*BUSHRA*
_By_
_REAL ESHAA__Am Sorry My Fan's naga sa'kon ku jiya biki muke shiyasa ku ka jini shiru nagode da kulawar ku..._
*Page 11&12*🖊
_______________📖Driving yake anma baki 'daya ba shida walwala,Ha'ki'ka da yana da ikon can zawa Baby 'kaddarar ta to da ya canza mata!,Da ace yana da ikon da ze mayar da ita 'Yar asali kuma 'yar dangi daya mayar da ita,da ace ku'di ko kadara ze iya canza wa Baby Bushra 'kaddaran ta tabbas da ze 'karar da duka dukiyar sa dan ta sama 'yantacciya.Da akwai wata hanya da zebi yaga Bushra ta dawo 'yar sa wacce ta fito daga tsatson sa da yabi domin guje mata gori da cin fuska da zata fuskanta anan gaba.Ya zama wa jibi ya zage dantse ya kuma jajirce wajen ganin yasada ta da iyayen ta da kuma dangin ta,Kai ya dafe cikin tsananin damuwa yace"Shin ta ina zan fara wannan aikin bani da wata sheda ko maka ma wanda ze sa in kaita ga iyayen ta,Wata zuciyar tace"se ka 'dauki 'kaddara a yanda tazo muku domin 'kaddara ya riga fata,tabbas yana tausayawa rayuwar Bushra yana tausayin rannan da akace baya numfashi a doron 'kasa!! yasan zata shiga 'kuncin da gararin rayuwa duk da baya fatan hakan ya kasance agare su.Ya zurfafa acikin duniyar tunanin da yake wanda yasa shi mance wa da tu'ki yake....Girgizasa Hajiya Asma'u tayi cikin ki'dima da tsananin tashin hankali sakamakon wata 'katuwar motar 'dangote da tayo kan su.Cikin tashin hankali yafara 'ko'karin kaucewa dan sam be lura da motar dake gaban su ba."Duk wata addu'ar da tazo bakin su shi sukeyi, cikin ikon Allah ya samu nasaran kauce wa sede, motar 'dangoten tagogi bayan tasu,Ba abinda suke furta face Alhamdulillah tunda cikin su babu wanda ya samu matsala....
Nan take mutane suka yo Kansu ana fatan babu abinda yasa mesu,Wasu daga cikin mutanen wajen ke fa'din lalle bayin Allah kuna tare da addu'ar iyaye badan addu'ar iyaye na bibiyar Kuba sede ayi labarin wasu anma ba kuba. Sauran jama'ar wajen kam fa'da suke kamar zasu ari baki kan yana ganin motar anma be kauce ba se kace ya sayi hanyar....Ha'kuri ya basu sannan yaja motar suka tafi,babu Wanda ke magana acikin su kowa da kalan tunanin da yake aransa,Jin shirun yayi yawa ne ba maganan Baby Bushra yasa Hajiya Asma'u le'kawa baya ko lafiya,Ba 'karamin raza tayi ba ganin Baby Bushra kwance rabin jikin ta yana kan sit 'din motar rabi kuma yana tsakanin kujeran cikin tashin hankali tace"Innalillahi wa'inna ilahi raji'un,ya Allah ka daka jarabce mu da abinda baza mu iyaba!Cikin kuka ta 'karashe maganan tana 'ko'karin 'daga Bushra.Alhaji Aliyu na jin salatin da Hajiya Asma'u yayi saurin parking agefen hanya zuciyar sa na bugawa da 'karfi....A sukwane Hajiya Asma'u ta bu'de motar ta fita tare da shiga bayan,'dago kan Bushra da babu alamar numfashi atare da ita,tayi ta'daura acinyar ta, hawaye na fita daga Idanun ta tace"Dan Allah Baby ki bu'de idon ki babu abinda zesa meki!!.'Daya side 'din Alhaji Aliyu ya shiga suka sa Bushra atsakiya..
Ruwan dake hannun sa ya yeyyefa mata tare da tofa mata addu'o'i.Dogon numfashi Bushra taja tare da 'kan'kame Hajiya Asma'u cikin kuka tace"Mam'ma tsoro nakeji dan Allah karki bari motan ya bugemu!"...Rungume ta Hajiya Asma'u tayi tana wa Allah godiya da babu abinda yasamu Bushra."Kiyi Shiru Baby Insha Allah babu abinda zesa meki kin ji in kinga ai babu motar anan kuma idan kinga abinda ya tsorata ki kidinga addu'a".Kai Bushra ta gya'da tana sau'ke ajiyar zuciya...
