family'n ne suka iya yi masa fatan alkhairi,while da yawa daga ciki suke kallon abun a matsayin sakamakon bijirewa mahaifinsa da yayi. Bayan dawowarsu direct aka wuce da Jay part ɗin Mami,here da masu murna da masu taya ɓaƙin ciki suka fara zuwa taya Mami alhinin abunda ya samu Jay,ita kam gaba ɗaya ma ba ta iya magana saboda yanayin da Jay yake ya mugun ɗaya mata hankali,ganin tunda suka je Katsina har suka dawo bai farfaɗo ba har yamma. Guraren ƙarfe 7pm ya farka da wani irin ƙaran azaba,hawaye suna sauka cheecks ɗinsa,Mami ta shigo ɗakin da yake kusa da nata da sauri,tana kallon yanda yake kuka tace "sannu Mujaheed.. Bari a kira Dr" za ta fita Jay yace "Mami my head.." Da sauri ta juyo tana kallonsa tace "does it hurt?" Yace "ehh! It felt like it was going to take off,ina jin zafi da ciwo all over my body" sympathetically take kallonsa tace "sannu bari a kira Dr ya dubaka,in sha Allah za ka samu sauƙi" ta fita da sauri tana share ƙwallar tausayi,sanda Dr ya shigo ya duba Jay yayi masa allurai da za su rage masa raɗaɗi da zafin ciwon then ya koma bacci,a ranan Safiyyah ƙanwarsa dake aure London ta sauka ƙasar tare da autar su Jay Sulthana dake gurinta tana karatu,lokacin da suke shigowa sun tarar da shi yana bacci,suka fita bayan sun ga jikinsa suna share hawaye,a nan suka samu Mami a ɗakinta,Safiyyah tana kallon mahaifiyar ta su tace "Mami how Yaa Jay ya samu accident irin wannan?" A hankali Mami dake zaune saman pray mat ta idar da sallah ta basu labarin komai,Sulthana tana kallon Mami hawaye cike idanunta tace "duk ba kowa ya janyo matsalar nan ba sai Hjy Babba,akan me za ta dage tasa mai martaba tilasta masa auren wacce ba ya so? Akwai wanda aka taɓa yima auren dole ne duk family? Kawai sai shi saboda ba'a sonsa?" Mami ta ɗago tace "ya isa haka Auta,ba na son haka kin sani" Safiyyah dake zaune ta yi tagumi hannu bibbiyu tayi saurin sauke hannunta tace "ai gaskiya ne Mami kome ya samu Yaa Jay Hjy ce sanadi,da bata takurawa mai martaba ba da haka bai faru ba" Mami tace "shi uban naku baku ga laifinsa ba da ya dage shima? Ai shi ne mai babban laifi da baida ra'ayin kansa sai abunda aka ce.. Da ya tsaya akan ra'ayinsa babu wanda zai na zuwa masa da magana ya karɓa.." Shiru duk suka yi basu sake magana ba,Mami ta ɗauke kai ta ci gaba da lazimi. Wasa² sai da Jay ya shafe almost 2 weeks yana jinya kafin ciwukansa suka fara healing,karayan kam sai da ya sake samun one week sannan aka kwance,lokacin kuma sai ya tsiri wani sabon hali,haka nan yake wani irin ɗabi'u kamar wanda ke da matsalar shafar aljanu ko na ƙwaƙwalwa,ko yaya idan Mami taga ya zauna yana tunani sai ta tambayeshi me yake tunani me yake damunsa? Sai yace mata he feels like he has lost something very important a rayuwarsa,duk sanda yake irin maganar Mami sai tace "mene ne shi?" Sai dai ya girgiza mata kai yace "ban sani ba Mami,amma ina jin abun a raina" cikin haka lokaci yayi ta tafiya,su Safiyyah kuwa tuni suka koma London. Sanda Jay ya gama warkewa,wata rana suna zaune da Mami a parlon ta,saboda yawan tunanin da take ganin yana yi,yasa ta yanke shawarar yi masa maganar komawarsa India saboda tana tunanin hakan zai rage masa damuwar da yake ciki,sanda take masa maganar kai tsaye yace mata bazai komai ba ya haƙura da aikin zai nemi wani a nan,hakan yasa ta tuntuɓi mai martaba da maganar,shima ya yi na'am da maganar Jay,cikin taƙaiccen lokaci yasa aka nema masa aiki a first bank Nigeria,sanda ya fara aiki da su tuƙuru ya kama aikinsa,dama can kuma Jay yana cikin masu hazaƙa. A haka rayuwar ta fara juyawa,sai dai a gefen Jay kullum zuciyarsa cikin sanar masa take ya rasa abu mai girma,sai dai duk wanda ya takurawa kansa da son binciko abun take kansa zai fara wani mahaukacin ciwon da zai kaisa ga kwanciya matsanancin rashin lafiya,sai anyi da gaske kafin ya tashi,wannan dalilin yasa mai martaba ya shirya fita da shi ƙasar waje a duba ƙwaƙwalwarsa,ko ya samu wani matsala basu sani ba sanadin accident ɗin da yayi days ago.

*Some years later...*     

'''DAWAKIN KUDU L.G.A,KANO STATE,NIGERIA.'''
   '''Thursday evening...'''
 
