💠💠💠💠💠
©®AS-2021.*♡KALLO YA KOMA SAMA¸.•💥*
_((SHAHO YA ƊAUKO GIWA))_'''#ƊAN MACE AGAIN'''
Bʏ
*HAWWA MUH'D USMAN.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.**FREE PAGE*
'''Yaa rabb! Provide good health to my friend with some good wealth too,may the smile on her face be brightened up and new.. Wish u quick and speed recovery Habibtii.. Please my peoples kusa NU'AIYMA ABDULL marubuciyar ONE BLOOD cikin addu'oinku..👏'''
09
#Disfavour
Bayan tafiyar mai gari daga gidan,Aslam ya shigo ɗakin yana kallon mutumin respectfully yace "Uncle za ku gaisa da Nani (Grandma)" mutumin yace "tou Aslam" ya tashi suka fito tare Aslam a forefront yana binsa,ƙofar ɗakin Nani Aslam yayi sallama,Mommie dake fitowa ɗakinta za ta shiga toilet taga mutum tsaye bakin ƙofar ɗakin Nani,a ɗan ruɗe ta fara ƙoƙarin komawa,sanda ya ɗago kai akayi sa'a itama ta juya,suna haɗa ido tayi cilli da butar hannunta ta fasa wani razanannen ƙara,da sauri Nani dake ɗaki tace "lafiya? Ihun mene ne haka ɗin kuma?" A mugun firgice Mommie tace "Ammi! Fito kiga" da sauri Nani ta taso tana faɗin "me zan gani ne Khaniiy?" Mutumin dake tsaye ta shiga nuna mata jikinta was vibrate tana cewa "sss.. Shhhh.. Shi ne Ammi.. Wallahi shi ne ya dawo" hawaye har sun fara zarya a fuskarta,Nani kam bata fahimci me take nuna mata ba,tace "Khaniiy! Nutsu ki min bayani shi wa?" Da ƙarfi tace "ga shi nan a bayanki,wallahi shi ne,JAY ne" a ruɗe Nani ta juya tana kallon inda take nuna mata,saurin yin baya tayi tana dafe ƙirji tace *"JAHEED!"* Mutumin ya dunga kallonsu da wani irin ruɗani yace "wane ne shi? Dan Allah kun sanni ne?" Sanda yayi magana kuma sai duk suka tsaya kallonsa sun kasa tabbatarwa,shi ne ko ba shi bane? Nani ta zuba masa idanu a tsorace tace "ba Mujaheed bane?" Ya girgiza kai yace "a'a shi ne? Amma dan Allah wane Mujaheed ɗin?" Sanda yayi magana for the second time Nani ta dunga kallonsa ta kasa yarda da abunda kunnuwanta suke jiye mata,tace "ya ya ne sunanka bawan Allah?" Yace "Mujaheed" shiru tayi tana maimaita sunan tace "shin ku ƴan biyu ne?" Ya girgiza mata kai yace "ni da wa?" Tace "fara amsa min tambayata tukun" yace "a'a Mama,ni kaɗai mahaifiyata ta haife ni" Nani dai sai kallonsa take unbelievable tace "ikon Allah.. Wallahi babu maraba tsakanin ku,maganar kune kawai ya bambanta ku" gaba ɗaya kalaman Nani sun sa shi shiga ruɗani yace "wane ne shi ɗin?" Numfashi sosai Nani ta sauke tace "labarin yana da tsayi.. Amma bawan Allah shigo daga ciki muyi magana" Nani ta shiga ɗakinta tace "Khaniiy! Yahan aayiye..(Come here)" ƙaton pray mat family size ta shimfiɗa musu a ɗakin,suka shigo suka zauna,Aslam sai kallon Nani da Mommie yake speechless,gaisawa suka fara yi,Nani daİ har lokacin bata yarda mutumin da take gani a gabanta ba Jay bane,mutumin yana kallonsu duka kamar yanda suke yi yace "Mama wane ne shi wannan Mujaheed ɗin da kuke magana akansa?" Nani tace "mijin ƴata ne,shi ne kuma uban wannan yaro da ya kawo ka gidan nan" a hankali ya ɗan gyaɗa kai yana murmushi yace "Allah sarki! Ya mutu ne?" Kallon² akayi tsakanin Nani da Mommie,kafin Nani ta girgiza masa kai tace "a'a bamu sani ba" da mamaki ya dunga kallon Nani yace "tou me ya faru? Sakinta yayi? Ko ba ƙasar yake ba?" Nani ta sauke numfashi a hankali tace "tou! Sanin gaibu dai sai Allah.. Mujaheed yana raye ko ya mutu,Allah shi kaɗai ya barwa kansa sani" mutumin dake ta sauraron Nani ya sauke ajiyar zuciya yace "Mama na kasa gane maganarki,dan Allah ina kuka taɓa haɗuwa da shi?" A hankali Nani da