🌼🌼 ZUBAR HAWAYE NA🌼🌼
STORY AND WRITTEN BY
GIMBIYA AYSHU 💞💞💞
ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚
PAID BOOK
NORMAL GROUP 200
VIP 400
COMPLETE DOCUMENT 500 A GARAPASA.ACCOUNT NAME: AISHA MAARUF
BANK NAME:UBA
ACCOUNT NUMBER:2245462427
NUMBER OF EVIDENCE VIA WHATAPP:08076119294NAGAMA FREE PAGES DINA ALHMD SAURA NAGAMA LITTAFIN ALLAH YA BANI IKON GAMAWA LAFIYA.AMEEEN.
WHATPAD NAME:AISHA MAARUF
AREWABOOKS:2503
FACEBOOK:AYEESHA ASHRAF MUHAMMAD.INA GODIYA GA MASOYANA WA'INDA NASANI DA WANDA BANSANI BA,INA GODIYA,ALLAH YA BAR KAUNA.
PAGE 20/21
________________________________Alhmd su Nasreen sun kammala exam din su lafiya inda aka basu hutu,A hutun nan Mummy ta dauke ta suka bar kasar zuwa garin Dubai saboda wani business din ta,inna ce muku Arif yaji dadin tafiyan nan nayi karya,dan"tun kafin su tafi yayi ma Mummy magiyan ta barta ko kuma a je da shi sai ya dinga mata aike tare da wasu abubuwan",Amman mummy kememe Taki tace bawani Aiken da zatayi, yayi zaman shi da baban shi,in ta kwashe su duka baban kuma fah,wa zai zauna da shi,yayi rokon yayi magiyan Amman duk busuyi aiki ba,Da Mummy tagaji da Abin da yake tace wai mai haka ne Arif yaushe muka fara hakan da kai inajin dai ba yau nafara tafiyan ba,ka taba cewa zaka bini y This time,"shiru Arif yayi Dan his totally speechless and hope less,tun da su Nasreen suka tafi Arif ya Zama kaman wani mara lafiya,kullum sai ya kira Mummy sunyi waya bayan sun gama gaisawa sai yace aba Angel,ba musu Mummy ke bata waya suyi fin awa suna waya ko mai suke cewa oho! Mummy ko ita abin har mamaki yake bata,in ita kadai ce a daki sai ya maida akalan wayan zuwa video call yayi ta kallan ta, inta ce maiyasa yake kallan ta, sai yace yayi missing din kanwan shi ne kawai,in yace haka shikenan sai dai tayi ta washe hakora tana mishi shiriritar ta.
Satin su Nasreen biyu suka dawo Nigeria,wannan satin biyun da sukayi Arif ya dinga ji kaman shekara sukayi,Arif ne yaje tarban su a Airport,mintin shi 15 da tsayuwa jirgin su Mummy sukayi landing,Nasreen da Mummy ne kesaukowa daga matattakalan,Hango Arif tayi da tsauri ta saki hannun Mummy ta ruga da gudu ta nufi wurin shi,tana isa batayi wata wata ba ta rungume shi,shima hannun shi yasa ya matse ta a jikin shi yana sauke ajiyar zuciya sai kace wanda yayi gudun kilometer ashirin '20',rada mata i miss u yayi a kunne,dagowa tayi tace i miss u too my lovely yaya, murmushi yayi sossai har sai da hakoran shi suka bayyana,cire ta daga jikin shi yayi sakamakon irin kallan da Mummy ke aika mai da shi,karasowa wurin su tayi tana auna ma Arif harara,gaishe da Mummy Arif yayi,amsawa Mummy tayi a dakile,wurin mota suka nufa suka shiga suka nufi gida.
