Chapter 7

20 1 0
                                    

(Gidan kamal)

Lafiya safiya na ganki rai a ɓace haka ina hubbin yake? Safiya tace salma lafiya lau shi kuma na baro shi a asibi amma zai dawo anjima, salma tace to amma mai yasa baki jira shi ba kuma gashi naga yanayinki kamar akwai matsala idan bazaki iya faɗawa kishiyarki ba to ki faɗamun a matsayin ƙawarki mai yake faruwa dan Allah? Safiya ta ɗan numfasa tace na faɗamiki ba komai kawai ji nake raina yana ɓaci may be gajiya ne. Zanje ɗaki na huta idan ya dawo kice kada ya tasheni karma yazo inda nake.
Kafin salma tace wani abu safiya ta juya tayi tafiyarta, salma tace tabbas akwai abunda ke faruwa da safiya dan cikin satin nan duk ta canza kuma ta koyi masifa.
Bayan shuɗewar daƙiƙa goma sha biyar da dawowar safiya sai ga kamal ya shigo gida, in da shigarsa keda wuya ya tadda salma na zaman dakon sa. Bayan tayi masa tarba irin wacce ta saba sai yace ina safiya fa dan nace ta jira ni mu dawo tare amma ban gantaba kuma na kira wayan bata ɗauka ba har saida na tambayi sister maryam tace mun ai ta ganta tana shiga napep so shiyasa na dawo gida dan nasan bazata wuce wani gurinba...
Salma tace hakane ta dawo tana ɗaki, tacemin ta gaji zata huta kuma inka dawo na faɗa maka kada ka je ɗakin dan zatai bacci. Kamal yace ikon Allah to amma mai yake faruwa da safiya ne naga kamar bata cikin walwala kwanan nan? Salma ta ɗan numfasa tace na tambayeta amma batace komai ba sai kawai na barta dan kar na matsa mata amma idan ta tashi sai kaje ka sameta kuyi magana, kamal yace in sha Allahu. Ya batun result din da kika karɓo tinda kinƙi faɗamun a waya kince sai nadawo gida? Salma tayi murmushi sannan tace zo muje in nuna maka wani abu kamal yace to my dear muje. Bayan sun shiga ɗaki sai salma ta nuna masa wasu kaya data siyo tace buɗe ka gani, yana buɗewa sai yaga kayan wasan yara ne a cikin ledan kamal yace kyauta zakiyi da su ne? Salma tace eh wannan shine kyauta ta farko da zanbawa babynka a matsayina na uwa...
Kamal yayi shiru na ɗan lokaci sannan ya juyo da sauri ya rungume matarsa cikin tsananin murna da farin ciki sannan yace Alhamdulillah Allah na gode maka bisa dukkan ni'imar ka salma kice kin kusa zama uwa ni kuma uba kai Alhamdulillah 😁😀 gaskiya naji daɗi sosai dajin haka dan Allah ki kulamun da kanki sosai kinji ko banda yawan aiki, ɗaukan abu mai nauyi, tsalle, da kuma sauri ki riƙa samun hutu kuma gobe in sha Allahu zan sa aka muku masu aiki sannan kuma ni da kaina zan na kama hannunki a hankali muna tafiya sannan kuma... Kafin ya ƙara salma tace yallabai ɗan dakata lafiya ta ƙalau fa sannan cikin sati huɗu ne kawai dan haka ba buƙatan sai ka kama hanuna in zanyi tafiya kabari sai ya girma tukun. Kamal yace to shikkenan ai duk abunda kikace haka za'ayi yanzu faɗamun me kike so na kawo miki? Salma tace ba komai ai duk abunda nake jin ina so akwai shi a gidannan tinda ga kanan kai ne masoyina, abun alfahari na farin cikin zuciyata kuma walwalar fuskata ina sanka mijina kuma ina fatan na kasance tare da kai har a gidan Aljanna tare da iyaye, 'yan uwa da yaran mu da sauran muminai. Kamal yayi murmushi sannan yace bana gajiya da jin muryarki koda abu ɗaya zaki ta maimaitawa sannan bana gajiya da ganin wannan kyakkyawan fuskar mai ɗauke da murmushin sanyaya zuciya idan kina kusa dani sai naji zuciyata ta ƙara matsowa gareki idan kuma nayi nesa da ke sai naji zuciyata ta bar jikina ta dawo gareki duk abunda nake kina nan cikin tinanina, Allah ya amsa addu'ar ki milky na kuma ya barmu tare ina kaunarki💞milky na maman baby Allah ya ƙara muku lafiya kuma yasa ki haihu lafiya yanzu abunda zanyi shine zanyi wanka naci abinci sai naje na kaiwa mama labari dan masan zatayi murna sosai. Salma tace haba yaya kamal ko kunya babu ni gaskiya karka faɗa kawai ka bari in ya girma ai za'a gani, kamal yace to ai bazan iya riƙewa ba amma dai shikkenan bazan miki alkawari ba in na faɗa kada kiga laifi na in kuma ban faɗaba to kinyi nasara.
Amma dan Allah ki dubamun safiya anjima kuma kiyi ƙoƙari ta ci abinci dan naga kamar bataci abinci ba yau kuma in na fita zan tafo maku da ɗan abun taɓawa in sha Allahu. Salma tace to ba komai yanzu dai muje kayi abunda zakai tukun baban wa zance? Kamal yace kice baban faɗima (abu faɗima) in sha Allahu salma tace to Allah yasa faɗimar ce....👨‍👩‍👧
Kamal yace amin ya hayyu ya qayyum.

INGANTACCEN KISHIWhere stories live. Discover now