*BUSHRA*
_By_
_REAL ESHAA_*page 15&16*
________________📖 *ASALIN LABARIN*;Malam idris da matar sa maimuna tu haifaffun garin Kano ne inda akayi musu Auren zumun ta,suke zaune a unguwar"Jakara,batare da ta ta'ba kallon sa ba haka shima be ta'ba kallon ta ba.Zaman lafiya suke inda Allah ya azurta su da samun 'ya'ya uku maza biyu mace 'daya Fatima itace Babba anma suna kiran ta da (fadi)Se kuma me bi mata Aliyu suna kiran sa da(Aliko)bayan haihuwar Aliko Maimuna tu sun 'dauki lokaci me yawa basu sake samun haihuwa ba se daga baya Allah yasa ke azurta ta da samun ciki aka haifi Zakariyya'u suke kiran sa da Ya'u" tun daga kansu Malam idris da maimunatu basu sake samun haihuwa ba shiyasa maimunatu ta shagwaba Ya'u sosai kasancewar shine Auta Ya'u ya taso abai-bai,duk acikin su ba wanda yakai Aliyu ha'kuri da sanin yakamata ga girma ma manyan sa ya 'dauki ma kwabtan su tamkar iyayen da suka haifesa babu wanda zakaji yakawo aibun Aliyu ko kuma ace yayi abinda beda ceba shiyasa yake samun addu'o'i daga wajen dattijawan anguwa da duk wanda suke ala'ka Sa 'banin Fadi da kuma Ya'u Sam basu ganin girman na gaba dasu ga 'dan banzan ba'kin hali gwanda ma Fadi da sau'ki dan wata ran tana rangwanta wa mutane, anma Ya'u bega nin kan kowa da gashi bayan iyayensa da kuma Aliyu babu babu Wanda yake shakka,duk ha'kurin Aliyu beraga wa Ya'u idan yayi babde'deba wannan dalili yasa Ya'u yake shakkar sa ...
Aliyu mutum ne mai zuciyan neman na kansa ya taso da zafin neman halar 'dinsa ya kanyi duk wani Sana'a da yasan ze samu"Sannan abin shi be rufe mai ido ba ze Iya baka shi ya ha'kura shiyasa iyayen sa ke alfahari dashi,duk kyawawan 'dabi'un Aliyu gada yayi awajen mahaifin sa Malam Idris ya koya, domin babu abinda Aliyu ya rage na daga cikin halayyar mahaifin sa sema wanda ya 'kara"Itama Maimuna tu tana da halaye me kyau sede tana da fa'da gata da mita uwa uba saurin fushi da rashin ha'kuri, shiyasa ba aganin alkharin ta duk cikin 'ya'yan ta ba wanda ta fiso kamar Aliyu sede bata nuna masa haka saboda son da Malam idris ke nuna masa afili yake sannan tasan Ya'u da ba'kar zuciya muddin ya fahimci hakan to ze Iya yiwa Aliyu wani illah idan har ya fahimci sunfi son aAliyu hakan yasa ita ta 'boye soyayyar da take masa.
Aliyu NA KOWA shine sunan da kowa ke kiran sa dashi saboda temakon sa ga Al'umma da kuma kyawawan halayyar sa shiyasa mutane ke alfahari dashi sam abin hannun sa be rufe masa ido ba kuma duk da yawan dukiyar sa hakan besa ya zama me girman kai da 'daga wa ba.Cikin hikimar Ubangiji Allah ya sanya masa albarka acikin Sana'ar da yake sosai Aliyu yake tallafa wa marayu da miskinai da kuma masu 'karamin 'karfi....Rana 'daya ciwon ajali yakama Malam idris ba a 'dauki dogon lokaci ba Allah ya kar'bi ajiyan sa"Ha'ki'ka wannan ahali sunga tashin hankali mara misaltu wa 'Ya'yan sa sunyi kuka rashin mahaifin su haka makwabtan sa sunyi jimami da kewar makwabcin kirki kamar sa.Ahaka Iyalan sa suka ha'kura suka danga na komai ga Allah tun daga sannan duk wani 'dawai niya na kansu ya dawo kan Aliyu Na kowa,gashi yayi iya bakin 'ko'karin sa kan Ya'u ya kama Sana'a anma firrrr ya'ki ga shegan kashe ku'di da albazaran ci besan menene tattali ba burin sa idan ya samu ya kashe...Gidan su na Jakara Aliyu ya sayar yace"tunda ba mahaifin su bazasu Iya zama awannan gidan ba.A fagge yasai musu gida me kyan gaske wanda yake 'dauke da sashe biyu ko wanne sashe na 'dauke da 3 bedroom da kuma 'katon falon,Aliyu da Ya'u sun 'dauki sashe 'daya Hajiya ta 'dau sashe 'daya.Ya'u abin nema ya samu duniya tadawo sabuwa sharholiyar sa yake tare da cigaba da shuka rashin mutunci son ransa muddin akazo Neman temako idan Aliyu baya nan se ya kori mutane...Koda Hajiya ta samu labarin abinda yake yi ta ki rasa take masa fa'da akan abinda yake be dace sannnan ya kamata ya kama Sana'a. haka yayi kunnen uwar shegu da maganan ta aganin sa tunda yayan sa yatara dukiya shi base ya nemaba Sannan maganan temako kuwa inde yana gidan baza ayi ba duk wanda yakeso yaje ya nemi na kansa duk wannan abin da yake Aliyu ba shida labari kasancewar sa ba ma zauni bane....
