*BUSHRA*
_By_
_REAL ESHAA_*PAGE 13&14*🖊️
_______________📖Washe gari;Da wuri aka shirya Azeemah saboda yanda ta azalzalesu da jaraba,Zare mata ido Ya'u yayi yace"babu inda zaki je sede kiyi kukan jini,Wani uban ihu Azeemah ta kurma wanda seda falon ya amsa suwan Muryan ta Zubewa tayi 'akasa tace"Wayyo nashiga Uku na lalace Abba!!Dady sunce baza su kaini wajen Bushra ba.Tsugunna wa Rabi tayi akan ta ta 'dagota tace" haba Azeeman Dadyn ta yanzu tafiya zaki yi ki barmu??,ki ha'kura da zuwa zan kai gidan zoo.Cike da sangarta Azeemah ta fashe da sabon kuka tace"Nide ba naso gidan Abba nake son zuwa",ta kaici da ba'kin ciki yasa Rabi kwa'da mata mari"Ihu Azeemah ta sanya fiye da na farko."Wannan sababi da meyayi kama ni Munari ace da sanyin safiya acika mana gida da ha yaga'ga kamar layin allura cewar Hajiya tana kallon Azeemah dake birgima a'kasa.Batare da sun bata amsa ba suka ce ina kwana Hajiya.Wani shegen kallo ta watsa masu tace"Nifa bana son iya shege da tsegumi ya ina tambayar ku,kuna wani gaishe ni se kace ance muku dan kar'ban gaisuwar Ku nazo ko kuwa baku San inda nake bane??.Ta'be baki Rabi tayi daga haka ta mi'ke ta shiga kitchen,da kallo Hajiya ta bita cike da masifa tace"Uwar ki me dattin 'dan kwali kika ta'be wa baki bani ba banza fitsararriya.Kallon ta tamayar kan Ya'u da ya zabga tagumi tace"ba tambayar ka nake ba ka wani zuba Uban ta gumi kamar wanda aka yiwa aka aikawa da sa'kon mutuwa?."Hajiya Azeemah ce wai se an kaita gidan Yaya akan munce ta ha'kura da zuwa shine take wannan kukan cewar Ya'u yana Hararan Azeemah da har yanzu take kuka.Yau naga abinda ya ishe ni be ishi Allah ba yanzu Ya'u saboda tsaban rashin ta ido shine ka ke sake maimaita ta min abinda ya faru,anma de Wallahi anyi girman kwabo tunda Har yarinya tafi ka sanin abinda ya dace, yo in ba gidan Aliko ba kana da gidan uban da zata je ya wuce nasa ne?,ta inda Hajiya ke shiga bata nan take fita ba se da tayi musu tasss kafin ta fice tare da bashi umarnin maza ya kai Azeemah...
Babu yanda suka Iya haka suka sake shirya Azeemah cikin shiga me kyau ba dan ransu yaso ba se dan jaraban Hajiya da kukan Azeemah.Madu drive Ya'u ya kira ya ba Izinin ya kaita da gudu Azeemah ta fita daga falon tana murnan zuwa ganin 'kawar ta"mota ta shiga tare da 'dagawa Ya'u da Rabi hannu.Key Madu yayi wa motar sannan yaja suka tafi.Motar na fita Ya'u ya mayar da kallon sa kan Rabi da ta zuba Uban ta gumi kamar wacce aka aikawa da sa'kon mutuwa!,Cikin 'kunan zuciya Rabi tace"Wallahi Dadyn Azeemah na tsani waccan tsinanniyar yarinyar me 'kiran aljanu!,dubi yanda duk ta birkita mana hankalin yarinya nifa ina zaton Wallahi wannan yarinyar ba mutum bace,Ka dubi yanda take abu kamar wata babba yarinya 'karama se shegen fele'ke da shiga ran tsiya,ko da ganin yanda take da shiga rai ai kasan ba abanza ...Numfasa wa Ya'u yayi yace"kede barni da la'ananniyar yarinya Rabi,Na gama yanke hukunci abinda zan mata wanda ba ze yiwa kowa da'di ba sede duk abinda zefaru yafaru anma nagama magana.Dan sena nuna mata wanene asalin Ya'u.Cikin tsoro da fargaba Rabi tace"Dadyn Azeemah mekake shirin aikata wa?,karfa kaje ka aikata abinda zamu zo muna dana sani har 'karshen rayuwar mu!!...