lokaci ɗaya taji mutumin ya kwanta mata tace "tou! Mu da Mujaheed dai a India muka haɗu,kuma asalinsa shi dama ɗan nan ƙasar ne,karatu ya kaishi can sai kuma ya samu aiki,a can yake zama har sanda suka yi aure da Fatima,bayan Allah ya azurta su da wannan Yaro,rana ɗaya ya shirya zuwa ya sanar da iyayensa maganarta,tou fa shi ne har yau da nake ba ka labarin nan bamu sake haɗuwa ba.." Mamaki shimfiɗe saman fuskarsa yake kallonsu,zuciyarsa cike taf da tarin tambayoyi,a hankali ya girgiza kai yace "Allah ya kyauta.." Nani ta amsa,Khaniiy kam har lokacin kuka take ƙasa²,abunda ya faru 15 yrs back yana sake dawo mata fresh a ƙwaƙwalwarta,Nani dake bata haƙuri tace "ki bar kuka haka nan Khaniiy.. Idan Allah ya rubuta za ki haɗu da shi,duk wahalar nan da muka yi sai kiga ya zo ya wuce kamar ba'a yisa ba,sanda tayi mata nasiha sosai kafin tayi shiru,shi dai mutumin nan kallonsu kawai yake da tausayi. Can bayan wani lokaci Nani tana kallon copy ɗin Jay dake gabanta ta sauke ajiyar zuciya tace "bawan Allah.. Ashe haka abu ya faru da kai daren jiya?" Ya gyaɗa kai yana sauke numfashi yace "wallahi Mama ai na auna arziki.." Nani tace "tou! Allah ya ƙara tsarewa,ya rabaka da sharrin maƙiya" ya amsa,then suka gaisa,Khaniiy ta masa jaje jikinta a sanyaye,ita kam ta kasa yarda ba Jay ɗinta take gani ba,can dai Nani ta kasa haƙuri tana kallonsa tace "tou yaya ne sunanka ma kace ɗan nan?" Yayi murmushin ƙarfin hali yace "suna na Mujaheed Ali,amma colleagues ɗina da sauran mutane suna kirana M.A" Nani ta gyaɗa kai tace "Allah sarki,tou wane aiki kake kuma?" Yace "ni barrister ne.. Sai ɗan business da nake taɓawa" Nani ta wani gyaɗa kai tace "a'a cewa za kayi mutanen da suke farautarka dukiya suka gani" bai san sanda yayi murmushi ba,yace "dukiya Mama?" Tace "iiihhh! Me zance to? Ka ce kana business,sannan kuma kai lauya ne" yace "haka ne" tace "tou! Kaga ai da abunda suka gani tare da kai.. Ko kuma ka tsayawa wani shari'a ne kun yi nasara akansu shisa suke binka?" Yayi murmushi,sanda yayi flexing legs yace "a'a Mama.. Kawai dai turosu akayi" wani zaro idanu Nani tayi tace "tou! Ai kaji inda magana ya maƙale.." Ya jinjina kai,tace "tou ka san sune su ɗin da suka yo maka aiken a kasheka?" Wani murmushi yayi ya gyaɗa kai yace "na sani Mama.. Ƴan uwana ne" da ƙarfi Nani tace "a'uzhubillahi minashshaiɗanir rajiim.. A'a lamari ya lalace" yana girgiza kai yace "abunda har yanzu idan na tuna yake min ciwo,ban san dalilin da yasa suke son ganin bayana ba,ni da ba wani abu na tara ba" Nani tace "ai duk bazai wuce kan dukiyar da kake da shi ba.. Amma kada ka damu,akwai Allah zai saka maka,zai maka katanga tsakaninka da su" yayi wani murmushi yace "na gode sosai Mama" tace "a'a babu komai" yayi shiru kamar mai tunani,can yace "Mama zan iya roƙon wani alfarma?" Nani tace "tou! Allah yasa ina da ikon maka" yace "dama ina son roƙon ki ne,idan bazan takura maku ba na ɗan zauna nan tare da ku na wani lokaci kafin na tafi,tunda ban san me zanje na tarar ba idan na koma yanzu" Nani dake kallon Khaniiy da tayi shiru bata ce komai ba,tace "babu komai kayi zamanka,su kuma ƴan uwan naka Allah ya shirye su" ya amsa da "ameen" har ransa yake jin son Nani da Aslam,sai yake ganinta kamar mahaifiyarsa,yace "na gode maƙuta Mama,Allah ya saka maku da alkhairi" Nani tace "ameen².. Sai kayi zamanka nan tunda ga Aslam nan,duk abunda kake buƙata sai ya nemo maka,kai kam ai baka ga ta fita ba kuma barkatai,kada gantalallun mutanen su sake biyo ka.." Yace "tou Mama.. Gaskiya