BA LABARI Page 13- 14

265 22 0
                                    

BA LABARI
   By
Fadeela Lamido

https://youtu.be/YErlnJjLv_U

EXQUISITE WRITER'S FORUM.

                      Page  13-14

  Ahankali ya cikaba da takawa zuwa gareta, yayin da yake matasawa gareta yana hango yadda rawan jikinta ke dada tsanan ta.

     Itakuwa Unaisa jin Karan karfen  gigitata yake yi, dan haka tai saurin tura kanta tsakanin cinyan ta, sandan yazo gabanta kuwa jin kamshinsa take har cikin cikin ta.

     Tsaye yayi agaban ta, a hankali ya jingine karfen sa daya na gefen dake da lafiya tare da fadin, " menene ya same ki lokaci daya haka?

   Jimmm yayi yana son jin wani kalma daga gare ta, ganin tsayon lokaci hakan ya gagara yasa Modibo ya sake fadin, " ko na dame ki ne?"

        Nan ma shiru babu amsa, kallo ya gama kare mata sannan yace"

       Aunty! Na dameki in tafi?

           Ahankali ta dago kanta, tacikin ni'kab dinta ta kalleshi suka hada Ido, cikin sauri ta maida idon ta kasa.

        Waigawa yayi ya kalli gidan ko Ina da ina, ya mutsa fuska yayi sannan ya dauki karfen sa ya fara takawa, kitchen din ya leka sannan ya nufi makewayin dake gidan, tsaye yayi yana kare masa kallo tsaf yake babu wani datti ko alamar kazanta, bushe yake alamar an dade ba'a shiga ba, kofar ya saki ya dawo kusa da ita har yanxun tana nan yadda ya barta, kallo ya kare mata tsayon lokaci sannan ya nufi dakin ta, tsintan kansa yayi da tura kofar Yana daga tsaye fakin kofar, dakine irin na tsofi marasa karfi, babban gado da karamin gado gyare suke lukui, banda kamshin turaren wuta babu abun da dakin ke yi, komai na dakin kal, wannan ya tabbatar masa yariyar tana da tsafta, ahankali ya daga kafar sa ya shiga cikin dakin, wani hoto yagani guda biyu gefen filon  ahankali yasa hannun sa ya dauka, wata tsohuwa ce ta bayyana daganin ta bafulatana ce  saidai bakace bata da haske kwata kwata, bayan ya gama kare ma hoton kallo ya juya bayan sa, Innawuro yaga an rubuta cikin wani irin rubutu wadda Modibo ya bata lokaci wajen kallon sa, motsi yaji akofar dakin dan haka ya daga kansa ya kalli kofar yana jingine jikin babban gadon.

        Hango kafar ta yayi ta kasan labulen dan haka ya maida wannan hoton baya ya tsaya kallon daya, tsoho ne shima, saidai wannan yafi kama da bahaushe ba fulani ba, bakine shima wadda saboda tsofa har ya rankwafa, cikin sauri ya juya bayan hoton inda yaga anrubuta Baffana da irin wancen rubutun dai.

        Ido yasama hoton sosai Yana nazarin wasu abubuwa be ankaraba ya fara hangota hannunta rike da tsintsiyar laushi, tundaga kofar dakin ta dauko shara dan haka ya tsaya kawai ya zubawa sauratar Allah idanu.

        Sosai take shara, kuma har yanzun bata tare da nutsuwarta, duk da cewa babu wani datti adakin, kallonta kawai Modibo keyi yana dan shafa gemon sa a hankali.

      Duk dakin tabi ta share ko Ina, yayin da ta tsaya adaidai lokacin data kawo kurar gaban shi, ahankali ya sauke idonsa ya kalli kasa yana dan shafa gemun shi tare da Satan kallon ta, ganin ta dauki tsitsiyan tana Shirin cigaba da sharan yace, "  Aunty idan kika sake Kika daura tsintsiyar ki ajikina idan na tsinka miki mari saikin kwana biki farfado ba, duk wadda ya hadiye tabarya to kuwa zai kwana atsaye, izza na Kano, sarauta na Sakkwato, yaki na Zari'a, Karin magana na Bauchi, ba'a fini tsumma ba kar a badamin kwarkwata, idan kika fusatani abun bazai mana kyau ba.

      Lumshe idonta tayi, cikin ranta take fadin, wannan wanni irin mutum ne, sosai ta kule dashi har babu misali, banda kafin hali me yakaishi shigowa har daki, har yanzun tsintsiyar na hannunta takasa matsawa kuma har yanzun jikinta rawa gake, kamashin Modibo kuwa tuni ya bade dakin, ko kamshin nasa gigitata yake yi.

BA LABARIWhere stories live. Discover now