Who's who

127 15 4
                                        

💠💠💠💠💠
©®AS-2021.


      *♡KALLO YA KOMA SAMA¸.•💥*
        _((SHAHO YA ƊAUKO GIWA))_

'''#ƊAN MACE AGAIN'''
         
            

   *HAWWA MUH'D USMAN.*
       (Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*

*FREE PAGE*

                            07

#Who's who
 
       Since he left that place yake sauri ya isa gidan,but kamar ba tafiyar ma yake ba,ƴar kyakykyawar yarinyar data kai masa rahoto kuwa,da gudu² take iya binsa saboda mugun saurin da yake zubawa kamar wanda yake shirin tashi sama,at last sanda yaga tafiyar ya ƙi ƙarewa bai san sanda ya fara sassarfa ba. Daf da kwanar line su yana karyowa ya hango taron mutane cike a ƙofar gidansu,kai ka ce wani gagarumin taro ake yi,a tsorace Aslam ya sake zaro oily eyes ɗinsa ya nufi ƙofar gidansu zuciyarsa na bugawa da sauri²,cikin rashin sani sanda yake tunkarar gidan nasu yaji ya buge mutum,but firgicin da yake ciki bai sa ya tsaya dubawa ba,da sanyayyan muryarsa ya ɗaga hannunsa yace "maaf kijiyega! (Sorry)" daga haka ko waiwaye bai ba ya dunga ratsa mutane yana wucewa,sanda ya kutsa kai cikin soron gidan,tun daga nan yake jiyo muryar dattijuwar gidan cikin hayaniya tana faɗin "zancen banza zancen wofi.. Har mu za'a ma gorin asali Allah na tuba? Mutumi ya jira zai yi kallo da yardar Allah,lokacin da za ku san ko mu su waye baiba,ai har yanzun akwai sauran lokaci.." Dai² nan Aslam ya dafa shoulderta,a tsorace yana mata wani kallo yace "Nani! Aur kutch? Kya ho raha hai? Baat kya hai? (Grandma! Anything else? What's up? What's the matter?" A fusace Nani ta waigo idanuwanta sunyi jaa,cikin wani irin ɓacin rai tace "yo inba abun mutanen ƙauye ba,ƙauyen ma irin wannan,har *AFNAN* wani banzan ɗan mai unguwa zai kalla ya kira mara asali? Kana ji na ko ina faɗa maka,na rantse da Ubangijin da ya busa min numfashi,da ya san ko wane ne ubanta,ina da tabbaci a kan ko cewa akayi ya ɗaga kai ya kalleta,idan ya iya Allah ya lafta min albarka,kawai dan ta ce masa ita a gidansu karatu akasa tayi zai buɗe baki yace mata Ƴar Mace! Har Ƴaƴan mace suna da wani buri? Su da ba'a san asalinsu ba,wai dan ma ta samu ya ce yana sonta zai rufa mata asiri,idan ba shi ɗinba,waye kaf garin nan zai yarda yayi soyayya da ita? Ka ji min yaro dai da wani magana irin na taɓaɓɓu kafirawan farko.." Wani irin kallo mai cike da tsoro Aslam yake jifan Nani da shi tun da ta fara maganar cike da kaɗuwar irin maganganun da take fitarwa daga bakinta,nan da nan jikinsa ya ɗauki tsuma,cikin tsanani gami da ƙololuwar ɓacin rai,idanuwansa sun yi wani irin juyewa ya juya yana kallon inda Afnan ta rakuɓe daga can bakin ƙofa tana kuka ƙasa² da sharce hawaye,yana jifanta da wani mugun kallo a tsawace yace "uban waye ya kiraki Ƴar Mace?" Nani dake bayansa ta kama waistband cikin zafin rai tace "yo banda wannan fitsararren yaron ɗan mai unguwa meye ma suke kiransa ne ohoo? Kaf garin nan waye zai buɗi bakinsa ya faɗi irin maganar nan? Shi ne dan ta maresa ne ko mene ne ma tace min ya faru a kan maganar? Wai shi ne uban yake iƙirari da yi mana barazanar zai tashe mu,har