*BUSHRA*
_By_
_REAL ESHAA_*page 9&10* 🖊
_________________📖 _After four years._
Abubuwa da dama sun faru acikin wa'annan shekarun,ciki kuwa hadda Amincewar da hajiya tayi na barin Baby Bushra ta zauna dasu anma da shara'din tana girma Alahaji Aliyu zasu sanar mata cewa basu bane asalin iyayen ta tsintar ta sukayi a dokar jeji a'kasan bishiyar mangoro me shegen duhu....Ba musu Alhaji Aliyu ya amince saboda yana da ya 'kinin kafin Bushra ta girman Insha Allah komai ze dede ta sannan ya mantar da Hajiya maganan.A 'bangaren Ya'u kam ba haka yaso ba dan ko ka'dan beji da'din amince war da Hajiya tayi ba yaso taci gaba da kyarar Alhaji Aliyu har seya mayar da Bushra inda ya 'dauko ta ko kuma ya kaita gidan marayu,anma Hajiya ta watsa masa 'kasa a ido da sannu ze yi abinda se ya jijjiga kowa,Wannan dalilin yasa tsanar Baby Bushra ya sake nun kuwa azuciyar Ya'u fiye da ko yaushe,A 'bangaren Rabi ma haka take jin tsanar Bushra kamar ta kasheta!!,Yayin da sha'kuwa me 'karfi yashiga tsakanin Bushra da Azeemah,Ya'u na matu'kar son Azeemah kamar ran sa dan ya gwammace ran uban kowa ya 'baci inde Azeemah za tayi farin ciki duk wani Abu da Azeemah keso shi Ya'u ke mata...Wata kyaky-kyawar yarin yace" ta fito daga falon wacce a 'kalla shekarunta baza su wuce hu'du ko biyar ba,duk da kasancewar ba fara bace,anma kalar fatan ta me kyau ne dan tafi kama da black America,tanada dara-daran idanu wanda eyeballs 'din ya kasance brown....Duk da 'kan 'kantar shekarun ta hakan be hana aini hin kyawun ta fito ba...
Cikin shigar dogon riga me kyan gaske ta fito an tufke mata gashin ta da ya sakko yana lilo har ka fa'dan ta da farin ribont yayin da takalmin ta shima fari ne rigar ta kuma ja ce cikin nutsuwa ta nufi parking space fuskar ta 'dauke da fara'a."Hararan ta Hajiya Asma'u tayi tace"Wallahi Baby kin cika lazy tun yaushe muke jiran ki anan anma dubi yanda kika 'bata mana lokaci??.Murmushi tayi ta kama kunnen ta,tace"Sorry Mam'ma ban 'karawa...
Dariya Alhaji Aliyu yayi yace"Oyaaa Baby zoki shiga mu tafi dan naga alamun kun manta dani keda Mam'man ki.Sorry Abba na ayimin afuwa ai kasan bazan Iya mantawa da kuba.Murmushi yayi yaja hannu ta suka shiga mota,
Hong yayi me gadi ya fito da sauri ya bu'de musu gate,Har suka isa gidan suna hira.Alhaji Aliyu na parking bayan sun isa gidan.Baby Bushra ta bu'de murfin motar ta fita da gudu ta nufi sashen su Azeemah."Karo su kayi da Ya'u wanda shigar ta yayi dede da fitowar sa zeje sashen Hajiyar sa.Cikin rashin sa'a Baby Bushra ta take mai 'kafa. Seda ta 'dauke wuta na wasu mintuna sakamakon wani gigiceccen marin da ya sau'ke mata a kuncin ta...Wani razanan nen 'kara tasaki wanda seda compound din gidan ya'dauka suwan muryan ta...A Iya tsawon rayuwar ta ba'a ta'ba yi mata irin wannan gigiceccen Marin ba...Jin Ihun ta yasa Azeemah ta fito da gudu Cak! taja ta tsaya ganin yanda hannu mahaifinta ya fito ra'da'da afuskar 'kawar ta...
Banza la'ananniya me 'kiran aljanu tsintacciyar mage,wacce iyayenta suka jefar da ita saboda gudun abin kunya,Wallahi idan na sake ganin wannan tsinannen 'kafan naki asashena se na 'bal-'ballasu cikin tsananin fushi Ya'u ya 'karashe maganan yana huci saboda wani irin tsanar Bushra dake sake nin kuwa a zuciyar sa.Kuka Azeemah tasa tace" Dady dan Allah kar ka 'kara dukan ta koyi mata fa'da inde har kana sona!, in kuma ka 'kara wallahi zan 'ki cin abinci kuma bazan sake kula kaba!!,Wani mugun kallo Ya'u ya bita dashi yace"maza wuce ki bani wuri kafin nakar yaki banza mara tunani...
Da gudu Baby Bushra ta fita daga sashen nasu tana kuka me ta'ba zuciyar duk wani me imani duk da 'kan'kantan shekarun ta hakan be hanata fahimtar Dady Azeemah baya 'kaunar ta ba.
