Chapter 15

18 2 2
                                    

The final charpter....

INGANTACCEN KISHI
NA
FATIMA SAJE (UMMUAMNA)


(Shirin daga taurarinmu karo na biyu
Tate da Malam Abdullahi Baƙoji Adamu a gidan talabijin na sunnatv.)

....O
Bayan mai gabatarwa ya yi sallama tare da gabatar da shirinsa a karon farko sai yakara da gabatar da baƙinsa na wannan makon, Shin wasu baƙi ne za'a karɓi baƙwancin su a yau? Amsar da masu kallo sukai ƙihuu a gaban talabajin suke jira su ji.

Hajiya Safiya Abdullahi Goni tare da amaryar su wato Amatullah Haidar ne suka samu damar amsa goron gayyatar da akai musu a wannan makon. Lalle yau wannan shirin zai kayatar da masu kallo da kuma saurare.

Bayan baƙin sun bada taƙaitaccen tarihinsu kamar yadda al'adan shirin ya saba, mai gabatarwa ya buƙaci Hajiya Safiya da ta ɗan yi tsokaci game da ma'anar KISHI a taƙaice, ga bayananta kamar haka...

"Bismillahir-rahmanir-rahim, gaskiya na ji daɗin wannan tambaya da Malam Abdullahi ya yi dangane da sanin ma'anar kishi a rayuwarmu. Kishi dai abune mai kyau kuma halal duba ga Allah da kansa yana kishin a haɗa shi da wani wajen bauta kuma ai daman ko a hankalce babu wani abu a faɗin duniya da ya can-canci a bauta masa in ba Allah ba, ko da kuwa mala'ika ne ko annabi ballantana wani mutum ko dutse ko gungi da duk wani abu da ake bauta wa.

Sannan idan muka duba tarihin zamantakewa tsakanin ma'aiki da iyalensa akwai ƙauna, soyayya, tausayi da kuma kishi; kazalika tsakanin sahabbai da matayensu.

Haka in muka duba iyayenmu zamuga irin kulawa da suke wajen killace iyalensu da 'ya'yansu ƙarƙashin inuwar kulawa da bibiyan dukkanin lamuransu, mai suke yi a gida, ina suke zuwa, mai suke yi a waje, dawa suke hulɗa, su waye ƙawayensu da abokansu, wace sana'a suke yi, su waye suke neman auren 'ya'yansu mata ba irin wannan zamanin ba da zaka ga yarinya budurwa tana soyayya da saurayi shekara biyu ko uku mahaifinta ko mahaifiyarta basu sani ba.

Sai kuma asalin kishi wanda muke magana akai ma'ana kishi tsakanin abokan zama ko nace tsakanin mata biyu, uku, ko huɗu da suke ƙarƙashin kulawar namiji guda ɗaya.

Wato a gaskiya kishi abune na ɗabi'a wanda Allah ya haliccemu da shi kamar yadda ya haliccemu da jin yunwa, ƙishi, barci da kuma sha'awa; sai dai a dukkanninsu kowani mutum ko nace ko wace mace da yadda take jin zafin kishinta.

Sannan shima wannan kishin yanada rassa kamar haka...

Akwai kishin da ƙauna da soyayya ke sawa, wannan shine sanannen kishi da ake samu tsakanin masoya da ma'aurata; domin ɗabi'ar ɗan adam baya san wani ya raaɓi abunda ya ke so koda shi bai kai ga mallakar wannan abun ba.

Sai kuma kishin da gasa ke sawa ayi, misalin idan mace na gasa da 'yar uwarta a duk abunda ya shafi rayuwa misali karatu, ko fasaha to tana kishin waccan tayi masara akanta.

Akwai kishin da hassada ke sawa, shine mace taga abokiyar zamanta, ta fita abun duniya misali 'yar gidan sarauta ce ko tana da dukiya ko wata ni'ima da Allah ya bata.

Akwai kuma kishi tsakanin matan yaya da ƙani, ana kiransa da kishiyar balbali. Wannan yakan tsananta idan sun kasance a gida ɗaya kuma ƙanin ya fi yayan nashi kuɗi ko dukiya.

Sai kishin da ƙiyayya da mugunta ke sawa ayi, misali mace tana zaune da miji amma bata sansa kuma tana gana mai azaba sannan kuma bazata bari ya auri wata ba dan kar ya samu nutsuwa.
Ko kuma an tabbatar bata haihuwa sai kuma taƙi yadda ya kara aure dan kar ya samu zuriya alhalin ita bata da shi kuma zata iya yin komai dan kar ayi auren ko salwantar da amarya bayan auren harma da yaranda amaryar zata haifa, ko ta hanyar tsafi ko kuma kisa ta hanyoyi daban-daban.

INGANTACCEN KISHIWhere stories live. Discover now