yana cewa sai ya koremu daga garin yaga uban da ya tsaya mana,kamar dai wanda muka ci gadon gidan hannun tsohonsa.." Aslam dake sauraren bayanin Nani bai san sanda wani kyakykyawan murmushi ya suɓuce masa ba,ya ɗaga idanuwansa da suka rine a hankali ya sauke su kan Afnan dake binsa da kallon tsoro,da hannu ya yafito ta,babu musu ta taho inda yake,cikin sanyin maganarsa sanda ya riƙo hannunta da kyau ya tsayar da ita gabansa,da duka palms ɗinsa ya tallafe sides ɗin fuskarta yana jinjina kai,sounding a little bit angry,without ya tambayeta ba'asi yaji yanda al'amarin ya faru yace "daga yau duk wanda zai gaya maki magana,ko wane ne shi,duk girmansa in dai akan *ASALINKI NE* ban lamunci ki ɗaga masa ƙafa ba,duk girman mutum,ko da shi mai garin ne da kansa ba ɗansa ba,idan ya ɗaga miki yatsa,if kina da daman karyawa,ki karya yatsar da aka ɗaga miki,if not ki ɗaga na ki yatsar ki mayar da martani,matuƙar mutum bai riƙe girmansa ba ya zubar,na ba ki daman ki taya sa ɓararwa.. Ni nan Yayanki zan tsaya maki akan komai,zan ga uban wanda zai taɓa ki,duk abunda zai faru ya jima bai faru ba,babu uban wanda muke tsoro kin gane?" Daga haka bai ƙara cewa komai ba ko jiran amsarta ya saketa ya juya cikin fushi ya nufi hanyar barin gidan,sanda ya kai ƙofar fita yana ƙoƙarin sa kai cikin soron gidan,daga bayansa ya jiyo wani sanyayyan murya yana tambayarsa "Aap kahan jaa rahe hain Aslam? (Ina za kaje Aslam?)" Cak ya tsaya a gurin yana fesar da wani iskar ɓacin rai,da ƙarfin gaske ya runtse idanuwansa yana matse forehead ɗinsa ƙasa² yace "why now Mommie?" Kyakykyawar matar da take mugun kama da Afnan,tana daga tsaye bakin ƙofar ɗakin riƙe da labule har lokacin,ganin bai juyo ba cikin nuna alamun ɓacin rai tace "kya koi pareshaani hai,aur kya aap kisika intezaar kar rahe hain? (Do u have a problem,or are u waiting for someone?)" A hankali Aslam dake waiwayowa ya kalleta ya girgiza kai,fuskarsa a ɗaure,Mommie ta masa wani kallo kafin ta saki labulen tana faɗin "idan ka ga dama ka zo,in kuma baka ganshi ba kana iya tafiya" not only Aslam ya bita da kallo,hatta Nani sakin baki tayi tana kallon Mommie da ta shige ta barsu tsaye cirko²,Aslam ya kalli Nani fuskarsa kamar mai shirin kuka yace "yeh kya hai Nani? (What is this Nani?)" A hankali Nani ta lumshe masa idanu alamun kada ya damu,tana nuna masa hanyar fita tace "jeka abunka,zan yi magana da ita yanzun" Aslam dake kallonta yace "amma Nani kina ji cewa tayi naje fa" cikin jin haushi Nani ta hararesa tace "tou kuma ni na ce ka tafi,ko dai ban isa na sa kayi abu ba ni ɗin?" Yanda tayi fuskar faɗa tana kyafta idanu yasa shi sakin murmushi,a hankali yana satar kallon ɗakin da Mommie take yace "sorry Nani bance haka ba,but ki bari naje naji me za ta ce" Nani ta ƙara sakar masa harara tace "yo ba sai kayi ta zuwan ba,kaima da kanka ka sani cewa za tayi kada ka ɗauki ko wane irin mataki akan maganar" Aslam dake satar kallon ƙofar ɗakin ya taɓe baki,sanda yayi ƙasa da muryarsa yace "tou kuma idan tace ni sai na rabu da shi? Ai wallahi sai na sa yaron nan ya gane kuskurensa" da sauri Nani ta washe baki tace "tou yi maza kaje