Chapter 3

17 1 0
                                    

(Gidansu zubaida)
... Cikin sanyin jiki zubaida ta buɗe ƙofar ɗakin mahaifiyarta sannan tayi sallama, bayan inna ta amsa sallamar sai ta dubi zubaida tace mai ya kawo ki gurina? Wannan shine tambayar da yake fitowa daga bakin inna a duk sanda zubaida ta kusanci inda take. Inna nazo ne muyi magana cikin alamun kuka ta faɗa sannan ta naimi guri ta zauna. Babu wani abunda ya rage wanda banjiba daga bakin maƙwabta, dangi, da kuma sauran mutanen gari sannan babu abinda ya rage wanda ban gani ba tin da gashi ina rayuwa tareda ke da kuma jikata a cikin gidan nan duk da cewar ban aurar dake ba. Zaazzafar hawaye ne suka fara zuba daga idanun zubaida sannan ta koma kan guiwowinta tare da haɗe hannayenta guda biyu gaban mahaifiyarta tace inna dan Allah ki saurareni ki taimakeni kibani daman nayi magana wannan shirun naki yafi dukkan wani hukunci raɗaɗi da ƙuna inna, shekara guda kenan ina ta binki dan ki bani dama na faɗa miki abunda ya faru da ni amma kinƙi kullum ji nake kamar akan garwashin wuta nake dan Allah ki saurareni inna!
Ajiyar zuciya inna tayi tace zubaida nice nake cikin raɗaɗi domin ke ai abunda kika nema shi kika samu, niko ba abunda na nema ba kenan amma gashi dolena na karɓa. Kasancewata mace a gidanmu mahaifina bai sani a makaranta ba fahimtarsa shine mace bata dace da boko ba, ina ji ina gani aka hanani karatu duk da ina so. Bayan nayi aure na fara haihuwa sai na ƙuduri niyyan tsayawa tsayin daka ga karatun yara na har sai na cika burina na karatu akan yara na amma sai gashi kin watsa mun ƙasa a ido a maimakon kiyi ilimi mai amfani sai kika ɓata rayuwarki da san abun duniya kika biyewa mummunar huɗuba irin ta mahaifinki wanda a sanadin baƙin cikin hakan yasa nake girban abunda bani na shuka ba. Kaiconki zubaida haƙiƙa kin cutaddani, kin cuci kanki kuma kin cuci wannan yarinyar samha!
Cikin tsakanin kuka da tashin hankali zubaida tace nashiga uku inna dan Allah kiyi hakuri ki yafe mun, haƙiƙa na zalunci kaina na biyewa ruɗin kyau da dogon buri da kuma kwaɗayin abun hannun mutane yanzu gashi hakan ya sani cikin nadama. Tabbas ba wanda zaici amanar iyaye ya zauna lafiya, naci amanarki inna nayi watsi da tarbiyarki, nasiharki, jan kunnenki, dakuma soyayyarki agareni. Nasan banida kalamanda da zanyi amfani dasu wajen sanyaya zuciyarki amma inna kisani ban taɓa bada kaina ga wani ɗa namiji ba sannan ban taɓa keɓewa da wani ba haka kuma ban taɓa aikata zina ba.
cikin fushi inna tace to idan bakiyiba a randa kikasha cikin kenan!?
Ranan da abun ya faru na miki ƙarya kamar yadda na saba sai na tafi wajen birthy party na ƙawata zillaziyya, bayan munje gurin an kawo mana abun ci da sha, muka ci kuma muka sha ni da sauran ƙawayena. Bayan kaman minti ashirin ko talatin sai na fara jin jiri sai na tashi na fito waje dan na dawo gida amma sai na faɗi, kwatsam sai naga wani ya tsaya a kaina amma bana iya kallonsa sosai inaji ya ɗaukeni ya sani a mota daga nan ban sake tina komai ba sai kawai farkawa nayi na ganni a wani kufai (yasashen guri da aka manta dashi) bayan hankali ya dawo jikina saina sa ihu mai tsanani amma ba wanda ya jini haka naita kuka bayan wani lokaci sai na tashi da ƙyar dan na dawo gida sai naga kuɗi naira dubu ɗari biyar da saƙon wasiƙar nan.... Kafin zubaida ta ƙara cewa komai sai inna tayi wuf ta karɓi wasiƙan daga hanunta, bayan ta buɗe sai ta fara karantawa kamar haka....
" Alhamdulillah itace kalmarda duk wanda ya samu nasara yake furtawa, yau ina cikin farin cikin yin nasarar buɗe hajar da kafinni ba wanda ya taɓa nasarar buɗe ta.... Ga wannan kuɗin ki kai kanki asibiti kuma ki kula da kanki. Nagode miki domin kuwa kin zama sanadin arzikina dan kuwa nayi nasarar lashe gasar miliyan biyar da wani yasa akan ki dan haka kema ga naki. Kada kiga laifina dan ke kika jawa kanki. Ki huta lafiya."
Inna ta kasa cewa komai sai zazzafar sheshsheƙar kuka da takeyi na ɓaƙin ciki da tsananin takaici abunda ta karant a wasiƙar. Zubaida na gefe tace inna wannan shine sakamakona na irin cutar dake da nayi sannan kuma da ƙin jin maganarki bugu da ƙari nayi watsi da koyarwan addini na, na manta da cewar addinin musulunci shine gatan duk wata mace a duniya kuma musulunci shine 'yancin ta...

INGANTACCEN KISHIWhere stories live. Discover now