7&8

9 0 0
                                    

*BUSHRA*



_By_
_REAL ESHAA_



*Page 7&8* 🖊

________________📖WASHE GARI:duk da kasancewar Alhaji Aliyu ba suyi bacci da wuri ba hakan be hana su tashi
da wuri ba.Shiya fara tashi sannan ya tashi Hajiya Asma'u, Alwala yayi ya nufi masallaci.Bayan tayi raka'atin fajir da asbah sannan ta mi'ke kitchen ta shiga gas cooker ta kunna Sannan ta ta fasa ruwa,Bayan ya tafasa ta juye tayi wanka tana fito ta shirya bata 'bata lokaci wajen kwalliya ba,kitchen ta koma ta ha'da musu breakfast me sau'ki sannan ta shirya a dining.Ruwan 'dumi ta ha'da me zafi ta yiwa Baby Bushra wanka sannan ta ta shirya ta acikin 'daya daga cikin kayan da Alhaji Aliyu ya siyo mata da 'kyar ta iya sa mata kwalli a ido.Da sallama Alhaji Aliyu ya shiga bedroom 'din,Jin gina bayan sa yayi ajikin 'kofa yana kallon su cike da so da 'kauna ba 'karamin kyau suka masa,A 'kasan zuciyar sa kuwa tasbihi yakewa Ubangiji daya a zurta sa da samun 'ya ta hanyar da beyi zato ba....A nutse Asma'u ta 'daga kanta jin alamun ido na yawo ajikin ta idanun su ne ya sar'kafe da juna kasancewar shima ita yake kallo."Fuskar ta 'dauke da murmushi tace"Barka da safiya Abban Bushra!.Wani sanyi ne ya mamaye ilahirin zuciyar sa wai yau shi ake kira da Abba,A fili ya furta "Alhamdulillah ala kulli halin".Murmushin sa me kyau ya mata yace" barka de Ummun Bushra kyakyakyawar matata me kyawun hali,yafa'da yana 'karaso wa cikin 'dakin fuskar sa 'dauke da murmushi.Zama yayi a kusa da ita ya 'dauki Baby Bushra dake 'kwance agefan ta wasa ya shiga mata yana 'daga ta sama,kasancewar shi mutum ne me son yara  se gashi yau Allah ya mallakama sa 'ya amatsayin ta sa...
Wayarsa ce tayi 'kara alamar shigowan kira,Ahankali ya ajiye  Bushra dake hannun sa,yayi picking call 'din maganan da be wuce minti uku ba yayi sannan ya katse kiran.Kallon sa ya mayar kan Asma'u dake shiryawa Baby Bushra kayan ta yace"Na gama sawa akawo min komai na Baby nan da wasu awanni zasu 'karaso Insha Allah,"sannan nace"musu ko abinda ban rubuta a list 'din ba inde sun san Ana yiwa Jarirai amfanin dasu to su ha'do min dashi...
"Masha Allah,Ubangiji Allah ya'kara bu'di da 'daukaka,Allah yasa kafi haka Allah yabamu ikon ri'ke amanar mu  ta fa'da tana wasa da hannun Baby Bushra dake 'kafan Alhaji Aliyu."Ameen Ummu Bushra Insha Allah zamu kasance masu ri'ke Al'kwari, da kuma amanar ta har sanda zamu sadata da iyayen ta ko kuma mu Aurar da ita,Inde ina numfashi Baby ba zata ta'ba neman wani abu ta rasa acikin rayuwar ta ba Insha Allah.Yana gama fa'din haka yami'ke yace" zanje gidan Hajiya in sake bata ha'kuri kin ga jiya ta tafi tana fushi damu anma ba da'dewa zanyi ba kafin akawo kayan zan dawo Insha Allah seki fara arrangement na komai kafin na dawo.Cikin sanyin murya tace"Adawo lafiya Allah yasa kuma Hajiya ta amince da bu'katar mu.Ameen ya amsa sannan ya fice....
Alhaji Aliyu na fita yashiga mota tare da yi mata key,hong yayi me gadi ya bu'de masa yafice daga gidan zuciyar cike da tunani dan besan yanda Hajiyar sa zata am shesa ba addu'ar sa 'daya Allah yasa ta ha'kura tabar sa da 'yar sa kada ta raba su Kamar yanda ta fa'da,sosai yake jin 'kaunar 'yar sa sannan baya fatan wani abu ya ra basu..
Da wannan tunani ya isa gidan da kuma far gaban abinda ze biyo baya,Yana tsoron yaje tace"sai ya maida 'yar sa haka de ya daure ya isa.Yana  parking ya fito,Kai tsaye sashen ta ya nufa.Zaune ya hangota ta hakimce akan kujera tana goga goro a'karamin roban dake gaban ta.sallama yayi,shiru ba amsa sakewa yayi akaro na biyu nan ma shiru,bu'de baki yayi da niyar sake wa akaro na uku anma ya fasa sakamakon mugun kallon data jefasa dashi.

