🎡🎡ZUBAR HAWAYE NA🎡🎡
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚
WHATPAD NAME
*AISHAMAARUF*📚📚PAID BOOK📚📚
*FREE PAGE*
Insha Allahu zan cigaba da posting din ZUBAR HAWAYE NA on 15 0f August insha Allah.indai na Fara posting baka biya ba sai dai ka bidi complete.mai bukata ya biya kafin date dinnan pls.
PAGE 8
__________________________ Tafiya ta farayi a hankali kaman kwai ya fashe mata a ciki, tana kaiwa bakin kofan ta bude Baki da niyyan gaya ma mama magana sai kuma tayi shiru ko me ta tuna ohoo!, "mama ko harde hannuwa tayi a kugu tana wani karkada jiki" dukawa lauratu tayi ta fara kwashe kayan ta dake watse a kasa wani hawayen bakin ciki na taruwa a idan ta, diba wanda zata iya tayi ta nufi dakin Nasreen dashi, "Nasreen dake kwance kanta saman pillow ta harde hanayen ta akan cikin ta ne tabi Antyn nata da kallon alaman Karin bayani, amman Allah bai bata daman bude baki ba tayi magana" haka laurar ta ajiye kayan a kan tabarman data shinfida a dakin sannan ta fita, "binta da ido kawai Nasreen tayi dan bata fahimci komi ba" bayan kaman minti 2 sai ga Anty lauratu da Akwatin kayanta, "Nasreen naganin haka ta tabbatar da abinda zuciyan ta k raya mata, kokarin tashi tayi sai ta dan saki kara kadan alamun tadan pama inda k mata ciwo" juyowa Lauratu tayi tace" banace karki tashi ba, maza koma kar ranki ya baci, ta karasa ranta a dan bace" juyawa tayi zata fita ta jiyo muryan "Nasreen na fadin Anty tayaki kwashewa kawai zanyi" Juyowa Lauratu tayi tace Nasreen Nasreen Nasreen!!! Saunawa na kiraki, "uku Anty" toh! Idan kika kuskura na ganki a waje sai na jibgeki dukda ba warkewa kikayi ba amman saina kara miki, kuma in karya ne ki sallake magana na ki gani ta karasa da barin daki, Bayan tagama kwashe kayan tassss! Ta jera su a cikin dakin aiko dakin ya kara kyau, wurin hand bag dinta ta nufa ta dauko mata magani sannan ta dibo ruwa a cup mai tsapta, "dan Nasreen akwai sapta gata karamar yarinya", balle maganin tayi zata samata a baki, "sai Nasreen ta fara yamusa fuska tana turo baki" iko dole kisha shi, dan zai taimaka miki sossai, maza bude bakinki, "bude baki Nasreen tayi tana taushe hanci dan batasan warin maganin, aiko maganin na shiga bakinta tayu tsaurin anshe cup din a hannun Anty ta shanye ruwan kopin tasss! Tana tsauke ajiyar zuciya" Dungure mata kai Anty lauratu tayi tace ko k fahhh! AI yanzu zakiji sauki insha Allah, yanzu ki kwanta kafin nagama hada mana kayan kari tana shafa kan Nasreen da murmushi a fuskan ta, tashi tayi ta nufi Akwatin ta ta dauko wani bargo mai laushi wanda saurayin ta ya bata da wasu kaya a last birthday ta, bayan ta dauko ta kulle akwatin sannan ta nufi gadon, warware bargon tayi ta kulleta dashi sai kamshi k tashi a jikin bargon dan ba laifi Anty lauratu akwai sapta, fuskan ta ta leka taga harta fara barci, murmushi tayi sannan ta bar wajen, zama tayi akan tabarma ta fara tunanin duniya da halin da suke a yanzu sannan tace "ashe dama haka mutun yakeji idan baida kowa, wani hawaye ne ya taru a idan ta, hannu tasa ta dauke shi, sannan ta fara tunanin halin da yarinyar tashiga tun rasuwar mamanta, hawayene kawai k diga a fuskan ta, sai shashekan da take, hannu ta daga sannan tace Allah nagodema daka kubtar dani ka dawo dani hanyya madaidai ciya, sannan tayi Addu'an Allah ya shirya mamarta da yaruwarta, sannan ya warware kullin da akayi ma baban su, sai da taci kukan ta ta gode Allah kafi ta tashi ta dau hijabin ta, wayanta dake saman gado ta nufa taga karfe 10, zaro ido tayi a zuciyar ta face Ashe najima a zaune, daukan wayan tayi ta nufi jakan ta ta dau dari biyar ta fita a dakin, mama ta tadda a sakar gida, har ta nufi zaure sai taji muryan mama tace "sai kuma ina gantalalliya"har Lauratu ta juya zatayi magana ko me ta tuna sai kawai ta juya ta fita a gidan, tana fita bata zarce koina ba sai wurin da ake siyar da kosai, layi ta tadda, dan akwai kaman mutane 6 a gaban ta, wani dan dutse dake kusa da ita ta zauna akai, zaman ta baifi minti biyu ba taji ana magana akan gidan su, har anayi ana nunata, daya daga cikin samarin dake wurin ne yace" I ko jiya naga