BA LABARI 5-6

305 22 9
                                    

BA LABARI
        By
  Fadeela Lamido

EXQUISITE WRITER'S FORUM.

                    Page 5- 6

Gaba daya motocin ne suka tashi lokaci guda, bayan ta suke bi a hankali, ita ko Unaisa ko waige batai, gudun ta kawai take tamkar wadda kura ya biyo ta.

      Layin nasu nada tsawo sosai, ga hanyar babu kyau dan haka sannu ahankali motar ke tafiya yayin da suke iya hangen yadda yariyar ke falla gudu a gaban su.

        Magaji ko ajiyan zuciya yake saukewa, ko ahaka yasan ya fanshe walar da taita bashi dan haka kallon mugunta ya ke ta binta dashi, shikuwa daya matashin ban da dariya babu abun da yake har yanxun, yayin da Modibo  ya hade fuska, idon sa akan ta, baya kawarwa zuwa can yaiwa driver Umarni daya tsaya domin wannan lokacin motar suce agaba.

       Dan  tsayawa sukayi kadan yariyar ta kara nisa sosai dasu sannan yace muje.

    Magaji ne yabi Modibo da kallo, cikin nutsuwar sa yaga Yana bin yariyar da kallo dan haka shima ya juya ya kalli yariyar da tayi nisa dasu sai arta gudu take, Modibo ya sake kallo yayin da yaga sai shafa gemon sa yake tare da shafo kansa, sunkuyar da kansa yayi yai murmushi sannan ya dago ya sake kallon Modibo yace, " Modibo!"

     Lumshe ido yayi sannan ya juyo ya kalle shi.

         Nace kodai mahaukaciya ce?

       Lumshe ido ya sake yi akaro na biyu tare da fadi ahankali, " lafiyarta lau"

      Ganin tasha kwana suka kara gudun motar, suna saka hancin motar akwanan sukaga ta shige wani gida ta rufo kofar.

                 ****

Matsanancin hakin da take yasa Dada rikecewa, kara shigewa cikin jikinta take tamkar zata shige cikin ta tare da haki babu kaukautawa.

        Unaisa menene??, gayamin me yake faruwa?

      Shid'ewa tayi gaba daya, yayin da Dada ta kara rudewa, girgizata take tare da Kiran sunanta, ganin babu alamar numfashi yasa ta zame ta, ruwa ta dauko aguje ta dawo ta shafa mata afuska sau uku sannan taji taja dogon numfashi, zama tayi sosai ta kara daurata jikinta tare da rungume ta sosai, tsayon lokaci tana rungume ajikin ta, ajiyan zuciya kawai take saukewa, saida Dada ta tabbatar ta samu nutsuwa sannan tace, " menene yake faruwa Unaisa, gayamin mene ya firgita ki har haka?

       Hawaye ta share tana manne ajikin Dada, Hankali tace, wannan ba'kin na Malam Baba ne suka tare min kofar shiga gida.

    Jimmm Dada tayi sannan tace, " akan wani dalili?"

     Bansani ba Dada, har biyoni suka yi da mota.

       Shiru Dada ta sake yi, sannan ta mike ta leka kofar gidan, bata jima ba ta dawo tana fadin, kindai tsorata ne Unaisa, amman babu wani daya biyo ki, mayafinta ta dauka ta sake fita, tsayon lokaci sannan ta dawo tana cewa, naje har layin naku babu kowa inajin sun wuce.

          Ajiyan zuciya Unaisa tayi mekyau sannan ta dauki nikaf dinta ta daura, itako Dada gaban murho ta isa tana kokarin daura girkin dare, yayin da hakan yayi daidai da shigowan wanni Dattijo, ganin Unaisa ya sashi yaja ya tsaya tunda nesa yana fadin, " tunda kin ajeta annan ni bari na koma"

     A'a Malam shigo mana, firgita tayi ne yau abun da bantaba ganin tayi ba, shiyasa hankalina ya tashi har ka ganta anan.

        Eh shiyasa zan baku waje ai, idan ta firgice dake lokacin zaki gane abun da ake gaya miki, nagaya miki batun yau ba bana son ganin Baharuwala acikin gida na, amman muje zuwa  duk wadda ya bari sauran tuwo ya Kona shi shiya so.

          Malam hakuri  zaka yi, abun duk da kaga ya koro bere ya fada wuta to yafi wutar zafi, ka tausayawa yariyar nan Malam, tana tsananin son kulawa.

BA LABARIWhere stories live. Discover now