na ji daɗi da Allah ya haɗa ni da ku,ba don Allah ya sa Aslam ya taimakeni ba jiyan nan da yanzu sai dai labari na.." Nani tace "hakan ma an gode Allah ai tunda ya kuɓutar da kai.. Ka san idan da sauran kwanan mutum a duniya,sai dai ya sha wahala,amma ƙarshe sai ya cika dai² kwanakinsa.." M.A yayi murmushi,sanda ya yiwa Nani godiya yayi mata sallama,za su fita tare da Aslam da tun shigowarsu bai magana ba,Nani tace "aafff! Ka ga na manta ban tambayeka ba kuma.." Dawowa yayi ya zauna yace "tou! Mama Allah yasa na sani" tace "dan Allah ko ka haɗa wani alaƙa da gidan sauratar garin nan?" A mamakance ya ɗago yace "wane gari Mama?" Tace "can gidan saurata na cikin gari" yace "wani abu ne Mama?" Tace "a'a dama zan maka wani ɗan tambaya ne" ya girgiza kai yace "a'a Mama,na dai san wasu a cikin mutanen gidan" tace "tou kamar suwa ka sani?" Yace "ehh tou! Da yake ni barrister ne na ɗan san mutane da dama" tace "tou amma baka san Mujaheed ba?" Yace "ai Mujaheed a gidan sarauta suna da yawa Mama,kuma ni asalina ba ɗan garin nan bane,zama ya kawo ni tare da iyalaina" Nani tayi shiru tana tunani,can ta girgiza kai tace "ashsha! Tou ai tunda kaima baƙo ne babu lallaima ka sanshi" yace "haka ne" tace "tou amma baka san Mujaheed ba duk zamanka a garin nan?" Yace "Mama Mujaheed a garin nan suna da yawa ba lallai na san wanda kuke nufi ba" Nani tace "haka ne kuma" daga haka sai bata sake tambayarsa ba,suka fita tare da Aslam. Da azuhur sanda ƙura ya ɗan lafa mai gari ya leƙo ƙofar gida,gaba ɗaya ranan bai iya zaunawa fada ba,sai lokacin ya fito zuwa masallaci,sanda aka idar da sallah yaga mutane sun fara kallonsa,ya tashi sum² ya fita daga massalaci yana muzurai,yana fakar idanun mutane ya shige gida da sauri,a gefe ɗaya na zuciyarsa kuwa tunanin laifin da zai liƙama Nani da family'nta yake,saboda abunda tayi masa yau ya janyo zubar ƙimarsa,yana jin dole ma ya rama. 3 days later gaba ɗaya M.A a gida yake rayuwa,ko masjeed ba ya fita,garin kaf babu wanda yasan da zamansa a gidan,Nani ta hanashi zuwa ko ina,sai dai duk abunda yake buƙata Aslam yaje yayi masa,da yamma lokacin Aslam ya dawo skul,sanda ya shiga ɗaki ya samu M.A yana karanta wani littafi,ya gausheshi,M.A yana masa sannu da dawowa,dariyar da su Naina da Afnan da suke tsakar gida suna taya Nani kaɗi,though ba iyawa suka yi ba,but sun dage sai sun yi,sanda Aslam ya leƙo yana kallonsu yayi wani tsaki ya koma,M.A dake ɗakin yayi murmushi yana kallonsa yace "did anything happened?" Fuskar Aslam a ɗaure yace "duk sun cikama mutane kunne" M.A yayi murmushi yace "kai dai baka son hayaniya ne kou?" Aslam yace "Uncle! Baka san yaran nan ba,kamar zararru haka suke" M.A yace "tou ai muma sai mu fita mu taya su" Aslam yayi murmushi yace "Uncle ai baza ka iya ba" M.A yace "mene ne bazan iya ba?" Yace "kaɗi" M.A yace "mene ne shi?" Aslam yace "wani abu ne can na su na tsofaffi" M.A yace "abun tsofaffi.. Kaima ai wata rana za ka tsufa,kenan za kayi?" Da sauri Aslam yace "a'a Uncle mata ne suke yi" M.A yace "tou ai ban gane abun ba,muje na gani" fitowa suka yi tsakar gida,Aslam ya shimfiɗa musu tabarma daga bakin ƙofar ɗakin,Naina da Afnan suka gaishesa,yana murmushi ya gaisar da Nani,sanda suka zauna shi da Aslam yana kallon yanda Nani take kaɗin yace "Mama bari na tayaki" Nani tace "a'a baza ka iya ba Mujaheed,mu dai da muke tsofaffi ma yi" yayi murmushi yace "ai babu wahala" tace "anya? Kana ganin wannan mashiriritan sun kasa" yayi murmushi yace "Afnan kawo muga na gwada" Afnan tayi dariya