BA LABARI Page 9- 10

276 23 1
                                    

https://chat.whatsapp.com/BEUl8JVOPSiCNIsfscHdU4

BA LABARI
    By
Fadeela Lamido
   

EXQUISITE WRITER'S FORUM.

                  Page 9- 10

    Ba Magaji kadai ba duk wadda yaji Umarnin da Modibo ya bada saida ya zare Ido, ciki har makocin Unaisa, gaba daya ji yayi kafarsa takasa daukan sa, Ido ya zuba masa cikin tsananin Mamaki take kare masa kallo tare da son sanin waye wannan.

        Magaji kuwa cikin sauri ya koma cikin jerin motocin da suka taho dasu, ba jimawa saiga wasu maza biyu tika tika sun fito cikin motar, gidan suka nufa gadan kadan yayin da Magaji da Muftahu suke jinkina bayan su jikin daya daga cikin motoci 8 da sukazo dasu yau.

           Gidan sukabi da kallo, suna kallon yadda majiya karfi suke dukan kofar gidan, idon Magaji akofar gidan yake motsa leben sa tare da fadin, " Modibo ya nace lallai sai yayi mgn da yariyar nan"

         Shima Muftahu be kalli Magaji ba idonsa akan kurar dake tashi  dazaran sun daki kauren yace, "ni wannan ba matsalata bace, ni yanzun Babban burina mukoma gida nagaji da garin nan wlh, babu nishadi acikin sa.

        Tsaki Magaji yaja, naso in riga Modibo ganin fuskar yariyar nan.

      Me yasa?, Muftahu ya tambayi Magaji.

       Kafin ya bashi amsa Karan faduwan kofar gidan yasasu mikewa, duk suka nufi kofar, kusan a tare suka isa kofar gidan da Modibo, sandan karfen sa guda biyu yake takowa, manyan kayane ajikinsa farar shadda kal kafarsa daya cikin wani hadadden takalmi yayin da daya kafar aka nannade wandonta ya wuce guiwa kadan, can kasa kuwa nade yake da bandeji tundaga tafi har kusan guiwar sa.

         Da taimakon Magaji da Muftaho yahau Kan dakalin kofar gidan sannan sannan  ya shiga gaba Magaji da Muftahu suna binsa abaya.

         Siririyar hanyace duwa suka bi har suka isa dan tsakar gidan da ba wani girma gareshi ba, Sallama Modibo yayi har sau uku ganin babu amsa yasa kansa cike da kwarin guiwa.

           Tsananin rawa da jikinta ke yi yasata makalewa abakin kitchen tai tsaye, idonta akan kofar gidan, dan haka suna shigowa suka hada Ido, duk da cewa jikinta na matsancin rawa be hadata kuresu da Ido ba.

            Mutun biyu ne masu tsananin kama da juna, daya lafiyye daya kuma bashi da lafiyar kafa, farare tasss Basu da banbanci da larabawa yayin da na ukun beye kama dasu ba saidai shima akwai kama sosai

        Magaji ne yace, " idan baki cire bushashshun idon ki akan mu ba saina taka cikin yariya, au ke wai da kinajin kikai banza damu, kunga min yar iskar yariya tanaji tai banza damu fa.

      Modibo ne yace, " bana son hayaniya, bashi bane ya kawo mu.

      Amman Modibo yariyar iskancinta yayi yawa, ace tana yar musulmai amasa Sallama ya gagare ta?, dan kaniyar ki ki bude fuskarki Kona baki Kashi agurin.

      Lumshe ido Modibon yayi sannan ya sake bud'e su akan yariyar da gashin idonta ke sama da kasa, hada Ido sukayi yayin da yaga wani kyalli na tashi kwayar idon ta Kamar an diga zaiba, daker ya iya tattaro kalmar kanwata bude fuskar ki, inason inji matsalar ki wadda ya sa kika zabi zama ke daya.

     Ko motse batai ba, hakan ya fusa ta Muftahu da Magaji sosai sai dai Basu da ta cewa tunda Moddibbo na gurin dole sai abun da yace.

           Modibo ko kare mata kallo yayi tsayon lokaci sannan yace, Muftaho ku danne min ita ku cire min wannan abun da ta rufe fuskarta dashi.

BA LABARIWhere stories live. Discover now