.....Tunda Safiya ta haihu take tambayan labarin Salma, "shin ya Salma take?" Kamal ne ya shigo gurinta jiki a sanyaye ya faɗa mata duk abunda ya faru; hankalin Safiya ya tashi matuƙa sannan daga bisani ta naimi wata alfarma a gurin mijinta.
Shin wata alfarma ce wannan?
Safiya ta dubi mijinta da ke riƙeda karamar baby tace masa "haihuwa akwai wahala har sai da nayi tsammanin bazan rayu ba; amma bayan na haihu aka nuna mun abunda na samu take sai naji hankali na ya kwanta idanuna sukai sanyi zuciyata ta cika da farin ciki da kuma tsananin yiwa Allah godiya da kyautar da ya min wanda babu mai yin irinta inba shi ba.
Kamal yace "tabbas wannan haka yake mata ta, ni kaina Allah ne kaɗai ya san irin farin cikin da nake ciki; Alhamdulillah".
Safiya ta ɗan tashi ta zauna sannan ta dafa hannun mijinta tace masa "ka taimakeni, kai min alfarman na bawa aminiyata kuma matarka ɗaya daga cikin kyautar da Allah ya bani; domin ina so itama taji irin farin cikin da nake ciki a yanzu."
Ƙura mata ido Kamal yayi yana kallonta kuma yana tinanin shin yaji abunda Safiya ta faɗa daidai kuwa!?
Shirunda kamal yayi yasa Safiya ta ƙara da cewa "wallahi bazan iya samun cikakken nitsuwa da farin ciki ba matuƙar Salma tana cikin damuwa yaya Kamal; dan Allah kada kace mun a'a!"
........()
A hankali kamal ya buɗe ƙofar ɗakin salma yana sanɗa kamar an ɗaura masa kwai a ka, "na fa ganka so garama ka saki jiki kawai"Salma ta faɗa.
kamal yace "ai ban so kika tashi ba, anty maimuna tace mun kinyi bacci shi yasa na shiga a hanakali kar na tashe ki; dama ina so muyi magana ne amma ban san ko zaki iya jure surutu na ba?""Hm, kai ko! Zauna kusa da ni amma fa tausar ƙafa zakai mun dan har yau ciwo ya keyi" kamal yace "Allah sarki! Sannu milky nah, Amma dai Alhamdulillah naga kumburin yana raguwa" "Hakane kam, shiyasa yake zafi kuma nake ji kamar ana matse mun kafar gashi duk yayi baƙi"
"Allah ya ƙara lafiya amin.
Jibi suna amma har yau baki bani amsar tambaya ta ba, shin su nan wa ki ke so a saka wa babyn mu?"
Salma da ɗan kishingiɗa san nan tace "Idan ka amince ina so na ka sa mata sunan mahaifiyar Safiya na san za taji daɗi sosai kuma zai rage mata raɗaɗin rashin ɗayan babyn ta da tayi"
"Allah mai iko!" Kamal ya faɗa cikin tsa nanin mamakin jin abunda ke fita daga bakin Salma wanda babu shakka maganarta akwai matuƙar ƙauna ga Safiyya; abunda Salma bata sani ba shine ɗanda aka nuna mata a matsayin ɗan Safiya wanda ya koma ga Allah to ɗan tane.
Bayan Safiya ta naimi alfarma a gurin mjinta, Kamal ya amince da ƙudurinta cikin sauƙi kuma ya nuna farin cikinsa tare da nuna matuƙar godiya ga Safiya.
Duk 'yan uwansu da ke asibitin Kamal yasa aka kirasu dan ya faɗa musu abunda suka shawarta da Safiya, nan take aka canza baby boy ɗin salma da baby girl ɗin Safiya.Jim kaɗan Salma ta farka daga dogon barcin da tayi, bayan ta buƙaci ganin baby sai aka ɗauko mata baby girl ɗin aka bata. Bayan ta tambayi Safiya sai aka ce mata ai Safiya ta haifi mace da ma miji amma baby boy ɗin ya koma. Nan take zuciyarta ta cika da tausayin aminiyarta matuƙa! Hajiya Samira ta ɗauko baby boy ɗin ta miƙawa salma ta ganshi; kekkewan baby da shi masha Allah.
Salma ta shafa kan shi ta masa adda'a sannan ta aika saƙon gaisuwa ga Safiya. Tsa kanin uwa da ɗa sai Allah, kallo ɗaya Salma tayiwa baby boy ɗin taji shi tamkar wani tsoka na jikinta.
Tambayar da Kamal ya yiwa Salma game da suna, haka ya yiwa Safiya. wani abun mamaki shi ne itama safiyar amsar da ta ba shi shine asa wa babayn ta sunan mahaifiyar Salma.