tace "Uncle da wahala fa" ta taso da wanda suke yi ta kawo masa,ya karɓa tarin audugar dake cure guri ɗaya,ya fara murzasa,da suka ga ya fisu iyawa,Naina tayi ihu tace "Uncle kawo nima nayi" yayi murmushi yace "a'a karɓo wani gurin Nani" Nani dake ta kaɗinta tace "a'a bazan basu ba,lalata min abu suke,na ce su bari na gama na basu,tunda sun iya yin lagwani" ɗan kallonta yayi yace "mene shi kuma?" Nani tace "yana nan dai ana amfani da shi.. Ke Afnan ɗauko masa yaga irinsa" saurin tashi Afnan tayi ta ɗauko masa,ya kalla yayi murmushi kawai,Aslam dai yana zaune yana duba wani littafinsa,M.A ya kalleshi yace "My friend level nawa kake ne?" Aslam yace "300 level" M.A yayi saurin kallonsa yace "wane skul?" Yace "B.U.K" gyaɗa kai M.A yayi yace "maa sha Allah.. But kana da sha'awar yin business?" Aslam yayi murmushi yace "a'a Uncle" M.A yace "me yasa?" Yace "haka kawai" M.A yayi murmushi yace "ni kuma har na yi sha'awar sa ka hanya" ɗago kai Aslam yayi yace "ai Uncle ba na son sake taɓawa kowa kayansa,na fi son yin nawa,idan aka ce dukiyata ce,kuma ni zan ja ragamarta,babu wanda zai gaya min magana kansa" M.A ya gyaɗa yace "but ka taɓa yin aiki ƙarƙashin wani?" Aslam ya gyaɗa kai yace "ehh! Sai dai ban ji daɗi ba,shisa ba na son sake yi" M.A yace "will u tell me what really happened?" Aslam ya gyaɗa kai yace "haan!" Ajiye abun kaɗin hannunsa M.A yayi yayi concentrating on maganar da suke da Aslam yace "za ka iya sanar min abunda ya faru?" Aslam ya gyaɗa kai yace "ehh Uncle" M.A yace "okay! Just go on.." A hankali Aslam yace "akwai wani gidan gona a farkon hanyar shigowa garin nan,think ka gansa ma ɗan ta wajen ake wucewa a shigo nan.. So head ɗin garin nan shi ne yake kula da wasu abubuwa na gurin ko da yaushe,a yanda naji ana cewa mai gurin yana jimawa bai zo ya duba gurin ba,sai shi head ɗin namu ne yake ɗan investigating gurin.. And shi head ɗinnamu shi yake kula da ma'aikatan gurin,kuma sai da yardarsa ake ɗaukan ma'aikata,shi yake kai duk wanda yake so,lokacin da baban abokina Sultan ya nemar mana aiki gurin,saboda rashin shirin da muke da ɗan head ɗin yasa shi ɗora min laifin sata,tun daga ranar ban sake zuwa ba.. And i hate duk wani abu da zai fito ta hannusa,ba shi ba har aiki ƙarƙashin wani na ji ba na so.." Kallonsa kawai M.A ya dunga yi yana gyaɗa kai,a hankali yace "idan ya zama kai ne shugaban gurin fa?" Aslam yayi murmushi yace "ko a mafarki na zama shugaban gurin sai na rama abunda yayi min,and zan tona masa asirin irin satar da yake yi.." M.A yace "wa za ka sanar ma?" Aslam yace "owner of the property" dariya sosai M.A ya fashe da shi,Aslam ya dunga kallonsa with suspicion yace "Uncle! Stop laughing,da gaske nake fa" M.A ya dafa shoulder sa yace "kwantar da hankalinka.." Aslam yace "i didn't get u Uncle" M.A yayi wani murmushi yace "ai ko yanzu ma ka tona masa.." Tsayawa Aslam yayi yana kallonsa da rashin fahimta,M.A yace "ni ne mai wannan gurin da kake magana.." Buɗa idanuwa Aslam yayi yace "really?" M.A ya jinjina masa kai,kawai Aslam ya fashe da wani dariyar da yaja hankulan su Nani...
*This book is not for free,it's #300 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ku iya tuntuɓar wannan number +22770766074.*
#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

YOU ARE READING
KALLO YA KOMA SAMA!
Historical Fiction... KALLO YA KOMA SAMA! Hausawa suka ce SHAHO YA ƊAUKO GIWA. Anya kuwa haka yana iya faruwa,duk girman GIWA ace SHAHO ya ɗauke ta? Duk lalacewar GIWA ko ta mutu ta fi ƙarfin jan KIYASHI..