💠💠💠💠💠
©®AS-2021.*♡KALLO YA KOMA SAMA¸.•💥*
_((SHAHO YA ƊAUKO GIWA))_'''#ƊAN MACE AGAIN'''
Bʏ
*HAWWA MUH'D USMAN.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*WATTPAD LINK:* https://www.wattpad.com/story/231697613?utm_medium=com.whatsapp&utm_source=android&utm_content=story_info
*LAST FREE PAGE*10
#Catastrophe
Dukansu suka zubo masa idanuwa da mamakin yanda ya sake yana dariya,Naina kam da Afnan sanda suka tallafe cheecks suka shagala da kallonsa,dama kuma suna kusa da su,irin kallon da yaga suna masa ya ankarar da shi,here ya ɗan saita kansa yana kallon M.A yace "Uncle da gaske?" M.A ya jinjina masa kai,Aslam ya gyaɗa kai bai sake cewa komai ba,M.A yayi murmushi yace "u didn't believe,right?" Aslam ya girgiza masa kai yace "not at all Uncle,i'm just confused" wani murmushi M.A yayi,yace "can i sent u?" Aslam yace "do u need anything?" M.A ya gyaɗa masa kai yace "idan ka fita ka kira min head ɗin garin nan,ka sanar masa suna na" Aslam yayi murmushi yace "tou Uncle.." Sun jima suna hira,sanda akayi kiran sallar maghreb,Aslam ya fita masjeed shi kaɗai,daga can ya ƙarasa gidan mai gari,sanda ya aika yaro yayi sallama da shi,mai gari ya leƙo,yana ganin Aslam ya ɗaure fuska yace "kai ne kake sallama?" Aslam yace "ehh! Aiko ni akayi" mai gari sai kallonsa yake kamar zai koma,ya daure dai yace "wa ya aiko ka?" Aslam yace "Uncle ne" kasa maimaita kalmar da yaji Aslam ya faɗa yayi yace "wa kace?" Aslam yace "Uncle! I mean Barr.Mujaheed Ali" wani murmushi mai gari yayi yace "kai a ina ka sanshi?" Aslam yace "yana gidanmu ya ma ce na kira masa kai ne" mai gari ya dunga kallon Aslam with suspicion,yace "kace yana gidan ku?" Aslam ya gaji da maimaita tambayoyin ya daure yace "ehh" mai gari dai bai yarda ba amma haka yace da Aslam "tou muje na gani,Allah sa ba ƙarya ka gindaya min ba" wani kallo Aslam yayi masa ya gyaɗa kai ya juya,a soron gidan mai gari ya tsaya yana kallon Aslam dake ƙoƙarin shiga gida yace "tou ka sanar masa ina nan" Aslam yace "tou" ya wuce ya shiga gidan,har lokacin M.A yana tsakar gida saboda zafin da ake kwaɗawa,kasancewar damuna tasowar hadiri a ƙasa² yasa garin yake a tsaye babu alamun iska,ƙarasawa yayi gurin da M.A yake yayi ƙasa da murya yace "Uncle he's there" M.A yace "where?" Yace "yana soro yana jiranka" M.A ya gyaɗa kai yace "alright! Let's go together.." Tare suka fito har soro,kasancewar da haske sosai soron,M.A yayi sallama Aslam yana biye da shi,mai gari yana jin maganarsa ya wani buɗe idanuwa,da sauri ya ƙarasa jikinsa har wani shaking yace "Allah ya taimakeka.." M.A yayi murmushi yace "ranka ya daɗe" ya miƙa masa hannu,hannu bibbiyu mai gari ya miƙo ya riƙe hannun M.A,har wani rusunawa yake yace "ashe da gaske yaron nan yake.. Ya je yace kana kira,ban yarda ba na dai biyo shi na ƙarewa ƙaryarsa gudu.." Aslam ya ɗaure fuska yana kallon mai gari,M.A yace "a'a My son ai ba ya ƙarya.." Mai gari yace "dama ka sansu ne?" M.A yayi murmushi yace "sosai ma" kan mai gari ya ɗaure yace "kuna da alaƙa da Nani dama amma ban taɓa sani ba sai yau?" M.A yace "tou ai kasan