Cikin sakewar gwiwa yanemi gefe da ita daga 'kasa ya zauna ina  kwana yace"da ita cike da ladabi.Banza tayi masa ta cigaba da goga goron ta tana gya'da kai.Dan Allah Hajiya....Da sauri ta dakatar dashi ta hanyar 'daga masa hannu,Shiru yayi tare da sunkuyar da kai batare daya 'karasa fa'din abinda ke bakin sa ba.Roban goron dake gaban ta ta janye tsuke baki tayi tace" Bana bu'katar gaisuwar ka dan haka ka ri'ke abin ka tunda ba ganin girma na kake ba ai babu amfanin zuwa gaishe ni tunda kafifita wancan 'diyar aljanun fiye dani,kuma Wallahi bana bu'katar sake ganin 'kafan ka acikin gida na inde har baka fitar da wancan aljanar daga cikin gidan ka ba tana kaiwa nan ta fashe da kuka cikin muryan kuka tace"Me za ayi da wannan zamani ace Sam 'ya'ya basu yi wa iyayen su biyayya mu lokacin mu ko wuta iyayen mu su kace mu shiga, shiga muke mu zauna saboda tsananin biyayya dubi nan 'dina ta fa'da tana 'ko'karin kwaye zanin ta...Cikin tashin hankali Alhaji Aliyu ya ri'ke hannun ta,yace"Dan Allah Hajiya kiyi ha'kuri ki yafe min!.Hannun ta ta fisge daga nasa tace"Aida kabari na nuna maka shedar biyayyan da muke ma iyayen mu...Shiga falon Ya'u yayi bakin sa 'dauke da sallama kasancewar ya hango shigowar yayan nasa,farin ciki ne  ya ziyarci zuciyar sa ganin hawaye sha'be-sha'be a fuskar Hajiya ga kuma yanda take fa'da kamar zata ari baki.Waje ya samu daga gefen Hajiya ya zauna."Cikin tashin hankali Alhaji Aliyu yace"Dan Allah Hajiya kiyi ha'kuri fushin ki masiface agareni dan Allah kiji kaina kiya femin lefin dana miki anma kar kice na rabu da 'yata ya 'karashe yana me ri'ke 'kafafun ta...Tausayi ya bata tausayi,anma kafin tace"wani abu Ya'u yayi saurin taran numfashin ta tare da fa'din"Haba Yaya wai dan Allah meyesa kake da taurin kai akan wannan maganan, akan 'karamin abu ka kasa faran tawa Hajiya rai,Wallahi da nine ta bu'kaci nayi haka da tuni nabi umarnin ta nayial abinda take so.A gaskiya na fara  zargin juyar maka da 'kwa'kwalwa sukayi in ba haka ba taya zaka 'ki bin umarnin Hajiya bayan da ba haka kake ba maganan gaskiya akwai abin duba wa acikin wannan lamarin,Ya'u ya 'karashe maganan yana Satan kallon Hajiya...Jijjiga 'kafa Hajiya keyi cike da masifa,kallo 'daya zaka mata kasan ran ta yagama 'baci.Ajiyar zuciya Ya'u ya sau'ke ganin ya gama kunna Hajiya...

