🌼🌼ZUBAR HAWAYE NA🌼🌼
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚📚📚
PAGE 10
__________________________Meeting din aka Fara ba Bata lokaci,basu suka fito a meeting ba sai karfe hudu,gaisawa duk sukayi aka rabu lfy,daganan masallaci Mafi kusa suka nufa,bayan duk sunyi sallah suka Kama hanyyan company,karfe 4:37 suka Isa company,ko da Arif ya Isa bai zarce ko Ina ba sai Office din daddy,shiga yayi da sallama, bayan ya gaishe da daddy ya fayyace mishi Yanda akayi a gurin meeting,bayan ya gama bayani,suka Dan tattauna da daddy sannan ya nufi office din shi,Yana shiga ya rataya coat din shi akan kujera,dakin dake cikin office dinshi ya shiga,dakin ya tsaru komi na cikin dakin blue ne da fari,royal bed ne a dakin yasha gyara da bed sheet Mai taushi,cire kayan shi yayi ya nufi bayi,bayan kaman minti 20 ya fito daure da bath rope fari Kal,da wani Dan karamin towel a hannun shi Yana share gashin kanshi da shi,hand dryer ya dauko ya busar da kashi, ya gyara,Bayan ya Gama ya shafa mayukan shi masu tsada,Tulare ya dauka ya feshe jikin shi da shi, drawer ya nufa ya dauko wani kananan Kaya farin riga Mai guntun hannu da wandon jeans navy blue,Tulare ya dauka ya fesa bayan ya Gama shiryawa,kallan kanshi ya yi a madubi, murmushi yayi sannan ya juya ya fita daga dakin.
12:00 Nasreen ta shigo gida bakin ta dauke da sallama,mama ta iske a tsakar gida da Anty lauratu suna girki,gaishe su tayi,Suka amsa,Anty lauratu ne tace sannu da zuwa,yau kin dawo da wuri,Masha Allah, murmushi kawai Nasreen tayi tana Mika ma mama kudin hannun ta,kwace kudin mama tayi tana hararan Nasreen,dauke Kai Nasreen tayi ta nufi inda ake ajiye kwanoni ta ijiye tiran.Buta ta dauka ta wuce bayi Bayan ta fito ta zo takama musu aiki.Da musalin karfe 12 da minti 55 Suka kammala girki,Anty lauratu tasa ma kowa nashi na baba Kuma akasa a cikin cooler. Tashi duk sukayi sukayi Alwala mama ko daki ta nufa Dan ita sai taga dama take sallan,bayan sun idar da sallah sukaci abince,tattara kwanon Nasreen tayi ta nufi waje,ruwan wanke wanke a hada ta fara,fitowa Anty lauratu tayi ta Fara tayata,sunayi suna Hira har suka Gama,bayan sun kammala wanke wanken Nasreen ta share tsakar gidan tas ta gyara ko Ina.
Tun da Nasreen ta kammala Aikin gida ta kwanta barci ba ita ta tashi ba sai karfe 4:30,tana farkawa ta duba lokaci,tana ganin time ta mike da tsauri da Addu'a a bakin ta,fita tayi ta saka ruwa a buta bayan ta fito tayi Alwala ta Yi sallah,bayan ta idar da sallah tayi Addu'a ta yima Ammin ta ma Addu'a,bayan ta kammala,ta cire hijabin ta sannan ta fita sakar gida inda ta tadda Anty lauratu na gyara wutan da za'a daura sanwa,tayata Nasreen tayi sukayi girkin,da misalin 6 saura suka kammala,tuwan masara da miyan kubewa bushashe sukayi,raba abincin sukayi yanda aka saba.
Cikin dare da misalin karfe 2 da minti 36 na dare Anty lauratu ta farka a firgice, bakin ta dauke da Addu'a,ta hada uban zufa sai zare Ido take,jikinta na rawa,ta Kai minti 10,a haka kafin tadan Fara samun natsuwa,juyawa tayi ta kalli Nasreen hawaye na tsauka daga idanta,shafa kanta tayi tayi Mata Addu'oi sannan ta shafa Mata,ba ita ta koma barci ba sai karfe 3 da minti 15,tana kwantawa barci Mai nauyi ya dauketa.......
Nasreen ce ta Fara tashi da Addu'a a bakinta Mirza idan ta tayi ta kalli a gogo taga karfe 5 da minti 15,Kiran sunan Antyn ta tayi Amman Bata amsa ba,hannu tasa ta jijjigata tana Kiran sunan ta,sai data yi mata hakan sau uku kafin ta iya tashi,tashi tayi tasa hannu biyu ta rike kanta da shi tana Addu'a,dago kanta tayi ta kalli Nasreen,sai mafarkin da tayi ya Fara dawo Mata,saurin kawar da mafarkin daga zuciyar ta tayi tana Addu'an naiman tsari, Nasreen ce ta katse Mata tunanin da take da fadin "Anty lauratu Mai ke damun ki kanki na ciwo ne, girgiza Mata Kai Anty lauratu tayi alamun ehhhhhh! Langwabe Kai Nasreen tayi kaman zata zubda hawaye tace sannu kinji Antyna, murmushi Mai Hadi da Hawaye Anty lauratu tayi ta rungume Nasreen tana kuka kasa kasa,Hawaye ne ya sauko daga idan Nasreen,tace"Baki da lafiya ne,Mai yasa kike kuka,nayi Miki wani Abu ne,in nice Dan Allah kiyi hakuri ki yafe min ta fada tana fashewa da kuka" cire ta Anty lauratu tayi daga jikin ta a rikice tace Dan Allah kibar kuka bakimin komi ba,kawai dai kaina ne ke ciwo,Amman Babu komi Bayan haka ta karasa tana share hawayen dake idan Nasreen,sannan tace "Baki taba min laifi ba kanwata,illa taimakon da Kika ma rayuwa ta,zuwan ki rayuwa ta Alkairi ne kuma babban ni'ima ce nagode ma Allah daya hadani dake,ta fada tana murmushi" murmushi Nasreen tayi har fararan hakoranta Suka bayyana, rungume juna sukayi suna murmushi da Hawaye,"itako Anty lauratu zuciyar ta sai suya yake,ba abinda take tunani kaman mafarkin da tayi, Addu'a take Kar Allah ya tabbatar da mafarkin da tayi"Basu suka saki juna ba sai da wayan Anty lauratu tayi Kara,tashi sukayi Suka nufi waje inda Nasreen tafara shiga bayi bayan ta fito Anty lauratu ta shiga,Bayan sun idar suka Fara aikin yau da kullum,"inda Sabo yaci ace sun Saba"Basu suka Gama aikin gidan ba sai karfe 9:20,shiryawa Nasreen tayi Dan ta wuce talla,bayan ta Gama shiri harta dau tiran a Kai ta Kai bakin kofa,Anty lauratu tayi saurin tare ta,tace tayi Addu'a Bayan tayi tabata wani ruwan Addu'an Tasha,sallama sukayi sannan ta wuce, tsayawa Anty lauratu tayi a zaure tana kallan ta har ta bace ma ganin ta,komawa ciki tayi jikin ta a sanyaye.
YOU ARE READING
ZUBAR HAWAYE NA
General FictionLadi tace"Bazaki taba Auren mai kudi ba sai talaka, talakan ma tukuf Wanda sai kun wahala zaku samu abinci" "yarana ne kawai zasu Auri mai kudi" Matsiyaciya mai kama da mayya, yar tsintarciyar mage " Ba abinda Nasreen keyi banda hawaye"...