yanayin duniyar komai sai lokaci ya yi ake saninsa.." Mai gari ya gyaɗa kai yana gaisar da M.A respectfully,M.A yayi wani murmushi yace "Mlm Bawa dama wani tambaya nake son maka" jiki na ɓari mai gari yace "tou yallaɓai Allah sa na sani" M.A yayi wani murmushi yace "mene ne tsakaninka da Aslam? Ko nace me ya haɗa ka da family'n Nani ka shigo cikin gidan nan 3 days ago?" Mai gari yace "a'a yallaɓai babu komai wallahi sai alkhairi.. Babu abunda ya taɓa haɗa ni da su" kallonsa M.A ya dunga yi yace "amma na ji kamar ana cewa ka yi maganar koransu daga garin nan,haka ne?" Mai gari ya girgiza kai yace "niiiihhhhh! Yallaɓai.. Me sukai min zan koresu? Gidan su ne fa suke zaune cikinsa ba haya ba" M.A ya dunga kallonsa yace "ohh! Dama mallakin su ne gidan?" Mai gari yace "ƙwarai kuwa,tun zuwansu garin nan suka siyi gidan sukai masa gyara na gaske.. Idan ka kalli gidajenmu da nasu ai za kaga ya bambanta... Sam zaman garin nan ma bai dace da su ba,har yau muna mamakin dalilin da ya kawo su garin nan.." M.A ya gyaɗa kai yace "tou! Shi kenan,dama kiran da nayi maka,na tambayeka naji nawa aka yiwa gidan kuɗi.. Amma tunda haka ne ta kwana gidan sauƙi.. Duk abunda ya tashi idan akwai buƙatar sake nemanka zan aiko a kira ka.." Mai gari kamar zai kwanta a gaban M.A yace "toh.. Tohhh.. Ranka ya daɗe,Allah taimaka.." M.A yace "ameen².. Na gode Mlm Bawa" mai gari yace "nine da godiya ranka ya daɗe.." M.A yace "babu komai.. Sai an jima" ya miƙa masa hannu suka sake yin musabaha,sanda suka juya suka shiga gida then Mai gari ya fita zuciyarsa taf da tunanin maganganun M.A,tabbas ta wani ɓangaren shi kam ya hango mugun kamar Aslam da M.A,ya jima yana son gano da waye yaron yake masa kama,saboda shi dai ya san mai kamannin,amma ya kasa sai yau yaga zahiri,shin mene ne tsakanin M.A da Aslam da su Nani? Mene ne dalilin zamansu a ƙauyen? Mene ne dalilin M.A na barin iyalinsa a irin wannan garin? Tarin tambayoyi makamantan wannan haka suka danƙare a zuciyar Mlm Bawa (Mai gari). Suna shiga ciki Aslam ya ɗago yana kallon M.A with suspicion yace "Uncle can i ask u something?" M.A yayi murmushi yace "just go on.." Aslam yace "me yasa baka faɗa masa gaskiyar alaƙarmu ba ka ɓoye?" M.A ya juyo yana kallon Aslam yace "saboda ina so ka rama abunda yayi maka" murmushi Aslam yayi yace "ok.. I understand.." Wasa² sai da M.A ya cika sati cif cikin garin bai taɓa fita ba iyakarsa bakin soro,banda mai gari da Yaawo babu wanda ya san yana gidan. Zuwa lokacin kaf ragamar gidan a hannunsa yake,duk wasu hidimomi da wahalhalu shi yake musu,tun Nani tana hana shi har ta saba,duk da abincinsu dama ba irin na sauran gidaje bane amma zamansa gidan yasa komai sake canjawa,sau tari idan ba ruwa akayi ba idan ka shiga gidan za ka same su a tsakar gida suna hira,saboda yanda suka yi wani mugun sabo,baza ka taɓa cewa a ɗan ƙanƙanin lokaci suka haɗu ba,wani lokaci kuma za ka tarar yana taya Nani kaɗin auduga,suna hira tana bashi labarin India da irin al'adunsu. Yauma ɗin kamar kullum,kasancewar ranar Thursday,Naina sun shigo tare da Afnan da taje ta