Chapter 2

19 0 0
                                    

.... Salma da safiya sunsha ado kamar yadda ake tsammanin ko wace amarya ta kasance. Safiya ce tayi murmushi sannan tace salma yaude burinki ya cika kin aure mun miji a ranar aure na da ace a baya za'a bani wannan labarin da tabbas zan ƙaryata.
Hm" safiya kenan "inji salma. Wato ke dai ba ƙya sarewa to amma ni a ganina ai kanki ya kamata ki tuhuma ba ni ba dan haka ki iya bakinki. Safiya tace shikkenan amma bansan ya zakiyi da amarcin yau ba, in da zaki bi shawara ta da kin koma ɗakin ki tinkafin mijina ya dawo. Safiya ta fara tinzira salma amma sai ta kwantar da hankalinta tace wai dan Allah safiya ba kya gajiya ne dan ni yau bazan iya biye miki ba nagaji sosai, safiya tace shiyasa nace kije ki kwanta amma kinƙi sannan kuma bana tinanin zaki ji daɗin zama a parlour tare da mu sabida baki damu da cin kaza ba sannan bakya san fura da nono abunda kika fi ƙi kuma shine zuma harma baƙya iya zama a inda ake shansa, ni da yaya kamal kuma muna san zuma sosai shiyasa nake faɗa miki cewar nafi dacewa da shi. Salma tace shikkenan kijira dawowan mijinnawa tukun. Rufe bakin salma keda wuya sai ga kamal ya shigo ɗauke da manyan laida guda biyu cike da kayan ƙwalam da maƙulashe na abubuwanda safiya ta lissafa harma fiye da haka. Amare kunsha ƙamshi in ji kamal..
Alhamdulillah"
Allah na gode maka"
In kunnu Allah"
Thank you Allah"
Miyatti Allah...
To fa farin cikin kamal bazai misaltuba shi kansa bai san sau nawa yayi sujudush-shukur ba da ga sanda aka ɗaura auran zuwa yanzu. Salma da safiya sukace wannan wani yare ne kuma "in kunnu Allah"? Kamal ysce yaren bolanci kenan, sukace to shikuma a ina ka koya? Yace a gurin abokina khalifa. To amma yanzu dai muje muyi alwala muyi sallah muyi wa Allah godiya. Hakan ko akayi bayan sunyi sallah sai kamal yace to ga ɗan abun taɓawa barin ɗauko tea flax da teacup dan nasan akwai dangin shayi a gurin...
Sukai murmushi sukace ai harda kai! Bayan an baje kayan abinci safiya na jiran tashin salma sai kawai taga Salma ta ɗauko zuma ta zuba cikin tea ta garwaya tana sha jim kaɗan kamal ya ɓantaro wani sashi mai taushi daga jikin kaza ya sa musu a baki sannan yace ga fresh milk da damun fura da nono salma tace to zan sha madara amma damu zan ajiye sai gobe in Allah ya kaimu. Kamal yace safiya ke fa? Cikin nauyin baki tace eh nima haka sai kamal ya tashi ya nufi kitchen dan yaje ya ajiye...
Bayan ya tashi sai salma tacewa safiya kinyi mamaki ko? Safiya tace yaushe kika koyi shan zuma? Salma tayi murmushi sannan tace safiya kenna ita soyayya bada baki kaɗai akeyinta ba, tin daga randa husby yacemun yana so nafara shan tea da zuma tin ina sha ina dawo dashi harna saba dan haka yanzu sai murnarki ta koma ciki😜.
Bayan kamal ya dawo gurinsu sai duk suka ce sun ƙoshi haka aka tattare guri aka gyara aka ajiye sauran abincin a in da ya dace. Jim kaɗan suka dawo suka zauna sai kamal yace to yanzu ya zamu raba kwana?
Dukkansu sukai shiru ba wacce ta amsa sai yayi murmushi yace to shikkenan ina ganin bari muyi wasan ɓuya wacce aka fara samu to kwananta ne fari, sai suka ce a'a, mai zai hana abi girma kawai inji salma tinda safiya ta fini da shekara ɗaya sai ta ɗau girma tayi haƙuri, nan fa safiya tace sam ai wajen miji ba'a girma inko hakane ai ke salma kece ya kamata ki haƙura tinda badan keba da yanzu ni kaɗaice tareda shi😏
Salma tace shikkenan gara kowacce ta rubuta sunanta sai ta naɗe sai a zuba a gabanka kai kuma ka rufe ido ka zaɓa guda daya wacece aka ɗau sunanta ita ce da kwanan fari.
Hakan ko akayi amma wani abun mamaki shine bayan kamal ya buɗe takaddar daya ɗauko sai yaga sunan salma amma da yanayin rubutun safiya sai abun ya ɗan kullemar kai🤔
Sai ya kalli safiya bayan sun haɗa ido sai yaga tamar alaman itace tayi hakan, salma kuwa sai farin ciki take a ganinta tayi nasara.
Kamal ya sunkuyar da kanshi ya faɗa a zuciyarsa har tsawon wani lokaci zaki riƙa danne kanki saboda salma safiya?
Nagode ya faɗawa safiya haka. Meye na mata godiya bayan ba wani sadaukarwa tayi ba.... Sai duk sukai murmushi sannan sukai wa juna sallama safiya ta koma ɓangarenta. Harta kwanta sai taji kamal na buga mata ƙofa bayan ta buɗe sai tace lafiya kuwa ina salma? Sa yace lafiya lau salma tana bayi.
aiko ni akai wajenki, sai tace ni kuma waye to...😳
Kamal yace zuciyata ce ta aiko ni da saƙon tukuicin abun da kikai na bajinta cikin kunya ta sunkui da kanta tayi murmushi. Kamak ya ɗago kanta ya sumbace ta a kuncinta sannan yace ina sanki matata ki kula da kanki sai da safe...
Safiya tace to nagode sai da safe.

INGANTACCEN KISHIWhere stories live. Discover now