Alhaji Aliyu beku tanka saba yace"Dan Allah haji...be 'karasa ba Hajiya ta daka mai tsawa Cike da masifa tace"Wallahi in baka tashi kabar min gida ba senayi maka abinda zaka da'de kana mamaki...Alhaji Aliyu be sake cewa komai ba ya mi'ke ya fita zuciyar sa na 'kuna,adede kofar fitan ne suka ha'du da Rabi 'dauke da Azeemah, gaishe sa tayi"Babu walwala atare dashi ya amsa.Shiga falon Rabi tayi ta samu Ya'u se famfo yake yiwa Hajiya, Zama tayi suka dunga zuga hajiya,basu suka bar taba seda suka gama cusa mata tsanar Baby Bushra,tu kunna suka kama gaban su cike da farin ciki,dan sun san Alhaji Aliyu da biyayya dole ya kaita gidan marayu tunda yana da tausayi baze Iya jefar da ita kamar yanda Hajiya ta bu'kata....
Haka Alhaji Aliyu ya fita zuciyar sa cike da 'kunci,ha'ki'ka baya son 'bacin ran mahaifiyar sa kuma sannan baya tunanin ze Iya rabuwa da 'yar sa saboda ita 'din amana ce agaresu.da haka ya Isa gida kafin yashiga seda ya dedeta kansa yanda Asma'u baza ta fahimci yana cikin damuwa ba.Koda ya Isa gida yasamu duk kayan dayasa akawo mai anka wosu.lokacin daya je Asma'u tana busy shiyasa bata fahimci damuwar da yake ciki ba,Shima yaji da'din hakan aran sa dan baiso ta fahimci halin da yake ciki direct 'dakin sa yawuce dan beson Hayaniya...
Misalin karfe hu'du suka gudanar da 'karamar walima Wanda da gasu se ma'kobtan su guda uku se kuma 'kawayen Asma'u guda biyu,masha Allah wajen yayi kyau...An shirya Baby Bushra cikin ha'da'dden shiga na alfarma Wanda duk shigarsu kala 'daya ce aka kawo musu. haka akaita 'daukan su pic kala-kala sunci me kyau sun kuma sha me kyau inda baby Bushra tasha addu'o'i daya wa,haka taro yatashi cike da farin ciki da kuma mutunta juna.agajiye Alhaji Aliyu suka koma cikin gida inda suka sake wanka sukayi sallah tu kunna suka kwanta,bacci me da'di yayi gaba dasu anma banda Abban Bushra,shikam kasa bacci yayi saboda furicin mahaifiyarsa se dake masa yawo akai,Tashi yayi yai alwala ya tada sallah raka'a biyu yayi yana ro'kon Allah ya sassauta zuciyar Hajiyar sa ta barshi da 'yarsa.

Koda ya'u yaga walimar da Yayan nashi yayi abin ba'karamin 'kona mai rai yayi ba,wato harma yafara 'bar natar mata da dukiya lalle zeyiwa tokar hanci tun lokaci be 'kure masaba ze 'dauki tsat-tsauran mataki.
_After four years_....

_Ga duk mai bu'katar completed documents din KI YADDA DANI 400 hundred ne se ya tuntu'bi wannan number 09068403802 danjin yadda za'a biya..._

*Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah ka gafar ta masa zunuban sa ya Allah ka kai haske kabarin ya Allah kaji'kan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya...*

  

                          *ESHAA CE*🤙🏻

BUSHRAWhere stories live. Discover now