rakito,M.A kuma yana zaune kusa da Nani suna hira,Khaniiy kam tana kitchen tana shirin girkin dare,time to time take ɗan saka baki a hiran da suke akayi sallama,Sultan abokin Aslam ya shigo,Nani ta amsa tana kallonsa tace "O'o! Ku dai yaran nan baku da kirki,idan ba neman Aslam kuke ba ba'a taɓa ganin ƙafafuwan ku a gidan nan" murmushi yayi ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta ta amsa,yana kallon M.A dake taya Nani kaɗi,Afnan da Naina sun saka shi gaba sai so suke ya basu saboda Nani ta hanasu,ya gaishe shi,M.A ya amsa fuskarsa da murmushi yace "dama Aslam yana da aboki bai taɓa sanar min ba?" Nani tace "bar wannan mutumi da shiririta kai dai *JAHEED* wani lokaci sai yayi kwana uku bai fita ba,sai sun gaji suzo nemansa" M.A yace "Allah sarki,ai abotar kenan,amma bai kyauta ba,tunda ya san suna zuwa nemansa idan suka ji shiru.." Nani tace "kai kake wannan tunanin,shi wancan mutumi dai ko gajiya da zaman gida ba ya yi kamar mace" fitowa Aslam yayi daga ɗaki fuskarsa ɗaure yana kallon Nani yace "me nayi kuma kike bada labari na? Dama an kwana biyu baki ce na yi wani laifin ba" M.A dai sai murmushi yake yace "abokanka ne suka zo neman ka" kallon Sultan ya dunga yi,Sultan ya ƙarasa ya miƙa masa hannu,yace "kwana biyu shiru ba ka fitowa,sai dai mu haɗu a masjeed.." Aslam yace "yeah! Ina karatu ne,mun kusa fara exams" Sultan yace "eyyahh! Ai bamu sani ba.." Baban'nan dake waje yana jiran Sultan yayi sallama shima,sanda suka gaisa da Nani yana kallon M.A ya gaishesa,ya miƙawa Aslam hannu,suka ɗan taɓa hira kafin suka yiwa Nani sallama suka bar gidan. A hanya suna tafiya Sultan yace "abun mamaki.." Baban'nan ya kalleshi yace "where?" Sultan yace "kai baka ganshi ba?" Baban'nan yana kallon Sultan yace "uhmn! I never thought Aslam zai taɓa ɓoye mana mahaifinsa yana da rai" Sultan yace "na yi mamaki saboda idan mun tambayesa ce mana yake ta mutu" Baban'nan yace "halin ɗan Adam ya gwada mana,dama kuma mu muke masa shishshigi,shisa ya ɓoye mana" Sultan yace "ai yanzu sai muyi baya²" Baban'nan yace "ka faɗa ma wani ya ji" sanda suka rabu kowannensu yana tunanin dalilin da Aslam zai ɓoye musu gaskiyar cewa mahaifinsa yana raye,Sultan ya shiga gida ya zauna yayi shiru yana tunani,Inna mahaifiyarsa sai magana take masa bai ji ba,sanda tace "wai tunanin me kake ina magana ka yi min shiru?" Sultan ya ɗan juyo yace "ni ne?" A fusace Inna tace "idan ba kai ba akwai wani ne?" Yayi ƙasa da kai yace "kiyi haƙuri" tace "tunanin me kake nace?" Ajiyar zuciya yayi yace "Inna dama babansu Aslam yana raye?" Da sauri Inna tace "kamar ya?" Yace "yanzu na ganshi a gidan da idona" ta dunga kallonsa tace "shi baban nasu zuwa yayi?" Sultan yace "tou nima dai ban sani ba,amma na ganshi yanzu da muka je nemansa,kwana biyu bamu haɗu ba" mamaki ne ya cika Inna ta dunga kallonsa ta kasa magana,can dai tace "ina zuwa" taja mayafinta a jikin igiyar shanya ta fita gidan,kai tsaye gidan Nani ta tafi,sanda tayi sallama ta shiga,Nani da M.A sai hira suke suka amsa,ta ƙarasa tana kallon M.A tun daga nesa,sanda suka gaisa da