Direct sashen Hajiya ta nufa tana shiga ta'fada kan Abban ta"'dago kanta Alhaji Aliyu yayi cikin tashin hankali!,Yace"meyesa ki Baby?",Shiru Bushra tayi takasa cewa komai se shesh-she'ka da take,"Kanta ya sake 'dago wa yana share mata hawaye yace"ki nutsu ki fa'da min meyesa meki??.Bushra na kallon sa tace"Abba meyesa Dadyn Azeemah baya sona??,Dan na taka 'kafar sa by miske shine ya mare ni kuma yace"idan na sake zuwa sashen sa seya 'ba'b'ballani".Ran Alhaji Aliyu in yayi dubu ha'kika ya 'baci tun ba yau ba yasan irin tsanar da ya'u ke nuna wa Bushra kawai yana kawar da kaine dan baya son matsala anma bakomai yasan matakin da ze 'dauka...Muryan Baby Bushra ya katse masa tunani,Tace"kuma cewa yayi wai iyayena sun jefar dani saboda abin kunya!!,Ai Abba ba zaku jefar dani ba kuma kuna so na ko??.Da sauri Alhaji Aliyu da ke kallon ta ya gya'da mata kai yace"Muna son ki Baby kuma Insha Allah babu abinda ze ra bamu dake,Lumshe Idanun sa yayi yana jin wani irin 'daci a ma'kogoron sa,wato tun yanzu Ya'u yake son fallasa wa Baby sirrin ta!,Sirrin da yake so binne wa har Illah Masha Allah babu wanda ze San dashi shine Ya'u ke 'ko'karin fallasa wa.Ko ka'dan Hajiya Asma'u bataji da'din abinda Ya'u ke yiwa Bushra ba domin aganin ta babu wanda yafi 'karfin 'kaddara anma ta lura da irin tsanar da Ya'u yake nuna wa Bushra tamkar ita ta za'ba wa kanta kasancewa ahaka Wanda ko ka'dan hakan be dace ba...
Ahankali Alhaji Aliyu ya 'daga Baby Bushra dake kan cinyar sa ya mi'ke afusace ze fita!!.
"To 'dan da masu 'ya ka wani tashi fuuuu kamar guguwa gidan Uban wa za kaje ahaka??Cewar Hajiya da tunda Bushra ta shigo 'dakin ba tace"komai ba se bin ta da harara da take kamar idanun ta zasu zazzago...Ko ba zaka dawo bane ka tsaya min akai kamar dogari? " Hajiya ta sake fa'da tana jifan sa da haraea."Hajiya ba kiji irin kalaman da Ya'u ke fa'da wa Bushra ba hakan ya dace kenan??".Allah yasa Buroshi ce ba Bushara ba,daka tashi da dogon 'kafafun ka ina za kaje?,Ina ce de ba 'karya ya mata ba?,in ba gudun abin kunya ba taya iyayenta zasu jefar ta!? Wato saboda ya fa'da mata gaskiya shine zaka je ka masa rashin arzi'ki,Kai a dole ga me 'Ya ko?.Tun randa Alhaji Aliyu yazo da Baby Hajiya ta dena sake masa fuska maganan arzi'ki baya ha'da su...Jiki ba kwari Alhaji Aliyu ya koma ya zauna duk zuciyarsa ba da'di....
Azeemah na shiga falon ta fa'da kan Rabi cikin kuka tace"Momy kinga Dady ya mari Bushra kuma yace"Idan ta sake zuwa sashen mu seya karya ta dan Allah ki bashi ha'kuri kinji!!?.Ture ta Rabi tayi tace"dalla can ni 'da gani banza wacce bata da kishin kanta, Ina ke 'yar asali da wacce bata da asali zaki ha'da kanki da ita,tana tsintacciyar magen?,"Wallhi koda wasa na sake ganin ku tare Allah ne ka'dai yasan azabar dazan gana miki!!.Dagudu Azeemah tami'ke tashiga 'dakin ta ta rufe 'kofa tana kuka.Tsaki Rabi tayi tace"idan kin gaji da zaman zaki fito ne... Fasa zuwa sashen Hajiya Ya'u yayi saboda takaici ya koma 'daki yayi kwanciyar sa yana tunanin yanda zeyi maganin wancan tsintattiyar Aljanar..
Shiru falon yayi Na wani lokaci,Hajiya de bata sake cewa komai ba se goga goran ta da take,'Ganin shirun yayi yawa ne yasa Hajiya ta 'daga kai seda ta 'kare musu kallo 'daya bayan 'daya Sannan tace"Ina fatan de Baku mance da al'kawarin da kuka 'dauka ba??.Shiru su kayi ba wanda yace"da ita uffan,"Ta'be baki Hajiya tayi tace"Ai idan maye yaci ya manta uwar 'da baza ta manta ba.Hajiya mu zamu wuce "se anjima cewar Alhaji Aliyu." Yo ai dama bani na gayyato Ku ba dan haka umma tagaida Aisha ta fa'da tana binsu da harara.Fakar idon su Alhaji Aliyu Bushra tayi ta zabga wa Hajiya harara da brown eyeballs din ta tare da murgu'da baki.Salati Hajiya tayi tace Aliko kaga abinda wannan aljanar 'yar taku ta min ko?.Kallon Bushra Alhaji Aliyu su kayi se sukaga kanta a'kasa kamar me wasa.Ha'kuri Hajiya Asma'u ta bata Sannan taja hannun ta suka fice duk ransu ba da'di akan abinda Ya'u yayi wa Bushra,Alhaji Aliyu yasan duk abinda Ya'u keyi ya samu goyon bayan Hajiya ce.Mota suka shiga sannan ya fice daga gida....._Ga duk mai bu'katar completed document din KI YADDA DANI 400 hundred ne seya tuntu'bi wannan number 09068403802 danjin yanda za abiya..._
*Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah kagafar ta masa zunuban sa ya Allah ka kai haske kabarin sa ya Allah kaji'kan duk kan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da imani...*
*ESHAA CE*🤙🏻