       Around 5pm and some minutes a agogon mu na nan gida Nigeria,yammaci ne da ya kasance mai cike da tarin ni'imomi,kasancewar yanayi na lokacin damuna,hakan yasa daddaɗar iska kaɗawa zuwa kowane ɓangare,daga gabashi zuwa yammaci,kudanci zuwa arewanci,yayin da koraye shar ɗin ciyayi suka yi luf²,bishiyu suke rangaji saboda kaɗawar da iska ke yiwa rassansu,yanayin garin ya ɗan lumshe,yayin da jefi²n giragizai suke gudu a sararin samaniya suna yin gabashi suna curewa zuwa gagarumin hadarin da ako wane irin lokaci za'a iya saka rai da saukowar ruwan sama. Can daga ƙarƙashin ƙatuwar bishiyar darbejiyar da ta raba hanyar biyu,ta kuma yiwa gurin inuwa,wasu matasan samari ne guda uku,dukan su baza su wuce 20yrs ba,biyu daga cikinsu suna zaune kan wani busashshen itace,while the third one yana kwance bisa dandagaryar ƙasa ya tallafe backhead ɗinsa da hannuwansa biyu,duk da kasancewar gurin hanya yalwar inuwa da iska,shi ne musababbin da yasa mutanen garin suka mayar da gurin ya zama kamar wata mahaɗa ta su,wanda ba iya samari kaɗai ba hatta dattijai a mafi yawan lokacin da zafin gari ya busa sukan taru a gurin su sha iska,wani lokaci har idan kazo wucewa ka tarar da su suna ciye²n irin su gyaɗa,rake,da sauransu. Though daga nesa nake kallonsu,hakan bai hana hankalina ya fi karkata kan matashin dake kwance ba,wanda tsananin kyaunsa ya so ya ruɗar da ni,gashin kansa dake a kwance luf² baƙi ƙirin yana kyalli gwanin sha'awa ya zubo ya rufe almost rabin fuskarsa,ɗan sajen da ke kwance saman kyakykyawar fuskarsa ya haɗe da siririn gemunsa dake nan very light,har ana iya hangen fresh skin ɗinsa,cikakkun girorinsa da suke nan thick kamar sumar kansa kaɗan basu haɗe ba ta tsakiya,yayin da madaidaitan idanunsa masu ɗan sauƙin haske suke kallon ganyayen bishiya da iska ke motsawa,a little bit light reddish lips ɗinsa ma su taushi suke motsawa kamar mai raɗa ko yake furta wani maganar,sai dai a zahirin gaskiya ba komai yake furtawa ba,kawai yana motsa bakin nasa ne,even though a kwance yake,hakan bai hana na tantace tsawonsa ba,yadda fatar jikinsa ke fitar da wani irin sheƙi da danshi² kamar wanda ya fito daga wanka,uwa uba kuma da ta kasance a lulluɓe da zara²n lullausan gashi wanda suka sake taimakawa wajen ƙawatuwar halittar jikinsa. Sanye yake da yellow colour t-shirt mai round neck,wanda ya mugun amsarsa,sai black skinny jeans,since ya zo gurin yayi shiru bai tanka ko ɗaya daga cikin maganar da abokan nasa ke yi ba,but kyakykyawan kallon tsanaki ɗaya za kayi masa ka fahimci damuwar dake bayyane saman kyakykyawar fuskarsa ita tasa shi yanke irin hukuncin. Tun daga nesa yanayin yanda yarinyar take gudu ƙafafunta babu ko takalmi,da sauri ɗaya daga cikin samari biyun dake zaune ya taɓashi,idanunsa har sannan akan hanyar da yarinyar ke zuwa yana sake studying yanayin da take ciki,da wani muryar da yake bayyanar da tashin hankali ya furta *"ASLAM!* Wake up ur Behen (sister) is coming!" Banza da shi Aslam dake kwance yayi,haɗe da mayar da idanuwansa ya lumshe,sanin a times abokan nasa sukan tsokanesa,wannan dalilin yasa ko yanzun ma yaƙi tankasa,he thought kawai tsokanar da suka saba yi masa ne,kasancewar tun zuwansu suke masa magana ya ƙi kulasu,and sun san a duniya idan ba Behen ɗinsa ko mahaifiyarsa suka ambata ba,bazai taɓa kula su ba,har zuwa sanda shi da kansa ya gaji da shirun,though ya tabbatar he clearly heard,a ɗan fusace ya sake bugar gefen shoulder sa yace "dallah can kana ji ina sanar maka ga ƙanwarka nan zuwa,do u think i'm kidding? Just look at how take zuwa kaga ko takalmi babu a ƙafarta,and it seems that something happened tazo sanar maka.." Kafin ya ƙarasa faɗan maganar Aslam dake kwance ya zabura ya miƙe zaune yana waro idanuwansa,dai² nan yarinyar ta ƙaraso,numfashinta yana fita sama² saboda gudun da tayi tace "Aslam bb.. Bhai.. Mommie!" Sunan Mommie kawai da yaji ya fito bakinta,yasa bai jira ya gama jin abunda za ta faɗa ba,ko ya yi magana ya miƙe a hanzarce ya bar gurin aiki a rufa masa baya...

   *This book is not for free,it's #300 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ku iya tuntuɓar wannan number +22770766074.*

     

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

KALLO YA KOMA SAMA!Donde viven las historias. Descúbrelo ahora