BA LABARI 3-4

324 27 2
                                    

BA LABARI
    
    By
Fadeela Lamido

EXQUISITE WRITER'S FORUM.

                 PAGE 3- 4

Cikin sauri Magaji ya juya ya nufi kofar gidan adaidai lokacin da ta dauki ledan ta take kokarin shiga gidan, cikin kaukausar muryan sa yace , " ke!!"

     Babu alamar ta jisa yaga ta daga kafarta tashi gidan.

   Ina miki mgn kina tafiya?, ko kinason ki nunamin baki da  tarbiya ne kamar yadda yake azahiri, Ganin da yayi ta kule cikin gidan dole yasa shi yin shiru yayin da bakin ciki ya cika masa zuciya, kasa komawa yayi jin ana sawa gidan sakata.

      Daker ya iya juyawa ya koma  motar ya shiga ya zauna tare da kauda idon sa daga gefen da Moddibo ke zaune.

           Moddibbo ne ya kalle sa yace, " ta maka mgn?"

    Batare da Magaji ya kalli Modibo ba yace, " a'a, batace dani kala ba"

   Ka mata tsawa ne ko?

     Kawar da Ido Magaji ya sakeyin sannan yace a'a

     Jimmm Modibo ya sake yi sannan ya sake cewa, " ka koma ka buga gidan lallai ko wanni hali ake ciki yau Ina son in ganta anan.

   Batare da Modibo ya gama mgnr ba Magaji ya fita, babban rigar sa ya gyara tare da daidaita zaman hularsa sannan ya koma kofar gidan.

      Tun kafin tafara jin bugun kofar turaren sa ya fara mata sallama, zaune take bakin kitchen tana kokarin daura girki, cikin sauri ta mike, acikin ranta take fadin, mutanenan ne na ranar nan, me suke nema gurina, me yasa suke bibiya ta, gaba daya jikinta rawa ya fara tanajin yadda yake buga gidan, zuwa can taji shiru dan haka ta fara takawa ahankali ta isa zauren sannan tasa hannunta akan kofar tare da zura idonta ta kafar kofar.

       Wasu maza matasa ta hanga zaune bayan motar su biyu, fararene sosai wadda sukafi kama da larabawa, sai dai shaddace lafiyayya ajikin su babban riga wadda akayiwa ado da aiki irin na zamani, mutun biyu kawai take hanga wadda suke zaune cikin farar shadda, saidai ganin su take tamkar mutum daya ne saboda tsabar kamar da suka yi, mgn suke wadda  batajin me suke fadi, shagala tayi da kallon su bata Ankara ba saigani tayi motar ta wuce.

       Cikin gidan ta koma ta zauna, gaba daya ji tayi jikin ta ya mutu babu wani karfi jikinta, fuskar mutane nan guda biyu kawai take iya tunawa, cikin ranta take tunani, sudin suwaye?, daga Ina suke haka, kuma me suke son ce mata?

   Iri irin wannan tunanin taita yi har ya dauke ta dogon lokaci dan haka ta kasa girkin, tattara kayan tayi ta ajiye sannan tai alwala ta nufi daki.

              Gaba daya yau ta rasa sukunin ta, komai ne baya mata dadi, fuska iri daya guda biyu sun tsaya mata axuciya, rasa abun yi yasata fara zubar da hawaye Koda dare yayi daker bacci ya iya daukan ta, cikin ikon Allah washegari ta tashi da sauki, duk aikace aikacen gidan tayi sannan tayi abun karyawa ta kwanta, kasancewar yau juma'a babu islamiya, baccin da bata samu jiya ba shi tayi wannan lokacin.

          Misalin daya ta shi, Nan ma sallah tayi sannan ta zauna tsakar gida, yau daya ta farajin zaman gidan ya dame ta, sosai take sha'awar tayi hira kamar yadda takejin mutane nayi, saidai tana tuna gargadin Innawuro.

         Washegari ta kama asabar dan haka ta nufi islamiya domin shikadai ke debe mata kewa tun bayan data kammala secondry school bata dawowa sai yamma liss, wannan ya matar da ita tunanin data fara sawa ranta akan samarin guda biyu.

                 *****

Yauta kama alhamis dan haka tun safe take dakon zuwan Dada amman ba ita tazo ba sai misalin biyu da rabi taji ana buga gidan tare da fadin, Unaisa taho bude min.

BA LABARIWhere stories live. Discover now