Nani,M.A ya gaisheta suka gaisa da Khaniiy dake fitowa ɗaki sanye da hijab,hira suka ɗanyi da Nani then tayi musu sallama,bayan fitarta daga gidan kusan mata 7 ne suka shigo,sanda suka fita Nani ta taɓe baki tace "za kuji da munafurcin dake ranku" M.A yayi murmushi bai ce komai ba,kafin maghreb kaf garin babu inda gulmar bai kai ba,majalisa² ko ina sai maganar ake,sanda Aslam ya fito sallah,yaga mutane sai kallonsa ake,abun ya bashi haushi ya wuce fuskarsa ɗaure,lokacin da yake fitowa masjeed bayan isar da sallah,akwai wani mutumin da yaji maganar,so da yake yana da ɗan matsalar ƙwaƙwalwa mamaki ya ishesa,lokacin Aslam yana tafiya a hanya,mutumin ya ƙwalo masa kira,Aslam ya ɗan tsaya yana kallonsa har ya ƙaraso,respectfully ya gaishesa yace "Baba Adahama lafiya kake kira na?" Mutumin yayi shiru yana kallon Aslam,Aslam ya ɗan girgizasa yace "Baba Adahama" firgita mutumin yayi kamar wanda ya farko daga bacci,Aslam ya dunga kallonsa yace "wani abu ne ka tsayar da ni?" Mutumin yayi murmushi yace "dama wani magana naji,shi ne nake son tambayar ka" Aslam ya gyara tsaiwarsa yace "tou! Ina ji" mutumin yace "da gaske ne da naji ana cewa mahaifinku ya dawo? Dama kuna da mahaifi?" Yace "a ina kaji?" Mutumin yace "duk gari ai babu inda maganar bai zagaya ba" Aslam ya dunga masa wani kallo kawai ya juya ya bar gurin ransa a ɓace,yana shiga gida ɗakin Nani ya nufa yayi sallama,sanda ta amsa ya shiga ya zauna gabanta hankalinsa a tashe,Nani dake kallonsa tace "lafiya Aslam?" A hankali yace "Nani me yake shirin faruwa?" Nani tace "a ina?" Yace "yanzu Mlm Adahama ya tare ni a hanya wai ya ji ana cewa mahaifinmu ya dawo" Nani ta dunga kallonsa,tace "tabbas za'ayi haka" Aslam yace "saboda me Nani?" Tace "tsananin kamar Mujaheed da mahaifinka da kai kanka dole duk wanda ya gansa yayi zargin mahaifinka ne shi.. Ni kaina na kasa yarda har yanzu ba Jaheed ne ya dawo ba" Aslam yayi shiru ya kasa magana,can dai ya tashi ya fita ɗakin. Ɗakinsa ya shiga ya samu M.A yana karatun Alqur'ani,ya ƙarasa ya zauna ƙasa yayi leaning bayansa toward ƙatuwar katifarsa,idanunsa a kulle har M.A ya gama yayi addu'ah,sanda ya juyo a hankali ya taɓa Aslam yace "hey My son" a hankali Aslam ya ɗago yana goge idanuwansa,fuskarsa cike da damuwa ya ƙaƙalo murmushi,M.A ya dunga kallonsa yace "what really make u cry?" Aslam ya girgiza kai yace "ba kuka nake ba Uncle.." M.A ya dunga kallonsa,yace "why are u lied to me?" Da sauri ya kalli M.A ya kasa magana,can ya daure yana girgiza masa kai yace "babu komai fa Uncle" M.A yace "alright.. But ina son magana da Nani.." Aslam yace "yanzu?" M.A ya gyaɗa masa kai,Aslam yace "okay!" Ya tashi ya fita,not too long ya dawo yace "Uncle ta ce kaje" M.A ya tashi suka fito yana riƙe da hannun Aslam,ƙofar ɗakin Nani yayi sallama,Nani tace "bismillah shigo Mujaheed" M.A ya shiga Aslam yana binsa a baya suka zauna,sanda suka gaisa da Nani,M.A yace "Nani.. Dama ina son sanar maki,in Allah ya kaimu gobe zan tafi.. Na yi magana da D.P.O na sanar masa komai,so yanzu sun kammala duk shirin da za suyi,ya ce zan iya