.....()
Alhamdulillah, an yi suna lafiya baƙi duk sun koma gidajensu. Sai Yafendo da Hajiya Karima da anty Maimuna sai maman 'yan biyu da ke zuwa ta duba su ta kuma sai kum 'yan aikin su, sune suka rage masu taimakawa Safiya da Salma.
Yafendo ƙanwar mahaifiyar Safiya ce, kuma sun haɗa kaka na gurin uba da Hajiya Samira; tun kafin suna Safiya ta wartsake amma Salma tana buƙatan kulawa ta musamman saboda aikin da akai mata.
Kamal ya kasance mai tsanani kula ga matansa, ga so da ƙauna da yake nuna musu ba dare ba rana sannan kuma yana taimaka musu wajen kula da babies ɗinsu.
Bayan wata biyu sauran matan su ma suka koma garuruwan su, a ka bar Kamal da matansa da kuma yaransa.
Ƙarfe ɗayan dare Intisar(babayn Salma) ta fara kuka kamar yan da ta saba, haka Kamal ya yi ta fama da ita yana yawo yana jijjata har ta koma bacci.
Yana sa kansa a pillow Ihsan (babyn Safiya) ma tace garina ya waye haka ya ɗauko ta idanunta abuɗe sai binsa da kallo take ko kaɗan babu alamun barci tare da ita.Safiya na jinsu tayi kamar ta na bacci, a ranta tace "wata tara nayi ba wanda ya tayani dan haka yanzu nima barci na zanyi" haka kamal ya yi ta jela tsakanin ɗakin Salma da Safiya yana kula da yaran su.
Da ƙyar Kamal ya ɗaga hannu ya bugawa maman sa ƙofa, ta ɓuɗe. "Subahanallahi! Kamal ya na ganka haka fuska duk a kumbure ga idanu sunyi jawur kaman an baɗa maka burkono?" Hajiya Samira ta faɗa.
Da ƙyar ya buɗe baki yace "mama an gyara ɗakin?" Hajiya Samira tace "eh" take kamal ya wuce ɗakin shi na gauranci ya kwanta ya fara bacci.
Tunda ya kwanta ƙarfe takwas na safe(08:00am) bai farka ba sai ƙarfe sha biyu da rabi na rana (12:30pm).
Yana fitowa parlour mahaifinsa ya tintsire da dariya sannan yace "kamal mai gida biyu maganin gobara, Baban biyu Allah ya ƙara biyu!, mai ya kawo ka gidana ɗazu da sanyin safiya?"
"Hm! Baba ai dole ka ganni, ashe haka abun yake?, yanda kasan kalangu haka Intisar da Ihsan suke bugani a gida!"
"To kai dama ka ɗauka auren wasa ne?, ai duk wanda ya ce yaji ya gani zai yi aure to dole ya shirya wa ɗawainiyar auren; mafiya yawan auren da ke mutuwa wata uku ko biyar bayan aure mafiya yawa sun jahilci auren ne.
Mafiya yawan mata ɗabi'un su na canzawa idan sun samu juna biyu, shi kuma goga in bai fahimci hakan ba sai ya ɗauka da saninta take masa wulaƙanci daga nan sai saki.
Wasu kuma bayan haihuwa ne ɗabi'un ke sauyawa saboda stress da kuma wahalar kula da miji, yara, da kuma gida san nan ga gajiya da rashin samun wadataccen barci.
A irin wannan yanayi sunfi buƙatan lokacin ka da kuma agazawarka tare da tausayawarka a gare su.
Yawan yabo da godiyar ka gare su tare da kambaba abunda su ke yi koda bai kai hakan ba, zai taimaka musu wajen samun nutsuwar zuci.
Nuna musu soyayya da ƙauna na da matuƙar muhimmanci wajen kwantar musu da hanakali da samun walwalar zuciya da na fuska."Kamal yace "tabbas haka ne baba. Allah ya ƙarawa mata albarka ya biyasu da gidan Aljanna tare da mu baki daya." amin.
Baban kamal ya miƙe yace mu wuce masallaci karfe ɗaya ta cika naji ana kiran sallah. Kuma daga yau ka zauna gida gurin matanka kada na sake ganin kafafunka da sunan kazo barci, kaje kai haƙuri irin yanda su ke yi. Allah ya muku albarka.
"Amin baba"Kamal ya faɗa.
.... Ina godiya da bibiyar labarin da nake kawo muku, sai dai haryanzu ina matukar buƙatan jin ta bakinku akan abunda labarin ya ƙunsa
..... yawaitar comment ɗinku zai ƙaramun kwarin guiwa. Na gode.
.... Fatima Abubakar Saje (ummuadam).
YOU ARE READING
INGANTACCEN KISHI
General FictionCigaban labarin bin dokar Allah ba ƙauyanci bane. Sannan kamar yadda sunan ya nuna zan fi maida akalan rubutun akan nau'o in kishi, dalilan da yasa ake kishi, banbanci tsakanin kishi da hassada. Ina fatan zaku kasance tare da ni. Kada ayi amfani da...