kaji abunda damo sarkin haƙurin za tace maka,kazo maza² kaje ka matsa yaron ya faɗa maka dalilin da yasa shi kiran Afnan Ƴar mace!" Sanda ya gyaɗa mata kai then ya wuce ɗakin,a ciki² yayi sallama ya ɗaga labulen ya shiga,Mommie dake tsaye ta goye hannuwanta biyu a baya,ta sauke numfashi tana kallonsa tace "Aslam neman faɗa za kaje kou? Me yasa kai a rayuwarka baka san ayi abu ya wuce ba sai ka dawo da shi ba-ya? Tunda abu ya kai haka har mai gari yana cewa zai tashe mu,idan ya koremu daga garin nan ina kake tunanin za muje? Kana ganin ina da wani guri da zan ɗaukeku muje ne? Cikin ƙasar da ba ni da dangi ko ɗaya kake so muyi ta gararin neman inda mahaifinku yake da danginsa suke? Tsayin shekaru 15 muke fafutukar neman inda asalinku yake,yau shi ne kake son zuwa ka ɗauko rigimar da zaija mana tozarci? Haba Aslam! Me yasa kai da kake babba,maimakon ka fahimtar da ƴar uwarka yanda ake zaman duniya da haƙuri akan al'amuran rayuwa,za ka yi ƙoƙarin ɗorata kan tafarkin da zai ja mana ƙasƙanci a gurin mutanen da basu kai su ci zarafinmu ba?" Wani irin sanyi jikin Aslam ya yi lokaci ɗaya,hawaye suna sauka fuskarta ta gyaɗa kai tace "shi kenan Aslam,idan so kake mu wulaƙanta,duk duniya ta san mu asalin su waye,maza jeka ka nemi faɗan da zai ja a koremu.. Kaje ka ɗauki shawaran kakarku ka ji?" Jikinsa a sanyaye ya sauke kansa ƙasa a hankali,he feel ashamed a gaban Mommie,he can see how angry she's,da wani cool voice kamar ba shi ba ya ɗago kai zai magana,sai ganin Nani suka yi ta shigo ɗakin kamar wanda aka cillota,fuskarta ɗaure ta kama waistband ta riƙe tana jijjiga jiki da kallonsu one after the other sai dai bata ce komai ba,Aslam ya kalleta ya kalli Mommie gaba ɗaya yaji ya kasa magana a tsakaninsu,ya san yanzun yana cewa wani abu al'amarin zai dagule,sanda yaga irin kallon da Mommie take masa,da sauri ya juya ya bar ɗakin,sanda ya fito bai tsaya cikin gidan ba,direct ya nufi inda abokansa suke,tun daga nesa suke kallonsa da mamakin yanda akayi ya dawo cikin sauri haka,sanda ya ƙaraso ya kalli wanda ya masa magana ɗazun fuskarsa babu annuri yace "Baban'nan ina kake tunanin zan samu Alvin?" Wani dariya ɗaya matashin yayi,Aslam da Baban'nan suka juya suna kallonsa da mamakin abunda yake yiwa dariya,sanda yayi mai isarsa ya miƙe tsaye yace "sorry dudes! Just follow me,na san inda za mu rutsa shi,but before then me ya haɗaku?" Cikin ƙuluwa Aslam yace "dalla idan za ka wuce muje to,idan kuma kana jira sai na faɗa maka abunda ya faru ka barshi kawai i don't want ur help,i can find out" yana faɗan haka ya juya da sauri zai bar gurin,Baban'nan yayi saurin riƙosa yana faɗin "just relax dude,me ya haɗaku kake neman sa?" Hancinsa yaja yana kallon Baban'nan yace "i just want to met with him,ya raina min wayo,yau dole na koya masa hankali" dariya sosai na ɗazun ya sake fashewa da shi,cikin ƙuluwa Aslam yana masa wani kallo yace "stop laughing at me,ka san ba na son dariya haka kawai" Baban'nan dake kallonsu su duka biyu cikin sauri yace "haba Sultan mene ne haka kake yi?" Da sauri Sultan yace "sorry dude! Let's go" yayi saurin wucewa gaba suka bisa a baya,suna