Bayan lokaci me tsawo da rasuwar Malam Idris,Aliyu sukaje 'daurin auren aminin sa Ayuba a Bauchi anan ne yaga wata yarinya daga cikin 'kawayen Amarya tayi masa saboda nutsuwarta bata da rawan kai irin na sauran 'yan matan da ke wajen daga ganin yana yin ta kasan daga gidan tarbiya ta fito.Nan take Aliyu yasanar wa aminin sa,Yaga wata acikin 'kawayen matar sa kuma tayi masa Sannan yayi masa kwatancen yanda take.Dariya Ayuba yayi dan ya fahimci wacce Aliyu yake nufi yace"Kar yadamu 'yar babban malamin garin ne ba suyi 'kasa a gwiba wajen zuwa mika 'ko'kon baran su,Bayan sunje sunyi gaisuwar mutunci kasancewar akwai kyakykyawar ala'ka tsakanin Ayuba da Malam Yahuza suka tambaya kan inba ayiwa Asma'u miji ba suna so.Koda Malam yahuza yagama jin jawabin su se yayi Murmushi yace" badamuwa anbasu anma kafin nan zeji taba kin Asma'u duk da tana da manema dayawa sede ba wanda yazo wajen sa kai tsaye Sannan daganin Aliyu yaji ya kwanta masa arai sosai shiyasa yayi na'am dasu.Sosai sukayi murna,aka tsaida magana akan Aliyu na ko mawa ze turo iyayen sa ayi magana."Kafin su tafi Malam yahuza ya tsaidasu yatura 'daya daga cikin almajiran sa cikin gida yace ya kira Asma'u takawo ma ba'kin sa ruwa,futowa almajiran yayi yace tana zuwa"ba'a 'dau lokaci ba Asma'u ta fito da 'katon hijab har 'kasa 'dauke da ruwan sha akofin silba da 'karamin tire akai tsugunnawa tayi tagaishes u,tunda suka ha'da ido da Aliyu taji wani yanayi Wanda batasan na meneneba,dasauri ta mi'ke tashiga gida"ka'dan su kasha ruwan sannan suka mi'ke cike da farin ciki suka tafi....
Bayan Malam Yahuza ya koma gida yasa aka yimasa kiran Asma'u.Cike da girmama wa taje kiran da mahaifin ta yake mata,Koda taje Malam Yahuza ya 'dauki lokaci yana na zarin ta kafin daga baya yake sanar mata da ya za'ba mata miji yana fatan zata amince domin yana sa ran ze kula mata da addinin ta da kuma tarbiyan ta.Cike da ladabi tace ta amince da za'bin sa domin ta tabbata baze ta'ba za'bar mata abinda ze cutar da rayuwar ta ba.Sosai Malam Yahuza yaji da'din yanda Asma'u ta amince da za'bin da ya mata,shiyasa ko acikin 'ya'yan sa yafi sonta albarka yasa mata Sannan yace takira masa mahaifiyar ta koda mahaifiyar Asma'u tazo Malam Yahuza ya sanar mata abinda ya yanke se tayi fatan alkhairi akai....