Murmushin dashi ka'dai yasan ma'anar sa yayi yace"kede ki zuba ido kisha kallo dan banason katse landan acikin lamari na."Shiru tayi tana binsa da kallon tsoro da mamaki aranta kuwa addu'a take Allah yasa ba mummunan Abu ze aikata ba.Ba wai dan ba taso ya cutar da Baby Bushra bane a'a ita tunanin ta in wani mummunan abu yasa mu Bushra ta tabbata Alhaji Aliyu baze 'kyale duk wani me hannu aciki ba in ma shi ya 'kalesu saboda shi 'dan uwansa ne to hukuma baze 'kyalesu ba...
"Ganin tayi shiru ta lula duniyar tunani ne yasa Ya'u fa'din"haba Rabi ki zama jaruma mana kada ki zamto matsoraciya, dan wallahi bazan fasa 'kudiri na akanta ba gwanda ma kisa ki ranki yayi maganan yana me tsareta da ido.Ajiyar zuciya Rabi ta sau'ke tace" Dadyn Azeema bawai abinda zaka yiwa yarinyar ne banso ba!, tunani hukunci da Yaya ze 'dauka akan duk wanda ya cutar da ita nake kasan muddin ya gane da saka hannun mu aciki baze yafe mana ba!...Dariya Ya'u ya kece dashi,cikin dakakkiyar murya yace"karki damu namiki al'kawarin Yaya baze ta'ba gane da saka hannun mu aciki ba duk wani abu da zanyi'zanyi shine cikin hikima da kuma taku dan haka kicire duk wani tsoro da fargaba a ranki...
"Washe baki Rabi tayi tace" dana fikowa murnan ganin an 'batar da wannan la'ananniyar yarinyar dan Wallahi yanda natsani mutuwa ta haka natsane ta na tsani in bu'de ido na ganta. Cigaba da 'kulla mugayen abubuwa da kuma 'kudirin su nason halakar da Baby Bushra su Ka cigaba da yi kafin Ya'u ya wuce bayan sun samu maslaha....
Madu na parking Azeemah ta fita da gudu tana 'kwala ma Baby Bushra kira tare da fa'din"Babyn Abba Babyn Mam'ma Baby naaaaaaaa ta 'karashe kamar zata tsaga gidan da ihu.Da gudu Baby Bushra ta fito jin muryan Azeemah cike da murna suka rungume juna ahaka suka shiga parlour, Abba da Mam'ma na zaune akan dining suna breakfast suka bisu da kallon so dan ba'karamin jin da'din yanda suke son junan su sukeba duk da kuwa da 'kananun shekarun su...
"Azeemah Kuzo kuyi breakfast,Dan Baby tace"baza tayi break ba se kinzo cewar Hajiya Asma'u".Dariya Azeemah tayi ta ri'ke hannun Baby suka zauna a dining 'din, cheaps da soyayyen 'kwai se kunun gya'da Hajiya Asma'u ta zuba musu.Suna hira suna ci har suka gama mi'ke wa sukayi suna wasa da shiriritan su.Hajiya Asma'u na gamawa suka shige bedroom suka barsu.Cak Hajiya Asma'u data fito daga bedroom ta tsaya ri'ke baki tayi tana bin falon da kallon makaki ganin 'barnan da suka yi mata baki 'daya sun canza wa falon halitta".Sannu 'yan albarka shine kuka lalata min falon ko?aikuwa sena za neku ta 'karashe maganan babu alamar wasa atare da ita.Wi'ki-wi'ki da ido Azeema da Bushra suka fara cike da tsoro su kafara hawaye.
Dariya Alhaji Aliyu da ya fito yake musu yace" lalle yau wasu zasu sha bulala wajen Mam'man su,da gudu suka rugo tare da 'buya abayan sa,Murmushi Abba yayi yace"Ayi musu afuwa Ummun Bushra ba zasu 'kara ba.Da sauri su kace eh"Mam'ma baza mu 'karaba kiyi ha'kuri Abba kace tayi ha'kuri baza mu 'karaba.Murmushi Mam'ma tayi tace" na ha'kura anma karku 'kara yimin ta'adi.Tsallen murna sukayi suka fito daga bayan Abba su kaci gaba da wasan su.Fita Mam'ma tayi ta kira me aikin ta tazo ta gyara falon...
"Adawo lafiya ta yiwa Abba da ake neman sa awajen aiki,sannan takoma ciki.
