BA LABARI PAGE 21- 22

258 18 0
                                    

BA LABARI
         By
    Fadila Lamido

EXQUISITE WRITER'S FORUM.

                   Page 21- 22

  Cikin dingishi yake tafiyan yayin da Suraj da Muftahu sukayi saurin kamashi, rikeshi sukayi yayin da Suraj yace, amman dai kasan yadda 'kafar nan take maka ko?, yanzun ne fa aka samu aka samu kanta, kuma ya bada sharadin ko kaji dama kada ka taka ta....

      Ganin Modibo yana kokarin d'ingisawa yasa su kara tareshi da saurin su, kowanne fuskar sa dauke da firgici, muftahu ne yai saurin zuwa ya dauko motar  yayin da Suraj ya taimaka masa har suka fito harabar gidan, Nan danan Suraj ya bude motar yayin da Modibo ya shiga gaba, Suraj ma zagawa yayi ya zauna a mazaunin driver shima Muftahu bayan motar ya zauna domin yanayin Modibo a yau ya basu Mamaki, bayan sun dauki hanya ma kowa da abin da yake sakawa cikin ransa, Modibo ma rufe idon sa yayi kawai tare da kwanciya jikin kujerar Motar.

     Sannu ahankali suke tafiya sabo da ruwan saman da ake shekawa, tafiyan minti 30 ta kaisu kofar gidan, ganin Modibo na kokarin sauka Suraj yace ka zauna bara na dubo ta, kafin Modibo yace wani abu Saraj ya hangi ta tana tahowa,  dan haka ya rike hannun Modibo yana fadin kaga gatacan ma tana tahowa.

      Acikin ruwan nan?, Modibo ya tambaya.

        Sauka Suraj yayi da saurin sa, ganin Suraj yasa ta tsaya cak tana kallon sa, saidai shi ko kada batajin tsoron sa domin ya jima yana zuwa gurin ta, kuma be taba matsa mata da karfi da yaji saita bude fuskarta ba Kamar yadda wadda suke Kira da sunan Modibo ke yi.

               Suraj ne tsaye agaban ta cikin tsareta da kallon yace, daga Ina kike?, Ido yabita dashi tsayon lakaci batace komai ba, ganin yayyafin da ake danyi a yanzun yana jika su yasa shi saurin fadin, " toh kizo ga Modibo yazo duba ki hakawai yana zaune ganin wannan ba'kin hadarin ya matsa sai yazo ya ga halain da kike ciki, kinsan meye tunanin sa?, ganin ba amsa zai samu ba yaci gaba da cewa, " be taba rayuwa cikin irin wannan gidajen naku ba, atunani sa be yadda da ingancin ginin ba, sannan kuma Yana ganin cewa ke kadai ce a cikin gidan dan haka yake tausaya miki, yau na tabbatar lallai Modibo na tsananin tausayin ki tunda ya fito a irin wannan lokacin, ni abun da nake so dake ki bashi hadin kai, ki zama karkashin kulwarsa, Ina me tabbatar miki zai kula dake fiya da tunanin ki domin yayi mun gani"

           Idan akwai abun da Unaisa tafi tsana a rayuwarta be wuce mgnr tabar dakin Innawuro ba, dan haka ma wannan lokacin ji take Kamar ta make Suraj, dan haka ta shiga tafiya kawai tana kokarin kasarawa gida.

   Bayanta Suraj ya biyo yana fadin toh kije Modibo na mota yana Kiran ki.

     Cak ta dakata tare da runtse Ido acikin zuciyarta tace, me ya dawo yi?, Ba tasowan hadarin nan ya wuce ba, nagaji da wannan zirga zirgar gaskiya.

       Ganin ta tsaya Suraj yace, Muji ko?

   Ba yadda ta iya dole ta fara takawa zuwa gurin motar su daya tal da sukazo da ita, domin tasan ko Bata tsaya va kota hadin yaye ne indai wancen motunin ne saya shiga gidan, Suraj ne ya nuna mata gefen da yake dan haka ta zagaya ta tsaya gaban kofar da gilashin sa yake rufe.

     Ahankali taga gilashin nayin kasa dan haka tai saurin yin kasa da kanta, ajikin ta taji kallon ta yake yayin da hakan yasa ta duk taji ta daburce.

         Daga Ina kie?

    Cikin dakarkiyar muryan sa yai mata wannan tambayan dan haka taji Muryan sa ta daki dodon kunnen ta, wannan karon ya dawo da takama, tafada azuciyar ta,  kafin ta dago idonta ta kalle shi.

      Ba kallona nace kiyi ba, kuma bana son shiru lallai yan Ina son kimin mgn, daga Ina keke cikin irin wannan yanayin kina awaje.

         Wasa ta fara da hannun ta dan haka yabita da Ido tsayon lokaci sannan yace, " Ina duka fa.

BA LABARIWhere stories live. Discover now