*BUSHRA*
_By_
_REAL ESHAA_*PAGE 5&6*🖊
________________📖A 'bangaren Ya'u suna isa gida yayi parking motar,cikin sauri ya fito ya bu'de wa Hajiya 'kofar motan,ganin bata fito ba yasa shi fa'din"Bismillah Hajiya ta mun 'karaso".Ta'be baki Hajiya tayi tare da zabga masa harara hannun zanin ta ta since ta ciro goro seda ta 'balla kafin ta kalle sa tare da fa'din",yau kuma wani sabon salo ka keji dashi?,ko kuma da kai kake bu'de min motar??.Ta fa'da tana binsa da mugun kallo,dan Allah ni matsamin in wuce kawani tare min hanya gulmamme kawai.Sum-sum Ya'u ya matsa mata ta wuce, Aran shi yace"kai Hajiya ita de ba ayi mata gwanin ta komai kayi seta gwasaleka. Anma duk abinda za tayi ina nan tare da ita harse ha'kata ta cimma ruwa wannan al'kawari nane, Murmushi ya sake kafin shima yashiga gidan....
Koda yashiga compound 'din gani yayi Hajiya ta wuce shashen ta,Ta'be baki yayi aran sa yace"ya defi.Direct sashen sa ya nufa batare da yayi salama ba ya kutsa kan sa cikin falon.Zaune ya samu matar shi tana feeding 'din 'yar sa 'karama wacce baza ta wuce wata uku ba. "Kallon sa tayi da murmushi afuskar ta tace"Sannu da zuwa Dadyn Azeemah,Murt'uke fuska yayi kamar beji ba ya nemi waje ya zauna.Da sauri Rabi ta tashi ta dawo kusa dashi ta zauna tana kallon sa tace"Lafiya kuwa Dadyn Azeemah??,"me yafaru naga kamar kana cikin ya nayin damuwa?.Ta gumi tayi cikin jimami tace"ko su Yaya sun samu nasara ne akan abinda suka je nema??."Nan ma shiru Ya'u yayi bece komai ba be kuma kalli inda take ba. Ido Rabi ta zuba masa tana kallon sa dan wataran halinsa na mugun 'bata mata rai dan 'karamin tsaki taja Iya bakin ta yanda baze jiba ta cigaba da feeding 'din Azeemah...
Ya 'dauki kusan ki manin minti shida kafin ya numfasa batare daya kalle ta ba yace" wannan shi ake kira ga 'koshi ga kwanan yunwa... Jin ya tanka ta yasa tayi saurin ajiye Azeemah agefen ta ta matso kusa dashi tace"me yafaru Allah yasa ba abinda nake zargi ba ne??. Ajiyan zuciya ya sau'ke yace"Basu samu abinda su kaje nema ba tunda kinsan dama ba me yuwa bane.Ajiyar zuciya me nauyi ta sau'ke tace"Toh kuma meye abin damuwa?,Batare da ya tanka mata ba ya cigaba dacewa sede ahanyar su ta dawowa gida sun tsinci jaririya!!...
A zabure Rabi ta mi'ke tare da fa'din"Innalillahi wa'inna ilahi raji'un hasbunallahu wani'imal wakin".Harara Ya'u ya watsa mata cike da masifa yace"lafiya kike yiwa mutane irin wannan salati kamar kinga wani abin tsoro ko dodo!??., Ya fa'da yana bin ta da mugun kallo. Zama tayi tace"toh ba dole kaji nayi salati ba wannan fa ba 'karamin al'amari bane,Anma wannan jaririyar akwai la'ananni ya yo inba shegiya ba tarasa inda zata zo se acikin zuri'ar mu Ina wallahi baze yiba duk yanda akayi wannan Jaririyar ba mutum bace anma koma menene toh wallahi se tabar gidan dan yanda ya 'dauko to haka ze mai da ita ta 'karashe maganan kamar za tayi kuka...
"Dafe kai Ya'u yayi cike da takaici yace" ni baki 'daya ma kaina ya kulle bansan yanda zanyi da ita ba,Sa'ar mu 'daya ma dan Hajiya ta nuna batason Jaririyar kuma nasan Yaya najin maganar ta to ina ganin wannan itace mafitan daza mu samu in kuma wannan hanyar be yiba to akwai wata hanyar, da zamu samu damar korar ta cikin sau'ki....