Kanta Alhaji Aliyu ya shafa yace" Sannu Baby, nina ja muku kiyafe min kinji kiyafewa Abba ki baze sake ba!.kallon sa tayi tana girgiza kai tace" Abba ba kayi min komai ba ai tsautsayi ne ko,ta mayar ga kallon kan Hajiya Asma'u tace"haka ne ko Mam'ma??.Kai Hajiya Asma'u ta gya'da batare da tace"komai ba sede tana nazarin maganan Bushra aran ta.Shafa kanta Alhaji Aliyu yayi yace"Allah ya Albarkan ci rayuwar ki"Ameen suka amsa".Fita yayi ya koma wajen zaman drive,Hajiya Asma'u kuma ta zauna abaya rungume da Bushra, Shiru motar tayi suna tafiya babu Wanda ya sake magana acikin su ko wanne da kalar tunanin da yake aran sa.
Suna Isa gida yayi parking ya fito,Hannu Baby Bushra ya ri'ke bayan ta fito,suka shiga falon Hajiya Asma'u na biye dasu.Zama yayi akan kujeran wayar sa ya ciro bakanike ya kira bayan ya 'daga yace"kazo gida ka 'dauki motata ya samu matsala,Cike da ladabi bakaniken ya amsa"Sannan Alhaji Aliyu yakashe wayar tare da mayar da kallon sa kan Hajiya Asma'u data tsaresa da ido.Murmushi ya sakar mata tare da fa'din"ya akayi ne Ummu Bushra irin wannan kallo haka??...Numfasa wa Asma'u tayi tace" meyesa ka kesawa kanka damuwa ne Abban Bushra??,Kana sane da cewa bawa baya ta'ba kaucewa 'kaddaran sa,Haka Allah ya tsarawa Baby Bushra nata 'kaddaran to meyesa baza kasawa ranka salama ba?,Menene abin tada hankali akan abinda Ubangiji ya tsara?,Meyesa ba zamu kar'bi 'kaddara ayanda tazo mana ba?.Karfa ka manta muma iyayen ta kuma kaf duniya bata da iyayen da suka wuce mu, Sannan Insha Allah zamu cigaba da kasancewa amatsayin iyayen ta na Har abada babu wanda zesan wannan sirrin,dan haka ka cirewa ranka damuwa akan abinda Ya'u yake fa'da ko kuma sauran 'yan uwa daman dole kaji,ka 'ki ji,ka gani ka kuma 'ki gani nasani abinda ake cewa Bushra da ciwo anma dole mujure,Insha Allah komai ze wuce tamkar ba ayiba,
Muddin fa baka cire wannan damuwar aran kaba bawai kai ka'dai zaka cutu ba hadda mu domin duk abinda ya shafe ka ya shafe mu,Ina me ro'kon ka akaro na 'karshe dan Allah ka cire damuwa aran ka.Kalli 'dazun badan Allah yatsare ba me kake zaton ze faru?...
Jikinsa ne yayi sanyi tabbas maganan ta gaskiya ne,Yana kallon ta yace"Ha'ki'ka zancen ki gaskiya ne kuma Insha Allah daga yau na dena sa damuwa a raina zanyi 'ko'karin ganin na kawar da duk wani Abu da ze sani acikin damuwa ko kuma tunani.Sannan zan cigaba da yiwa Allah godiya daya bani nitsatsiyar mace me addani da kuma kamala wacce aduk sanda nashiga damuwa seta gusar min dashi,Samun mace irin ki a wannan zamanin se antona,Mata irin ki sunyi 'karanci acikin al'ummah ina sake yiwa Ubangiji godiya daya mallaka min ke ina alfahari dake a rayuwa...Murmushi tayi cike da jin da'din kalaman sa se taji duk wani damuwar ta ya gushe,tana da ya 'kinin koda bayan ranta ne irin shedar da zeyi mata kenan.Mi'kewa tayi ta shiga kitchen dan ha'da musu abinci,'kwanciya yayi yana jin nutsuwa na ratsa duk wani sassan jikin sa....********
Azeemah ki bu'de 'kofar dan Allah kiyi ha'kuri bazan sake miki fa'da akan 'kawar ki ba nayi al'kawari kinji 'Yar Dadyn ta maza bu'de min 'kofa,Ki naso in kai ki wajen wasa da gidan zu da Shoprite ko cewar Ya'u cikin lallashi???.Banza Azeemah tayi ta dasu ba irin magiya da lallashi da lallami wanda Rabi da Ya'u ba suyi wa Azeemah ba anma tayi banza dasu...Ba 'karamin tashin hankali Ya'u da Rabi suka shiga ba ganin duk da 'dewar su awajen Azeemah ba tayi magana ba kuma basu ji motsin ta ba tsoron su 'daya kada ta cutar da kanta.Tunanin haka yasa Rabi fita da gudu ta nufi sashen Hajiya.Tana haki tace".Dan Allah Hajiya kizo ga Azeemah can tun 'dazu ta shiga 'daki ta rufe 'kofa kuma munyi-munyi ta 'bude ta'ki ta'karashe maganan kamar zatayi kuka!!.Harara Hajiya ta zabga mata Afusace tace" toh ina ruwa na da wani rufe 'kofar ta??,Ko kuma nice nasa kuyi mata abinda zata rufe 'kofa??Bade ku baku da hankali ba,In ba Iya shege da samun waje ba duka duka nawa Azeemah take dan anyi mata Abu zata shiga 'daki ta rufe??.Saboda rashin sanin ciwon kai yanzu kuma kin kwaso 'kafa kamar lauje wai kin kawo 'kara ba kunya bare tsoron Allah shasha!!...