wannan yayar tata da misalin karfe 11:30 wani kato ya ajiyeta, duk suka kwashe da dariya, banda wani dan matashin yaro da bazai wuce shekara 22 ba yace" ba shakiyanci ya kamata kayi musu ba, wa'azi zakayi, inkuma bazaka iyaba sai kayi musu Addu'a karka manta Allah ne k jarabta kuma su da suka sami kansu a halin da suke bayin kansu bane, "JARABTA CE" kar kaman ta kaima kana da kanne da kuma en uwa mata baka tunanin Allah zai iya jarabtan su da irin wannan halin, yanzu alal misali kanwarka ce a wannan yanayin yazaka ji, ba sai lallai kanwanka zakayi ma wa'azi ko gyra ba, a'a akwai hakkin makwabtaka, kuma inzaka ma mutun gyra bawai kayi mishi a cikin mutane ba a'a gefe zaka ja shi kamai magana cikin lafazi mai dadi, in Allah ya yarda ko bai bar wannan abin ba kaso 80 zai ragu, wannan shawara ce yana fada yayi kokarin barin wurin, tashi Lauratu tayi tace hakika Ahmad naji dadin duk abinda ka fada kuma Nagode sossai, hakika kacika makwaci nagari duk da baka taba tinkaran ko daya daga cikin mu ba, amman ba komi Nagode da abin da kace ta karasa da shasshekar kuka hannun ta daya kuma tana share hawayen ta dashi, Inasan inroki wata Alfarma daya a wurin ka, amman Inasan ya zama sirri ko zaka bani Aron minti 2 ta fada tana hada hannayen ta biyu alaman roko, " girgiza mata kai Ahmad yayi yace basai kin roke niba ni mai baki lokaci nane na daukeki a masayin yar uwata na jini sabida haka karkiji shakka, kawai ki same ni kai tsaye, "murmushin ta mai kyau ta saki har wushiryar ta ya bayyana, tashi sukayi daga inda mutane suke suka nufi gefe inda babu kowa sannan tace dan Allah so nake ka zame mana kamar yaya dan Allah, in zan kwace hanyya kamin gyra ta karasa tana hade hannayen ta alamun roko" murmushi yayi yace" dan wannan abin shine kike rikona, hmmmm! Karki damu na dauka insha Allah, Allah tayani riko" murmushi tayi mai hade da hawaye, komawa sukayi wurin mai kosan, tace Ahmad gashi an sama, kara na 50 aciki, karawa mai kosan tayi, amsa yayi ya mika ma Lauratu sannan yace ki tafi gida, kokarin mika mishi kudin hannun ta take amman yaki amsa sai ma hada mata danyayi da dari biyar ya juya ya bar wurin, kallan bayan shi take har ya bace ma ganin ta,juyawa tayi ta nufi gidan da ake siyar da kunu tasiya na dari da 150 sannan ta wuce gida, sallama tayi kafin ta shiga, tana shiga ta tarar babu kowa acikin sakar gidan hamdala tayi sannan tayi tsauri ta shige daki da sallama a bakin ta, samu tayi Nasreen nakan barci, a jiye kayan hannun ta tayi sannan ta nufi inda take kwance, tadota tayi sannan tace taje tayi brush, gani tayi ta dau brush din zata fita, Kiran ta Anty Lauratu tayi tace yanaga bakisa close-up ba,I banda shi Anty da gishiri nake yi, Kiran ta Anty Lauratu tayi tace ki bude wancan jakan akwai sabon brush da my clean, da tohh! Nasreen ta amsa ta nufi inda jakan yake, budewa tayi ta dau abinda take bukata sannan ta fita a dakin bayan ta gama ta shigo ta ijiye brush din a inda tasaba ajiyewa sannan tazo ta zauna a kusa da Anty Lauratu suka fara cin abinci, bayan sun gama ta kwashe tarkacen laidodin ta kai Bola kofin kuma ta dauriye shi ta maida shi mazaunin shi, zuwa tayi ta zauna a kusa sa Anty Lauratu, tayi mata magana sau uku akan shiru sai da ta tabata sannan ta juyo ta kalle ta, Anty tunanin me kike, sauke nauyayyen ajiyan zuciya Anty Lauratu tayi sannan ta fara bata labarin abinda ya wakana da taje siyan kosai, bayan tagama gaya mata Nasreen tace"Allah tsarki Allah yai mai Albarka yasa ya gama da duniya lfy ya Kare shi daga sharrin masu sharri, da Amen Anty Lauratu ta amsa sannan tace ni bari indan mike barci nakeji, tashi tayi ta hau kan gado sannan taja bargo, Nasreen ma tashi tayi ta hau kan gadon......................................
DAGA ALKALAMIN GIMBIYA AYSHU 💞💞💞
KUYI HAKURI DA WANNAN SAI MUN HADU A NEXT PAGE.
YOU ARE READING
ZUBAR HAWAYE NA
General FictionLadi tace"Bazaki taba Auren mai kudi ba sai talaka, talakan ma tukuf Wanda sai kun wahala zaku samu abinci" "yarana ne kawai zasu Auri mai kudi" Matsiyaciya mai kama da mayya, yar tsintarciyar mage " Ba abinda Nasreen keyi banda hawaye"...