komawa gida,za susa ido akan duk wanda suke da hannu cikin abunda ya faru.." Nani ta gyaɗa kai fuskarta da fara'a tace "tou! Allah ya amince.." Ya amsa yana murmushi,yace "sai abu na biyu da nake son faɗa idan babu damuwa.." Nani tace "a'a babu komai Mujaheed,ai kai ɗan gida ne,faɗi duk abunda kake son cewa" yayi ƙasa da kai yace "idan babu damuwa,ina son mu tafi tare kuga inda nake" murmushi sosai Nani tayi tace "ai dan wannan ba wani abu bane,Allah ya kaimu goben.." Ya amsa shima yana murmushi,sun jima a ɗakin suna ta hiran tafiyar,kafin suka mata sallama suka tafi. A ɗaki lokacin suna kwance,duk sun yi shiru tsakaninsa da Aslam,can Aslam yace "Uncle!" A hankali M.A yace "Aslam.." Aslam da jikinsa yayi sanyi yace "yanzu idan ka tafi shi kenan?" M.A yayi wani murmushi yace "a'a! Ba shi kenan ba" Aslam yayi murmushi,sai bai sake magana ba har bacci ya ɗaukesa. Da safe sanda suka gama shiryawa,M.A yana sanye da Jallabiya ya rufe kansa da hirami,Aslam yana sanye da ƙananan kaya,sai Nani da Yaawo,Afnan,Naina da Khaniiy,suka fito all together,Aslam ya rufe gidan suka shiga taxi biyu da ya ɗauko musu cherter drivers suka ja. Tafiyar 45 minutes ya shigo da su cikin garin Kano,M.A yana gaban ɗaya motar yana ma driver'n kwatance,har sanda suka shiga G.R.A ɗin,basu yi tafiya mai nisa sosai ba,suka tsaya bakin wani makeken get,gidan was big and cozy,faɗan tsaruwarsa kuwa abun sai ya zama ƙauyanci,tun daga waje sanda motocin suka yi parking M.A ya fara sauka,yana sauke wani numfashi haɗe da faɗin "Alhamdulillah alaa kulli halin.." Aslam ya sallami masu taxi,su Nani duk sai kallon M.A suke,sanda yayi murmushi yace "Nani mu ƙarasa" Nani tace "tou! Mujaheed" yana forefront hannunsa riƙe da na Aslam,suka ƙarasa get yayi knocking,daga ciki get keeper yayi magana then ya fito,yana ganin M.A yayi baya kaɗan yana faɗin "ranka ya daɗe.. Alhamdulillah.." M.A yayi murmushi yace "Mlm Idiris.. Mun same ku lafiya?" Mutumin dai kallon M.A kawai yake fuskarsa a faɗaɗe da farin ciki,M.A ya shige ya barshi tsaye sai surutu yake. Since suka shigo compound ɗin gidan,suke kallon uban dukiyar da aka narkar,parking spot kansa mutum ya kalla sai ya kusa suma,suka ƙarasa balcony,M.A ya danna door bell,suna tsaye gurin aka ɓude ƙofar,ƴar kyakykyawar yarinyar da baza ta wuce sa'ar su Naina ba,ta dunga juya manyan idanunta tana kallon mutanen,ganin babu wanda ta sani cikinsu tace "wa kuke nema?" Zare hiramin kansa M.A yayi ya ƙaraso kusa da ita,yana mata murmushi yace "hey cutie!" Zaro idanuwa tayi ta ƙwalla wani ƙara,da gudu ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesa,M.A yayi murmushi yayi hugging nata back,cikin kuka tace "Daddy where have u been? All this while ina ka shiga ka barni?" Ɗagota yayi yana share mata hawayen idonta yace "i'm here my cutie.. Stop crying.." Ta ƙanƙamesa da gaske tana girgiza masa kai yace "Daddy i know za ka gudu ka barni kuma" yayi murmushi yace "no bazan tafi na barki ba" tace "promise?" Yace "yeah promise" ɗan sakinsa tayi ta kama hannunsa ta ƙanƙame tana janyosa,tace "Daddy taho muje na nunama Mummy kai.. Always tana cewa baza ka dawo ba,mun yi kuka da ita sosai da bamu ganka ba" ya buɗa idanuwa yace "really?" Ta gyaɗa masa kai,tare suka shiga ko kula da mutanen da suke tare bata yi ba sai da suka shigo suka zauna,ta miƙe da sauri tana kallonsu,a hankali tace "ina yini?" Khaniiy tayi mata murmushi,da sauri yarinyar ta wuce stairs,M.A da ya bita da kallo yace *"SAMRA.."