Ba'kin cike da takaici ne ya to karewa Rabi ma'koshi jin 'diban albarka da ba'ka'ken maganan da Hajiya ke ya 'ba mata duk wannan be ishe ta ba seta ha'da da zagin halittar ta.Anma da ke nema ta keyi se tayi 'kasa da murya tace"Dan Allah Hajiya kiyi ha'kuri kije kar ta cutar da kan ta.Da 'kyar Hajiya ta yadda za taje har ta isa sashen mita take....Har lokacin da Hajiya ta isa sashen Ya'u na faman lallashin Azeemah anma shiru.Duk surutu irin na Hajiya da lallashi babu irin wanda ba tayiwa Azeemah ba anma tayi banza dasu,zuwa lokacin hankalin su yayi masifar tashi sun fara tunanin ko wani abune ya sameta....
Dabara ce ta fa'dowa Ya'u,cikin sauri ya 'dauko wayar sa tare da danna kiran lambar Alhaji Aliyu....Alhaji Aliyu na hira da Baby tana bashi labari yana ta dariya 'kira ya shigo wayar sa koda yaga mekiran 'kin 'dagawa yayi ya mai da hankalin sa kan Bushra.Seda Ya'u ya kira kusan sau goma kafin Alhaji Aliyu ya 'daga.Ya'u na jin yayi picking yayi saurin cewa dan Allah Yaya kayi ha'kuri ka bawa 'yar wajen ka waya Wallahi Azeemah ce ta tashi hankalin mu!!.Wacece 'yar waje na?Cewar Alhaji Aliyu. Takaici ne ya to karewa Ya'u ma 'koshi jin tambayar da Alhaji Aliyu ya masa,Da 'kyar Ya'u ya danne zuciyar sa yace" 'Kawar Azeemah fa nake nufi Yaya....Ta'be baki Alhaji Aliyu yayi yace"Gaskiya bangane wacce kake nufi ba da alama kayi mistake number ne ya 'karashe maganan da Murmushi a fuskar sa.Ya'u ji yayi Kamar zuciyar sa ze fashe saboda takaici wai yau shize kira sunan wannan Aljanar yarinyar.A ta'kaice yace"Bushra nake nufi...
Allah sarki Meyafaru da Azeemah?,toh cewar Alhaji Aliyu.Kamar jira Ya'u yake ya shiga fa'da masa abinda yafaru sede ya 'boye masa dalilin kulle 'kofar Azeemah,Ok sa wayar a hands Free cewar Alhaji Aliyu.Ba musu Ya'u ya matsa jikin 'kofar tare da sa wayar a hand's free kamar yanda Alhaji Aliyu yace".Cike da so Abba yashiga rarrashin Azeemah tare, da fa'din" Ya'u ka tabbata gobe kasa akawo ta,"Ok Ya'u ya amsa".Azeemah najin hakan tayi murmush.Mi'kawa Bushra waya Abba yayi yace"Ga 'kawar ki kiyi mata magana,Da sauri Bushra ta kar'ba tace" 'kawata.Azeemah na jin muryan Bushra ta bu'de kofar ta fito,wayan ta kar'ba a hannun Ya'u tayi gaba abinta ta barsu atsaye batare datayi musu magana ba.'Kwafa Hajiya tayi tace"anma wannan akwai 'kanwar ifritu babu ifirancin da bata iya ba saboda tsaban iya shege babu irin maganan da ba muyi ba anma tayi mana banza,tsaki taja tafice tana mita daga Ya'u har Rabi babu wanda ya tanka mata har ta tafi.Suma Ya'u haka suka bi bayan ta zuwa falon duk haushi da tsanar Baby na sake nun kuwa a zuciyar su...A 'bangaren Alhaji Aliyu kam sosai yaji da'din yanda Azeemah ke 'kaunar Bushra.Hira Azeemah da Bushra sukayi sosai abin su cike da yarinta,Nan Azeemah take sanar mata Dady yace gobe ze kawo ta, aikuwa ba 'karamin murna baby Bushra tayi ba,suna ta hirar su har bacci ya d'aukesu suna wayan zare wayen Abba yayi daga kunne Bushra ya 'dauketa ya kaita 'daki sannan yayi mata Addu'a....._Ga mai bu'katar completed documents din KI YADDA DANI 400 hundred ne se ya tuntu'bi wannan number 09068403802 danjin yadda za abiya..._
*Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunuban sa ya Allah kaji'kan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani...*
*ESHAA CE*🤙🏻