tafiya a hanya Sultan ya kalli Aslam yace "Dude! Wai me ya faru ne?" Cikin ɓacin rai Aslam ya musu bayanin komai,Sultan yana jinjina kai yace "kan uban can! Kace kawai muna ganinsa mu ragargaje ɗan banza,dama kwaya ta gama rarake shege!" Baban'nan dake gyaɗa kai yace "ka faɗa ma wani ya ji" Aslam dai bai ƙara magana ba sai jinjina irin hukuncin da zai masa yake. Sanda suka zagaya duk inda suka san Alvin yana zama cikin garin basu samu ko mai kama da shi ba,Sultan ya kalli Aslam yace "idan har kere na yawo,zabo na yawo dole ne mu jame (haɗu),ku zo mu sa shi kawai,next time!" Daga haka suka juya suka bar gurin. Yanda hadari yake ƙugi tun yamma har gabannin maghreb yasa dattijuwar mai kimanin shekaru 63 dake zarya daga ɗaki zuwa maidaidaicin kitchen wanda yake tsakar gida,ɗaga kai ta kalli sama for the countless time,kafin ta girgiza kai ta sake koma ɗaki,not too long ta fito hannunta riƙe da mayafi ta nufi hanyar fita,tana zura ƙafarta soro suka yi ido huɗu da kyakykyawar yarinyar wanda baza ta wuce 15yrs ba,da sauri dattijuwar ta koma baya ta rafka salati "la'ilaha illallahu muhammadur'rasulullahi sallalahu ailaihi wasallama.. *NAINA!* Me zan gani? Tun ɗazu nake jiranki ashe kina nan maƙale a soro,me kike jira baki kawo min niƙan ba?" In'ina Naina ta fara tana zaro madaidaitan idanuwanta tace "Yaa.. Yaawo! Shi ne ya zubar min da.. Mmm.. Mmmm niƙan" da sauri Yaawo dake sauraren Naina ta dafe ƙirji tace "kika ce me?" Naina dake ƙiƙƙifta idanu kamar za tayi kuka tace "wallahi Yaawo bige ni yayi niƙan ya zube.. Ba da sani na zubar ba" Yaawo tana kaɗa kai tace "ai shi kenan sai ki zo ki wuce ki nemi guri mu rungumi ƙaddara" tana faɗa ta juya cikin gida tana sauke mayafin daga kanta,a baya Naina ta biyota tana share hawaye,da yar siririyar muryarta tace "Yaawo kiyi haƙuri." Yaawo dake shiga ɗaki tace "haƙuri ai ya zama dole.. Idan ban haƙura ba zan kama ki na doke ki ne? Ko kuwa garin da kika ɓarar zai dawo?" Jiki a sanyaye Naina tace "Allah Yaawo ba da niyya na zubar ba,ki tambaya ma kiji shi ne ya bige min niƙan" Yaawo dake fitowarta ɗaki ta wuce kitchen tana kiciniyar sauke tukunyarta daga wuta,tace "ke kika sani dai kuma" kamar Naina za ta yi kuka take kallon Yaawo tace "ni wallahi ban zubar da niƙan da sani ba,na faɗa miki fa buge min yayi" a fusace Yaawo ta juyo tace "uban waye zai ɓarar maki,idan ba tsokana ko neman faɗa kika tsaya ba?" Kuka sosai Naina ta fashe da shi tace "na rantse da Allah ni ban tsaya ko ina ba,Yaya Aslam ne fa ya ɓarar min niƙan,kuma ƙofar gidansu a cike da mutane ni ban san me ake yi ba" saurin kallonta Yaawo tayi tace "kika ce mutane a ƙofar gidansu su?" Da sauri Naina ta gyaga kai tace "ehhh! Kuma na ji Nani sai faɗa take da zan wuce" da sauri Yaawo ta wuce ta koma ɗaki,mayafinta a hannu ta wuce ta nufi ƙofar fita gidan,da gudu Naina ta biyo ta tana cewa "Yaawo ki tsayani" Yaawo bata saurareta ba ta yi waje,a baya ta biyota sanda ta ja ƙofa ta rufe ta ƙarasa ƙofar gidan,tsakanin na su da na su Aslam gida ɗaya,ta shiga da sallama tana rarraba idanu,sanda ta ja ta tsaya bakin ƙofa jin bayanin da Nani take yiwa