* Ta waigo kaɗan tace "Daddy zan sanarwa Mummy ne" ya gyaɗa mata kai a hankali,da gudu² ta ƙarasa haurawa,not too long suka sauko da wata kyakykyawar mata da baza ta wuce tsarar Khaniiy ba,tun daga nesa take sakin murmushi tana kallonsu Nani,tace "sannun ku da zuwa.." Gefen M.A ta nufa tana masa murmushi hawaye cike idonta tace "My Barrister.." M.A yayi mata murmushi,lokaci ɗaya yaga ta tsaya ta ƙi ƙarasowa,ya dunga kallonta,yaga sai kallon sa take,eye balls ɗinta suna juyawa,fuskarta da wani tashin hankali kwance a kai ta nuna Aslam tace "Barr. Waye wannan yaron?" M.A yayi wani murmushi yace "sit please i'll explain it.." Da ƙarfi sanda hawaye suke saukowa fuskarta tace "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. M.A me kake son faɗa min? Me za kace min bayan abunda idanuwana suke gani.. Wane ne wannan yaron da kuke kama? Tell me who's this young man da kuke tare..?" Ta ƙarasa cikin wani ƙaraji,lokaci ɗaya kuma ta zube gurin a sume...
_#Turƙash... Wannan shi ake kira gobara daga kogi.. Ko wane irin al'amari ne wannan da yake neman ɓillowa haka kuma? Wai wane ne wannan MUJAHEED ɗin? Mene ne alaƙar dake tsakaninsa da ASLAM da kowa yake ganin kamar da suke da juna? Idan ta tabbata JAY ne ya dawo a wata suffa ta daban,shin mene ne hujjarsa na ɓoye asalinsa gare su? My peoples ni kaina i was confused,na kasa gane mene ne yake shirin faruwa.. Tabbas na san makaranta littafin KALLO YA KOMA SAMA! Kowa ka bincika ransa akwai tarin tambayoyin nan wanda ni kaina su ne danƙare cikin kaina,but duka da ni da ku,sai nace mu haɗu paid group idan Allah ya nufa.. Masoya REAL-SMASHER a motsa,idan kun shirya jin ƙarshen wannan labari maza garzaya kiyi paying kuɗin karatunki,inda za kiji warwarar wannan tashin hankali da ya ɓillo lokaci lokaci ɗaya.. Ina yi muku son so tare da fatan alkhairi masoya na,masu jiran free pages su ƙare daga yau sun ƙare. Na gode sosai da nuna soyayyar ku gare ni._
*-KALLO YA KOMA SAMA-300*
*-IN-LAWS-200*'''Idan duka kike so za ki biya #500,idan ɗaya kike so kuma za ki biya kuɗinsu kamar yanda yake a sama,idan ba kya son group,za ki biya 1k duka biyu,idan ɗaya kike so za ki biya #500,Via 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,Access bank. Dan Allah idan kuɗin da za ki tura ya wuce #200 kada ki tura min recharge card,kije gurin masu POS su tura,card ya min yawa a line na. Na gode.'''
#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.
YOU ARE READING
KALLO YA KOMA SAMA!
Historical Fiction... KALLO YA KOMA SAMA! Hausawa suka ce SHAHO YA ƊAUKO GIWA. Anya kuwa haka yana iya faruwa,duk girman GIWA ace SHAHO ya ɗauke ta? Duk lalacewar GIWA ko ta mutu ta fi ƙarfin jan KIYASHI..