Alhamdulillah wassalatu wassalamu ala rasulullah sallallahi alaihi wasallam. Godiya marar misaltuwa ga ubangijina ubangijin talikai baki ɗaya wanda cikin rahamar sa ya bani ikon kammala farkon wannan littafi mai suna "bin dokar Allah ba ƙauyanci bane" kuma gashi cikin ikonsa da ƙaddarawarsa ya bani ikon cigaba da littafi na biyu mai suna "ingantaccen kishi".
Salati marar adadi ga masoyinmu mai ƙaunarmu, da tausayinmu mai tsananin kwaɗayin rahama a garemu fiyayyen halitta manzon rahama sallallahu alaihi wa sallam.
Ina mai miƙa godiya ta musamman ga iyaye na tareda fatan rahama garesu.
Jinjina gareku masu bibiyan rubutuna batare da gajiyawa ba, ina miƙa godiya ga wa 'yanda suka ƙaramun ƙwarin guiwa ta hanyar addu'o in ku dakuma ƙoƙarin gyara a duk sanda suka ga kuskure a cikin rubuna.
Godiya da fatan alkairi ga mai gidana da kulawarsa gareni tsawon lokacin da muka ɗauka tare, babu shakka ya cancanci yabo na dukkan ɗawainiyar ciyarwa, tufatarwa, dakuma kula da dukkan buƙatun gida da yara ina fatan Allah yasa yafi haka amin.Bazan manta da kaina ba a cikin addu'a ina fatan Allah yasa duk abunda zan faɗa nafaɗi alkairi kuma yazamu abunda zai amfaneni ya amfani al'uma baki ɗaya sannan ina roƙon Allah da ya tsarkakemun niyyata akan dukkan ayyukana amin.
Dukkan nin labari na karantashi kyuata ce ba sai anbiya ba, amma ga masu san taimkamun da gudumawarsu kuna iya turamin ta...
0091869462 fatima abubakar saje access bank...
YOU ARE READING
INGANTACCEN KISHI
General FictionCigaban labarin bin dokar Allah ba ƙauyanci bane. Sannan kamar yadda sunan ya nuna zan fi maida akalan rubutun akan nau'o in kishi, dalilan da yasa ake kishi, banbanci tsakanin kishi da hassada. Ina fatan zaku kasance tare da ni. Kada ayi amfani da...