Yaawo kan matsalar da aka samu,Yaawo tana jinjina kai tace "anya! Kuma Afnan ɗin ce ta maresa?" Nani ta watsa hannuwa tace "yo wa ya sani musu ne" jin haka yasa da sauri Naina dake tsaye ta juya za ta fice tana turo baki,hurriedly Yaawo data kula da ita ta ƙwalo mata kira tace "dawo maza²" Nani dai ta saki baki tana kallonsu bata ce komai ba,Naina ta ƙarasa gaban Yaawo tace "ga ni" Yaawo tana binta da kallon tuhuma tace "ni na san dama ba banza ba kika ɓarar min da niƙa" Afnan dake tsaye tana jin haka ta kyalkyale da dariya,lokaci ɗaya Yaawo da Nani suka juya suna kallonta,Mommie da tun shigowar Yaawo gidan bayan sun gaisa,daga haka bata ƙara magana ba,tana jifan Afnan da wani kallo fuskarta babu wasa tace "ke lafiyarki lau kika sa mutane gaba kina musu dariya?" Da sauri Afnan ta haɗiye dariyarra tace "i'm sorry" ta sunkuyar da kai,Yaawo ta mayar da kallonta kan Naina da ta haɗe rai tayi kicin²,tace "za ki faɗa min gaskiya ko sai na zane ki a gurin nan?" Da sauri Naina ta matsa tana turo baki tace "toh! Yaawo ba shi ne yake zaginmu ba,ni kuma na maresa" salati duka suka ɗauka banda Afnan da Naina da suka kwashe da dariya,da gudu Yaawo ta rarumo ƙaramin kujera ta bisu,a guje sanda suka shige ɗaki suka ƙara fashewa da dariya,Nani dake tsaye tana tafa hannuwa tace "kiji ƴan kan uban yara,ashe haɗa kai suka yi suka ɗauko mana magana" Yaawo da ta tsaya bakin ƙofar dakin seeing that sun yo locking ta ciki tace "za ku ci ƙaniyarku idan kuka fito ai,ba haƙura nayi ba" Naina ta ɗaga murya tana ɓaɓɓaka dariya tace "wallahi baza mu fito ba sai kin tafi" suka sake fashewa da dariya,Mommie dake zaune tana aikin abincin dare tayi murmushi haɗe da girgiza kai,idan da sabo ya ci su saba da halin Afnan da Junainah na ɗaukar magana,Yaawo ta juya ta koma kusa da Nani ta tsaya tace "ai ko me ya faru,dama na san wannan mai farin idanun ce shaiɗaniyar da ta ɓallo bala'in.. Ni dai duk ba ma wannan ba,da za kiji ta tawa kinga da sai ince mu rufa kanmu yanzu² muje gidan mai gari mu ba da haƙuri kafin al'amarin ya ƙarra lalacewa ko kuwa?" Nani dai bata ce komai ba sai sauraren Yaawo take dake sababi,Afnan suna daga cikin ɗaki sai sauraren mitar Yaawo suke suna ɓaɓɓaka dariya,Mommie dake kitchen na taya su murmusawa,Yaawo tayi ta gaji sanda taga Nani ba ta da niyyar tankata kan batun da tayi na zuwansu gidan mai gari ta juya ta bar gidan,Nani kuwa dama ta gama ƙudurcewa a ranta babu inda za taje wani ba da haƙuri,ai shi ya janyo suka maresa,da bai tsokanesu ba suma baza su kulasa ba. At that same day,gabannin sallar isha'a lokacin hadari ya gama haɗuwa,garin duk ya yi baƙi,banda flashlight da ake yi gami da thunder storms da ya cika garin ba ka jin komai,kiran sallah da akayi yasa Aslam fitowa daga gida zuwa masjeed though he know idan yanayi yayi irin haka sallah a gida ya fi but really hate yin sallah alone ba'a jam'i ba,tafiya yake a nutse but har lokacin abunda ya faru ɗazun bai bar damunsa ba,maganganun suna masa amsa kuwwa a kunnuwa da ciwo a rai,ana idar da sallah ya fito masjeed,tsaye ya tarar da su Baban'nan a bakin masallacin,da alamun suma shi suke jira,ya