Ko da suka isa gida sun iske daddy na gida,tarban Mummy da daughter shi yayi,bayan sunyi refreshing suka sauko suka ci abinci,bayan sun gama suka yada zango a parlor aka bude babin hira,tunda aka fara hiran Arif ko uffan bai ce ba,jingina yayi da kujera yana ta kallan su,daddy ne yace son was wrong with you,are u okh son,amsawa Arif yayi da Yes daddy, Mummy ko kallan shi tayi ko kala bata ce ba,da misalin karfe 10 duk suka watse.
***********************************
A bangaren Anty lauratu yanzu watan ta biyu da Aure,tasaki jikin ta sossai a gidan mijin ta,sai dai har gobe Nasreen na zuciyar ta,wani lokacin inta tuna ta sai taci kuka,kuma tayi mata Addu'a.Anty lauratu ne ta tashi ta nufi bayi da gudu sai yunkurin Amai take Amman ta kasa,wanke bakin ta tayi ta dawo parlor,Bata kaiga Zama ba wani yunkurin aman ya taso mata,haka ta nufi bayi da gudu dan ji take kaman zai zubo,a ranar wuni tayi a kwance komi ta kasa yi,gashi mijin ta bayanan tunda ya fita bai dawo ba,kuma wayan ta na daki ta kasa zuwa dakin. Kwance take wuraren karfe 6,tayi dai-dai a kasa sai nunfashi take da kyar,Ahmad ne wato mijin Anty lauratu ne ya shigo parlor su inda ya hango matarshi kwance a kasa,da tsauri ya karasa inda take yana tanbayan ta lafiya amma ta kasa amsa mishi dan ta galabaita ba kadan ba,mikewa yayi ya nufi daki da sauri ya dau mata hijabi,sunkutan ta yayi ya nufi wajen gidan da ita,bai zarce ko Ina ba sai wani Asibiti,amsam ta akayi da gaggawa aka fara bata taimakon gaggawa,bayan ta sha Allurori aka daura mata ruwa,tuni barci wahala yayi awon gaba da ita,diban jinin ta akayi aka nufi lab da shi bayan anyi test aka kawo ma Ahmad result,budewa yayi yana dubawa,baisan sanda ya mike tsaye ba bakin shi ya kasa ruhuwa,hannu ya daga yana gode ma Allah da ni'iman daya mai,"Ba komi ke kunshe a takardar nan ba face test din da aka ma Lauratu,kuma angano cewa tana dauke da ciki kimanin wata daya da sati biyu wanda shine ya haddasa mata wannan aman da rashin kwarin jiki datake fama da shi.
Kwanan su biyu a Asibiti aka sallame su,inda doctor ya bashi shawara yanda zai kula da matar shi da kuma abinda ke cikin ta,bayan an sallame su bai zarce ko ina ba sai gida,ruwa ya daura a gas,bayan ruwan yayi zafi ya haɗa ya kai bayi,towel ya dauka ya Bama Lauratu bayan ta tube ta daura,taimaka mata yayi har bayi,bayan sun shiga ya kulle kofa,kokarin kunce towel dinta yake, kallan shi tayi da sanyyin jiki tace ka bar shi zan iya,girgiza mata kai yayi alamun "sam bazai sabuba bindiga a ruwa"kunce towel din yayi sannan yayi mata wanka tare da gasa mata jiki sossai,bayan ya gama ya daurota a towel ya kaita daki shirya ta yayi cikin kayan barci mai kauri da yake dare ne,hijabi ya bata ya shinfida mata darduma,bayan ta idar da sallah ya kawo mata abinda ya siyo,yayi feeding din ta,sai wani tattalin ta yake kaman kwan da baisan ta fashe.
YOU ARE READING
ZUBAR HAWAYE NA
General FictionLadi tace"Bazaki taba Auren mai kudi ba sai talaka, talakan ma tukuf Wanda sai kun wahala zaku samu abinci" "yarana ne kawai zasu Auri mai kudi" Matsiyaciya mai kama da mayya, yar tsintarciyar mage " Ba abinda Nasreen keyi banda hawaye"...