Murmushi Rabi tayi tace" 'kwarai kuwa dan inde ta bashi umarni baya 'ketare wa.Kai Ya'u ya gya'da batare da yace"komai ba.Da sauri Ya'u ya bu'de idanun sa dake lumshe yace"me kika ce, Ba tare da damuwar komai ba Rabi tace"Cewa nayi kode sayo ta yayi agidan marayu?,"wani shegen kallo ya mata yace"Ki iya bakin ki inba haka ba wallahi zanyi miki rashin mutunci yana gama fa'din haka ya mi'ke ya shiga bedroom.Tsaki Rabi tayi face"kaji da shi jarabebbe.*********
Hira suke me cike da farin ciki da jin da'di kallo 'daya zaka musu kasan suna jin da'din yana yin da suke ciki. Jin kamar 'kara ya sanya su mi'ke wa da sauri sukayi bedroom 'din,Cike da damuwa ko wanne su ke tambayan me yasame ta??,Alhaji Aliyu ne yayi nasaran 'daukar ta yana jijjigita a kafa'dar sa,waya ta'ba minke Baby na??,ya fa'da yana sa 'bata aka fa'dar sa ahaka bacci ya 'dauketa.Murmushi Hajiya Asma'u tayi tace"Ashe de ka Iya reno Miji na?. Dariya Alhaji Aliyu yayi yace" jeki kwantar da ita kizo muyi magana,ba musu ta kar 'beta ta kwantar da ita akan gadon sannan ta dawo ta zauna kusa dashi dan jin me zece...
Bayan ta kwantar da ita ta dawo kusa da ita ta zauna,tare da fa'din"gani mijina. Kallon ta yayi yace" daman kan maganan sunane wani suna kike ganin yakamata musa mata?? ,Shuru tayi na wasu mintuna tace"ni agani na mu sanya mata sunan Hajiya,Shiru yayi na wasu mintuna se kuma ya girgiza kai yace"a'a ayanda Hajiya take fushi akan maganan baza musa mata sunan ta ba, mu nemi wani sunan kawai. Shiru tayi tana nazari,"Murmushi yayi yace"to ko mu sanya mata sunan kine"??. Dariya tayi tace"aikuwa da naji da'di anma sede yanzu akwai sunan da nake so in saka mata tunda ba musa Hajiya ba. Kallon ta yayi yace" wani suna kenan kike son samata?? Ya tambaya yana kafeta da kyawawan idanunsa....
Batare data bashi amsar tambayar ba tace"Wannan kallon fa???.Murmushi yayi yace" dan na kalli fuskar kyakykyawar matata nayi lefi?? Shima yama yar mata da sigan data yi masa tambayar,"Dariya tayi tace" a'a ba kayi lefi ba anma yanzu de mu koma kan maganan sunan Baby, "Ok ina sauraran ki dan nasan matata gwanace wajen iya za'be. Dariya tayi tace"godiya nake mijina, *BUSHRA* shine sunan dana za'ba mata ina fatan zeyi maka??? ,Masha Allah suna me da'di gaskiya kin Iya za'be kuma kin za'bo sunan daya dace ya fa'da yana sakar mata da lallausan Murmushi.Sosai Hajiya Asma'u taji da'din yabon da ya mata tafin hannun sa ta ri'ke acikin nata tace" ina fatan mukasnce da ita har 'karshen rayuwar mu.Nima haka ya fa'da yana sumbatar hannun ta...
Gobe insha Allah zansa aka wo min ragon suna da sauran abubuwa bu'kata sauran kuma seki yimin list nasu dan kin fini sanin su,?."Insha Allah ta amsa masa,haka suka cigaba da tsare tsaren yanda zasuyi shagalin sunan Bushra da kuma sauran abubuwa har dare yatsala sosai basu sani ba suna ta shir shirya abubuwan da zasu gudanar..._Gamai bu'katar compled Document 'din KI YADDA DANI 400 hundred ne se su turo da katin wannan number 09068403802 ko kuma ta account 'dina Abdullahi keystone bank 6030406548..._
*Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah ka gafar ta masa zunubansa ya Allah ka kai haske kabarin sa ya Allah kajikan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya....*
*ESHAA CE*🤙🏻