ƙarasa yana musu kallon tuhuma,kafin yayi magana Sultan yace "kai muke jira dama,yanzun nan Alvin ya wuce ya yi gida" da sauri Aslam yana kallonsa yace "chaliye.. (let's go)" Suka nufi line gidan mai gari,Sultan da Baban'nan suna ci gaba da tattauna yanda za suma Alvin shegen duka,shi dai Aslam bai ce musu komai ba tafiya kawai yake,underneath yake tunanin maganganun Mommie na ɗazun,sai dai har yanzun bai jin zai iya haƙura ya rabu da Alvin ba tare da ya ɗauki matakin da nan gaba ko cewa aka yi ya kalli AFNAN zai iya ɗaga idanunsa ya sauke a kanta ba,dai² suna karyo kwanar line,suka yi kaciɓis mugun gamo,Alvin yana tafe yana ƴan waƙe² irin na riƙaƙƙun ƴan shaye²,Sultan ya fara matsawa ya tsaya ta bayansa,sai Baban'nan da ya koma gefensa,Aslam dake tsaye gabansa ya fesar da hucin ɓacin rai,yana kallon Alvin with his oily eyes yace "mene ne ya haɗa ka da ƙanwata?" Alvin yana kallon Aslam yace "ban gane me kake faɗa ba gaye" backhead ɗin da Sultan ya bugo cikin zafin nama yace "tambayarka ake dan uwarka,mene ne ya haɗa ka da Afnan?" A fusace Alvin yace "ita wannan Ƴar macen kuke nufi wai?" Kafin ya ƙarasa faɗa Aslam ya kai masa punch ya same shi a baki,nan da nan bakinsa ya fara jini,kafin ya sake magana Sultan da Baban'nan sun rufesa da duka,irin karin maganar nan da bahaushe yake cewa sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi,it was there suka masa lilis,sai ihu yake yana ba su haƙuri,sanda suka tara masa gajiya,Aslam ya sunkuya a gaban Alvin,yana zazzaro masa idanunsa with lots of warning yayi making snapped a dai² fuskarsa yace "idan ka cika ɗan iska,gobe ka sake tareta a hanya kaga yanda idan muka haɗu zan saɓa maka kamannin fuskarka.." Sultan dake tsaye bayan Alvin ya kai masa hauri da ƙarfi yace "daƙiƙin banza jaki" Aslam ya sauke numfashi ya miƙe tsaye yace "let's go guys.." Daga haka suka juya suka bar Alvin kife a ƙasa yana numfarfashi. Sanda suke rabuwa da su Baban'nan,tun a hanya iska mai ƙarfi ya fara tasowa,Aslam dake tafiya shi kaɗai hannayensa zube cikin aljihun wandonsa ya ɗaga kai yana kallon yanda ake walƙiya mai tsanani,haskenta mai kashe idanu da rugugin tsawa mai ƙarfin gaske,a ransa yake karanto addu'o'in da Annabi (S.A.W) ya koyar da mu a lokacin da iska ta taso dana tsawa,sanda ya iso ƙofar gida,yana ƙoƙarin shiga soron gidan,da ƙarfi ya dunga jiyo footsteps a bayansa kamar ana gudu,da farko bai ɗauki al'amarin da wani muhimmanci ba,sanda yaji kamar shi ake bi,so he thought ko Alvin ne ma,tunda ya san ba ya barin ramuwar gayya akan ko wane ne a garin,yana cikin tunanin irin mummunan dukan da zai naɗa masa,yaji an dafa shouldersa,da wani irin sauri ya waiwaya,lokaci ɗaya ya zaro idanuwansa a tsorace sanda yayi baya yace "tum?"

    *This book is not for free,it's #300 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman-Access bank. Then u show ur evidence of payment via my whatsapp digit 08165726609 to be added in the paid group. Ƴan Niger za ku iya tuntuɓar wannan number +22770766074.*

     

#Follow
#Vote
#Comment
#Share fisabilillah!
#Asli Smasher.

KALLO YA KOMA SAMA!Where stories live. Discover now