"Bayan an gama shagulgulan bikin Ayuba,Aliyu yakoma kano cike da farin cikin samun matar Aure.A cikin daren da Aliyu ya koma ya samu mahaifiyar sa yake sanar mata akan yasamu mata kuma ance ya tura,balefi ta tayasa murna inda tace zata yiwa aminan mahaifin sa maga akan aje atambayo musu,yaji dadi sosai"A washe garin ranan kamar yanda tayi masa al'kawari taje ta tasamu aminan Malam Idris guda uku tayi musu bayani sunji da'di sosai yanda ta sasu acikin lamarin kuma suka shirya akan Washe gari za suje tambaya."Godiya tayi musu sosai tare da addu'o'i Aranta tana mejin farin ciki Alikon ta zeyi aure har rawa sanda ta tashi ta taka sannan kuma tayiwa Allah godiya.
Da komai Aminan Malam Idris suka tafi dashi Bauchi wanda suka san za'a bu'kata awajen aure har sadaki,suna Isa suka sau'ka agidan Malam yahuza nan akayi musu tarba me kyau tare da karramasu kunsan malamai da girmama ba'ki"Gaskiya sun yaba da karamcin mutanen domin sun samu tarba mekyau ba 'bata lokaci suka mi'ka 'ko'kon baran su kan nemawa 'dan su auren 'yar sa,shi kuma Malam yahuza ya amsa da an basu.Awajen akasanya ranan aure cikin 'karamin lokaci sunyi murna sosai da karrama wan da suka samu,sunyi sallamah da juna cike da mutunta juna da kuma farin ciki.
"Shirye-shirye sosai akeyi inda Aliyu ya siya wani 'kerarran gida a Nasarawa tsaruwa da kyan da gidan yayi ba acewa komai,Komai na gidan masha Allah part Uku ne agidan 'daya nasa 'daya na matar sa 'daya kuma na mahaifiyar sa.Ba 'karamin 'bakin ciki Ya'u yayi ba ji yake kamar ya tona rami yasa Aliyu aciki duk da kasancewar yayan nasa berage sa da komai ba anma hakan beha nashi yimasa 'kyashi da hassada ba tamkar ba 'dan uwan sa ba...
Idan kaga abu be zoba to ba'asa masa lokaci bane,A wata ranan juma'a ce da bayan an sa'k'ko daga juma'a dubban jama'a suka sheda 'daurin auren Aliyu Idris Na kowa da matar sa Asma'u yahuza,anyi biki antashi lafiya an kawo Amarya 'dakin mijinta tare da addu'o'i.Masha Allah suna zaman su lafiya cike daso da 'kaunar junan su inda Asma'u take girmama mahaifiyar Aliyu tamkar nata hakan kuwa ba'karamin farin ciki yakesa Aliyu ba,saboda yana son mahaifiyar sa sosai duk da ita bata nuna masa so anma shi yana matu'kar son farin cikin ta kuma yana addu'ar Allah yasa tafara basa kulawan da ko wacce uwa kebawa 'danta duk da yana hango 'kaunar sa agareta anma besan dalilin da yasa bata nuna masa ba.Duk yanda Aliyu yayi da Hajiya kan ta dawo sabon gidan sa 'ki tayi tace"zata zauna a tsohon ita da Ya'u se wani lokaci zata koma can...
Bayan Auren Aliyu da Asma'u da shekara 'daya Aliyu ya keta hazo inda ya dawo Alhaji Aliyu Na kowa mutum me karamci da sanin darajan 'dan Adam kowa na alfahari dashi,wata shekara Na zaga yowa yabi yawa mahaifiyar sa tare da matarsa inda suma sukaje suka sau'ke farali, Bayan sunda wone dangi da 'yan uwa kowa yazo yana tayasu murna sun sau'ke farali Hajiya kam se washe baki take dan ha'korin makka biyu tama'kala abakin ta 'daya asama 'daya a'kasa saboda batason aga bata kai ba addu'o'i kuwa babu irin wanda bata yiwa Aliyu...
Hajiya tayi farin ciki mara misaltuwa Sosai 'kaunar 'dan nata da matar sa ya sake shiga ranta,sede kash babu halin nuna musu irin 'kaunar da take musu saboda gudun tashin hankali da kuma abinda zeje yadawo akullum kuma cikin yiwa Ya'u addu'a take kan Allah Yaya yemasa wannan ba'kin halin nasa ita kanta tana jin ciwon yanda take wofan tar da Aliko tamkar ba ita ta haifesa ba ba yaga duk irin kulawar da yake bata...._Ayi shearing Saboda Allah_
_Ga mai bu'katar completed documents din KI YADDA DANI 400 hundred ne seya tuntu'bi wannan number 09068403802 danjin yadda za abiya..._
*Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaina ya Allah kagafar ta masa zunuban ya Allah ka kai haske kabarin sa ya Allah kaji'kan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani...*
*ESHAA CE*🤙🏻
