Chapter 5

16 1 0
                                    

(Gidan hajiya Aisha)
Da hanzari hajiya aisha ta buɗe kofar parlour ta, hajiya samira ce tsaye na dakon a buɗe mata. Maraba lale sannu da zuwa "inji hajiya aisha" bayan sun zauna sai hajiya aisha ta kawo wa baƙuwarta laimo mai sanyaya maƙoshi hajiya samira ta karɓa tayi godiya. Ina yaran suke? Inji hajiya samira" hajiya aisha tace sun tafi hadda amma yanzu zasu dawo in sha Allahu, hajiya samira tayi murmushi sannan yace masha Allah yayi kyau. Wato hajiya aisha na zo ne musamman dan nai miki godiya akan tsayawa da ki kai wajen ganin komai na bikin kamal ya tafi yanda ya kamata hasalima musamman kika bar gidanki kika koma can gidana muka zauna tare akai komai yanda ya dace gaskiya ba abunda zance sai godiya kuma Allah ya barmu tare. Sai kuma abu na biyu wannan kyautar takice nasan kinasan abun hannu sosai (bangles) da kuma lass na siya mana tare amma kuma nayi karambani dan na ɗinka miki ba tare da izininki ba, sannan ga wannan na yara ne. Sai kuma abu na uku ga wannan kuɗin gudumawa ne dana samu daga gurin mutane shine na raba na kawo miki naki.
Masha Allah lallai hajiya samira ta canza kamar ba ita ba" maganar zuci kenan da hajiya aisha keyi sannan daga bisani tace to na farko dai bakida buƙatan yimin godiya akan auren kamal saboda ai ɗana ne dan haka abu ne daya kamata nayi. Abu na biyu kuma bakya buƙatan neman izini na dan min abunda ya dace dan haka nagode sosai nayi matuƙar farin ciki Allah ya ƙara buɗi. Gameda kuɗin nan kuwa kiyi hakuri amma bazan iya karɓa ba dan nima daga ɓangare na nasamu gudumawa daga gurim 'yan uwa da abokan arziki dan haka kibar kuɗinki nagode sosai.
Hajiya samira tace to shikkenan bazan ja dakeba dan nasan ku ko a kotu sai anyi da gaske ake kada ku😁
Hajiya aisha tayi murmushi tace ke dai ba kya rabo da zolaya, amma dai wuni zamuyi ko? Hajiya samira tace a'a banzo dan wuni ba yanzuma tafiya zanyi nida nazo babu appointment ai bai kamata na wuni ba hajiya aisha tace ke da gidan ki ai ba sai an san da zuwanki ba you are always welcome kada ki damu. Kuma albishirin ki...
Hajiya samira tace goro fari kyal, yau miyar zogale zanyi da tuwon shinkafa dan haka ko dan shi bai kamata ki koma gida ba sai kin jira munci abincin dare "inji hajiya aisha". Hajiya samira tace masha Allah gaskiya banga ta tafiya ba ina nan har dare in sha Allah kinga sai muje kitchen ɗin tare muna aiki kina bani labarin cases naji na dariya, takaici da ban haushi. Hajiya aisha tace ai ko zakisha labari dan ko yanzu wani case ne aka kai kotu na wasu ma'aurata ita matar tana aikinta tana da abun hannu amma ta jima ba tai aure ba kuma kinsan mata da sunkai wasu shekaru ba aure sai su shiga damuwa su mance shi aure da arziki lokaci ne in Allah ya kawo lokacinyi babu mai hanawa kuma auren wuri ba shine aure ba auren wanda ya dace shine ake kira aure. Kwatsam sai ta haɗu da wani saurayi tace tana sonsa harma sukai aure bayan shekara suka samu rabo a tsakani to ammafa ba ta da kwanciyar hankali yau ƙarya gobe zagi fitinar yau daban na gobe daban a ƙarshe ma guduwa yayi ya barta da goyon har sai da tayi ƙararsa a kotu aka nemo shi. Hajiya samira tace ikon Allah kenan ana zaman aure a ƙasar hausa...
Hmm gaskiya kam "inji hajiya aisha" bayan an kawo shi gaban alƙali sai yace shifa gaskiya dama tin farko auren dole tayi mar dan kafin auren ma sai da ya gudu amma ta nemo shi dan haka kawai a raba auren shi bazai iya ɗaukan nauyinsu ba😅 kuma abunda bai sani ba shine ko an raba auren sai an yake masa abunda zai riƙa bayarwa na ɗawainiyar ɗansa, ita kuma matar ta fara kuka wai dan Allah kar araba tana son mijinta😅
Hajiya samira tace ikon Allah kenan wato wani lokacin soyayya ba zuciya kaɗai yake narkarwaba harda ƙwaƙwalwa😂

INGANTACCEN KISHIWhere stories live. Discover now