BA LABARI
By
Fadeela Lamido
EXQUISITE WRITER'S FORUM.Page 7- 8
Dakewa tayi, ta hanyar boye firgicin ta tare dayin kasa da murya tace, " Unaisa! lafiyar ki?"
Cikin sauri ta dago ta kalli Dada adan firgice dan batai tsanmmanin ganin ta ba, dago hannunta tayi daga Kan sakatar da take kokarin cirewa sannan tace, " lafiya lau Dada"
Unaisa, me yake damun ki?, kuma Ina zaki da wannan Dattijon daren?
Gida zani Dada, dakin Innawuro, nakasa bacci kuma na tabbatar matsawar ba dakin Innawuro na kwanta haka zan wayi gari ban runtsa ba.
Wani irin kallo Dada taiwa Unaisa sannan tace, " ko zaki kwana bakiyi bacci ba babu inda zaki da wannan tsohon daren, ki koma ki kwanta kar Malam ya fahimci wani abu, kin sani sarai idan Malam ya ganki anan duk zuviyoyin mu bazasu yi dadi ba, idan safiya ta waye saiki tafi inda kike sakewa, banda abunki Unaisa garadan maza ke kawo miki hari, wadda harke dake ganin su kince baki rike me suke cewa.
Ai Dada dana kasa bacci na tuna kalmomi biyu da mutumin ya fada, natuna mara lafiyan kafar yace, gudu da waiwaye shike kawo mugun zato, sannan ya sake cewa kowa yaki tsotse hannu beji dadin miya bane.
Lumshe ido Dada tayi zuwa can ta bude sannan tace, " yaje ya tsotsi hannun uwar sa, danni ban gane inda zancen shi ya nufa ba, wlh Unaisa ke macece bana miji ba, kuma kinkai minzilin da maza zasuyi tunanin kasancewa dake musamman idan suka fahimci cewa ke kadaice agidan....
Dada gobe zan dawo, ni yanzun idan ba jina nayi dakin Innawuro ba hankalina bazai kwanta ba.
Wato kina nufin kin kafe kenan sai kinbi hanya awannan lokacin?
Shiru tayi dan haka Dada tace, shikena, Allah ya tsareki aduk inda kike, juyawa tayi ta nufi dakin da ta fito saidai bata iya runtsawa ba tunda taji alamun Unaisa bata dawo ba, idon ta bushewa yayi tunani da zullumi sun hanata bacci.
*****
Unaisa kuwa cikin tsanin firgici tare rawan jiki ta isa gida, bayan ta bude gidan ta shiga bakinta dauke da addu'a, tsitt gidan sannan ta bude kofar dakin ta shiga tare da kunna wutan lantarkin dake dakin, take haske ya gauraye dakin, hannunta tasa ta cire nikaf din dake fuskarta ta ninke ta aje a inda ta saba ajewa, sannan ta cire hijjabin, shima ninkewa tayi ta adana sannan ta dauki rigar da ta saba sawa idan zata kwanta ta cire kayan jikinta ta saka su, wani mayafi ta dauko babba ta yafa tare da daurewa a wuyan ta, dan tunda ta fara nono ko ita kadai adaki bata iya barin kirjinta abude, zaune tayi abakin gadon ta hada kai da guiwa, kanta abude.
Gashin kantane ya baje agadon bayanta yayin da da yakai tsakiyan bayanta baki sidik.
Tsayon lokaci ta dauka ahaka, hawaye na zuba afuskarta yayin da nutsuwa take kara shigarta, sai misalin 3 ta kwanta bajimawa bacci ya dauke ta.
Washegari da sassafe Dada ta iso bugu biyu tayi Unaisa ta gane Dada ce dan haka taje da saurinta ta bude kofar tare da fadawa jikin ta.
Lumshe ido Dada tayi jin Unaisa jikinta, a jiyan zuciya ta sauke me karfe sannan suka nufi gidan Unaisa na kwance ajikinta.
Cikin daki suka nufa, yayin da Dada tabi Unaisa da kallo tsayon lokaci sannan tasa hannunta ta cire nikabin fuskarta zuba mata Ido tsayon lokaci sannan tai maza ta rike kunnen Unaisa.
Cikin sauri Unaisa ta yamutsa fuska tare da kanne idonta daya tare da nuna alamar tanajin zafi tace, Dada kiyi hakuri Allah akwai zafi.
Aina dauka bakisan inda ke miki ciwaba Unaisa, kara matse kunnen Unaisa Dada tayi tana bin kyakyawan fuskarta da kallo.
YOU ARE READING
BA LABARI
Любовные романыLabari ne akan akan wata yariya wadda take rayuwa ita daya, Bata mgn da kowa, akullum fuskarta rufe take da ni'kabi, ana sanin ita din farar mace ce kawai ta hanyar kafarta da gefen idon ta, kowa aka tambaya lbr akanta saidai yace maka ace ita din k...