Da yammaci Ya'u ya turo madu drive yaje ya 'dauko Azeemah,Duk yanda Madu diver yayi da Azeemah tabisa su tafi 'ki tayi,Ganin haka yasa Alhaji Aliyu da Hajiya Asma'u suka shiga rarrashin ta anma, Azeemah ta'ki ji dan tace"cewa tayi ta dawo kenan baza ta koma ba. Abba yace"da Madu ya tafi ai danan dacan 'din duk 'daya ne.Madu na parking Ya'u dake coumpound atsaye ya 'karaso le'kawa cikin motar yayi ganin be ga Azeemah ba,Yasa ya kalli Madu Cikin 'bacin rai ya daka masa tsawa tare da fa'din"Ina Azeemah take??,Jiki na rawa Madu yace"Dan Allah Alhaji kayi ha'kuri Wallahi nayi nayi tazo mu tafi anma ta'ki Alhaji Babba ma yace" tazo anma ta'ki... Be 'karasa ba ya 'dauke shi da mari,cikin hargagi yace"kai wani irin wawa sakarai ne??,da alama ka gaji da aikin kane yasa kake wasa.Ha'kuri Madu ya shiga bashi, ko tanka shi Ya'u be yi ba yashiga motar tare da cewa ya kaisa jiki na rawa Madu yaja motar suka tafi har suka isa Ya'u na surfa masa masifa....
Suna Isa Ya'u ya shiga falom kai tsaye zaune yasa mesu Azeemah da Bushra na wasa Mam'ma da Abba kuma na hira daga gefen su."Sallama yayi suka amsa masa fuska sake,Ya wajen su Hajiya da Momy Azeemah cewar Mam'ma,a ta'kaice Ya'u yace"Suna lafiya.Ganin haka yasa Hajiya Asma'u sukayi shiru basu sake tanka shiba.Ke taso mu tafi dan reni har zan aiko atafi dake ki 'ki ko ya fa'da yana kallon Azeemah?. kafa'da Azeemah ta ma'kale alamun ba zata ba,zare mata ido Ya'u yayi anma ko a jikin ta, ta'ki tashi bin duniya da rarrashi babu irin wanda Ya'u beyi ba anma Azeemah ta'ki bin sa."Abba da Mam'ma 'kin sa baki su kayi amaganar suka 'kyalesu.Haka Ya'u ya tafi rai a'bace aran sa kuwa ya 'kudurce niyyar se ya aiwatar da niyyan sa akan Baby Bushra,koda yakoma gida yasanar wa Rabi yanda sukayi ba 'karamin bakin ciki taji ba,dan ma tana da tsohon ciki ajikin ta anma duk da haka bakamar Azeemah ba,domin itace farin cikin su,lallashin ta Ya'u yayi yace" ze 'dau mataki akai.Seda Ya'u ya jera fiye da sati Uku yana zuwa gidan Alhaji Aliyu anma Azeemah ta'ki yadda ta biyo sa daga 'karshe ma da ta gansa zata fara Ihu tana 'buya haka ya ha'kura ya 'kyaleta acan....
Haka rayuwa ta kasance a 'bangaren gidan Alhaji Aliyu cike da farin ciki suke komai nasu,inda Azeemah da Baby Bushra aka mai dasu makaran ta 'daya boko da islamiyya hatta suturar su kala 'daya komai na rayuwa kala 'daya akeyi musu.Bushra sun taso cikin so da 'kaunar junan su Wanda be saniba zeyi zaton twins ne saboda yanda suke da ha'din kai da kuma mai da hankali amakaran ta musamman ma Baby Bushra shiyasa iyayen ta ke alfahari da ita,komai na rayuwa tare Alhaji Aliyu yake wa Bushra da Azeemah baya ta'ba banbanci tsakanin su...
Abangaren ya'u haka ya ha'kura yabar Azeemah badan ya soba sedan ba yanda zeyi da ita gashi har yanzu yakasa cimma 'kudirin sa akan Baby,anma kobi jima ko bida'de baze fasa 'kudurinsa ba...
*ASALIN LABARIN*_Ga mai bu'katar completed documents din KI YADDA DANI 400 hundred ne se ku tuntu'bi wannan number 09068403802 danji yanda za abiya..._
*Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunuban sa ya Allah ka kai haske kabarin sa ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani...*
*ESHAA CE*🤙🏻
