*BUSHRA*
_By_
_REAL ESHAA_
*PAGE 3&4*🖊
______________📖'karasa wa falon su kayi ciki mutuwar jiki ganin irin mugun kallon da suke jifan su dashi.Dan Allah Hajiya ku zauna se inyi muku ba yani yanda zaku gamsu cewar Alhaji Aliyu.Harara Hajiya ta zabga musu kamar idanun ta zasu zubo, ganin rainin hankali irin nasu daga zuwa asibiti aduba lafiyar su sesu dawo mata da tsaraban jaririya saboda an maida ita shasha.Zama tayi tare da ha'de giran sama data 'kasa goro ta 'balla tace"Ina sauraron ka kuma Wallahi ka tabbatar duk abinda zaka fa'da gaskiya ne wanda ze min amfani in kuma ka tabbatar da babu amfani da ze min to karma ka wahalar da kanka da bakin ka kuna idan min 'karya wallahi ban yafe maka ba duniya da lahira.Kusa da ita Alhaji Aliyu ya 'karasa ya zauna jiki ba laka,Ahankali Hajiya Asma'u ta 'karasa kusa da ita da niyyar zama.Cike da masifa Hajiya tace"kar ki kuskura ki zauna kusa dani da wannan abin dake hannun ki dan bansan tsiyar da ke ciki ba ina zaman zama na ki kwaso min jaraba da ala 'ka 'kai....Jiki a sa'bule Asma'u ta koma nesa da Hajiya ta zauna tana 'ko'karin maida hawayen dake shirin zubo mata,ta'be baki Hajiya tayi tace"kyaji dashi gulmammiya....
Daga haka ta mayar da kallon ta kan Alhaji Aliyu,tana Hararan sa tace"kai nake sauraro ka wani sun kuyar da kai kamar me 'daukan darasi...
Lumshe idanu Alhaji Aliyu yayi duk wani 'karfin gwiwa da karsashi da yazo dashi yanzu se yaji babu.Cike da ladabi yace"Dan Allah Hajiya kiyi ha'kuri ki fahimce ni,Wannan jajiririyar da kike gani ba komai bace face baiwar Ubangiji da riban ha'kuri da kuma juriya yasa Ubangijin talikai ya ha'da mu da wannan kyautar baiwar tasa.Numfasa wa yayi yafara bata labarin abinda Dr Usman ya fa'da musu kamar yanda ake fa'da masa a sauran asibitin...Hararan sa Hajiya tayi tace"Toh ai wannan ba sabon Abu bane na da'de da sani so nake kayi min bayanin inda kasamo wannan abin??ta fa'da tana hannu Hajiya Asma'u".'kasa da kai Alhaji Aliyu yayi cikin sanyin murya yace"Tsintar ta mu kayi Hajiya,Cikin hukunci Ubangiji gagara misali ya ha'da ni da 'ya ta hanyar da banyi zato ba.Shiru yayi yana me kafeta da idanu tare da jiran jin abinda za tace a zuciyar sa kuwa addu'a yake Allah yasa ta amince ya ri'ke wannan jaririyar,dan yanzu itace garkuwar sa Sannan ita ce zata zamo mai tamkar gudan jinin sa...
Ya zurfafa a cikin tunani yaga Hajiya tami'ke tsaye tana salati ciki hargagi tace",yanzu Aliko neman haihuwar taka har takai kaje 'kunguru min jeji ka 'dauko 'yar aljanu jikar aljanu tatta'ba kunnen Ifritu!!,dan wannan jaririyar de ba mutum bace,Yo in'ma ba sakarci irin naku ba ina za'a samu 'dan mutum shi ka'dai a wannan dokan jejin anya Aliko kana da hankali kuwa??kode gamo kayi ne da mutanen 'boye suka bu'de maka ido??Toh Wallahi ka bu'de kunnen ka kaji ni da kyau ba dani za'ayi wannan sakarci da rashin arzi'kin ba ehee...Banda hawaye ba abinda Hajiya Asma'u keyi tunda Hajiya ta fara magana take kuka,tsoron ta 'daya kar ace za'a rabata da Jaririyar ta.Lumshe Idanun ta tayi hawayen da take 'ko'karin mayar wa sukayi nasaran zubo mata tasan halin mijin ta baya tsallake umarnin Hajiyar,Tasan muddin tace"bata so dole akaita gidan marayu,anma ta 'kudurce aran ta duk runtsi duk wuya ba zata ta'ba rabuwa da jaririyar taba...'Kun'kunin uban me kike Ma'u bade zagina kike ba Hajiya tayi maganan cike da masifa.Da sauri Asma'u ta bu'de Idanun ta tare da girgiza kai ba tare da tace komai ba.Tsaki Hajiya taja tace"munafuka!..
Cikin sanyin murya Alhaji Aliyu yace"dan Allah Hajiya kiyi ha'kuri Insha Allah wannan Jaririyar alkhairi ce acikin rayuwar mu dan Allah ina ro'kon ki kada kira bamu da ita ya fa'da hawaye nataru wa a kwarmin idanun sa ko ka'dan baison abinda ze raba su da Jaririya,Gashi Hajiya ta'ki tanka masa tunda yafara magana ya tabba wannan shirun da tayi ba alkhairi ba ne.
Gyaran murya Ya'u yayi wanda tun da aka fara magana bece komai ba saboda wani malolon ba'kin ciki daya to kare masa ma'koshi,Dede ta kan sa yayi yace"Haba Yaya mekake fa'da ne kana tunanin zaka ri'ke wannan Jaririyar acikin mune?a kuma acikin zuri'ar mu??Kai ma kasan wannan ba abu me yiwa bane kace zaka ri'ke 'Yar aljana to bada yawun mu ba.Kai ina sam wannan Aljanar Jaririyar ba zata zauna da muba."Wallahi Hajiya tun wuri ma ki fa'da masa yafitar da wannan abin daga cikin Gidan nan ni Wallahi daga ganin ta ma nasan babu alkhairi atattare da ita ji beta fa kamar wata jikar sarkin aljanu....Tunda Ya'u yafara magana Alhaji Aliyu ke kallon 'kanin nasa cike da 'dumbin mamakin yanda yake magana cike da Isa se kace shine gaba dashi...
Yi shiru Ya'u bar wahalar da bakin ka dan wannan Jaririyar ba taga wajen zama acikin wannan Gidan ba eheee! dole ma su fitar da ita idan su ta lashe musu kurwa to mu namu garau yake ehe!...Da sauri Hajiya Asma'u ta 'karaso kusa da Hajiya ta ri'ke 'kafar ta tace"Dan Allah Hajiya kiyi min rai ki dubi girman Allah da kuma darajan ma'aiki kada kira bani da ita Wallahi ina son ta...
Wani shegen Kallo Hajiya ta watsa mata cike da jaraba tace"Wallahi na gama magana wannan Jaririyar ba zata zauna acikin zuri'ar muba...Dafe kai Alhaji Aliyu yayi baki 'daya yarasa abinda ze yi,ya rasa ta wani hanya zebi yafahim tar dasu...
Maganan Hajiya ce ta katse ma Alhaji Aliyu tunanin da yake,"Ya'u wuce mu tafi, kuma Wallahi Aliko ka tabbatar kafin na sake dawowa cikin Gidan nan kafitar da wannan aljanar tana gama fa'din haka tayi waje yayin da Ya'u yabi bayan ta cike da farin ciki dan yayi al'kawari inde yana numfashi baze bar wannan Jaririyar acikin gidan yayan na saba dole ya zage 'damarar cusa tsanar yarinyar acikin zuciyar Hajiya dama duk wani Wanda suke da ala'ka dasu.Har suka fita Hajiya na mita yayin da Ya'u ke sake zu gata ita ko ta hau kai ta zauna daram...
Suna fita Hajiya Asma'u ta koma kusa da mijin ta tare da sanya mai kuka,Cikin raunin murya tace "dan Allah Aliyu karka bari su ra bamu da ita wannan itace ka'dai damar da Allah yabamu kada mu bari ya kufce mana.
Tausayin ta ne ya sake mamaye zuciyar Alhaji Aliyu, cike da so yace" Insha Allah nayi miki al'kawarin duk runtsi duk wuya bazan bari arabamu da 'yar mu kuma amanar mu,kalamai masu da'di ya dinga mata har ta samu nustuwa mi'kewa yayi yaje ya ha'da mata ruwan wanka seda tashiga sannan yafice....
Direct wani super market naka yan jarirai Alhaji Aliyu yaje sosai ya jidan mata Jaririyar kaya masu kyau da kuma tsada,duk wani abinda yara zasu bu'kata yasa an ha'da mata,sannan yaje yasai madaran yara Wanda xasu fara bata kafin gobe suje hospital abasu wanda ya dace da ita...sosai aka cika masa bayan Booth da siyyayan Jaririyar sannan yashiga mota ya mata key...
Asma'u na fito wa daga wanka tabi Jaririyar da kallon so da kuma tausayi wacce Har izuwa yanzu baccin wahala take,ruwan zafi ta ha'da tasa ta aciki aikuwa ta calla 'kara,da kyar tasamu ta wanke ta tana 'deta a towel tunda bata da kaya,tunanin take to ina Aliyu yaje,gashi yarinyar se kuka takeyi hannu tasa mata abaki tana tunanin mafita...
Da sallama ya shigo hannun sa Ni'ki Ni'ki da kaya sannu da zuwa Asma'u tayi masa tana murmushi,Martanin murmushi ya mayar mata tare da fa'din " kinga nafita ban fa'da miki ba kiyi ha'kuri naje suyowa baby kaya ne.Allah sarki sannu da 'ko'kari Allah Ubangiji ya'kara bu'di da 'daukaka, ameen ya amsa yana fito da kayan cikin ledan.
Madara ta ha'da ta bawa baby aikuwa tasha da yawa sannan tasa mata kaya,masha Allah jaririyar bade kyau ba.
Abangaren ya'u kuwa suna Isa gida...
_Ga masu bu'katar complete Documents 'din KI YADDA DANI 400 hundred se su tura da katin mtn ta wannan number 09068403802 ko kuma ta account 'dina Abdullahi Aishatu keystone bank 6030406548..._
*Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunuban sa ya Allah kaji'kan duk kan musulman da suka riga mu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani...*
Dan Allah kuyi shearing na sa👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
*ESHAA CE ~*🤙🏻
