f p 2♥️

73 6 0
                                    

𝑭𝒂𝒕𝒚𝒎𝒂𝒔𝒂𝒓𝒅𝒂𝒖𝒏𝒂

  𝒃𝒐𝒐𝒌 𝒐𝒏𝒆

   𝑪𝒉𝒂𝒑𝒕𝒆𝒓 2

Kaman saukan Aradu haka AMJAD yaji wannan maganan akunnuwan shi, baisan sanda ya turetaba tare da tashi daga kan gadon yana mai dafe kanshi da yake Neman tarwatse wa, ganin haka ne yasa zuciyar Fatouma bugawa da mugun karfi .

Juya wa AMJAD yayi tare da nufan kofan fita daga dakin, saida yakai kofa sannan yabjuyo yace mata , "Fatouna ina miki fatan alkhairi a rayuwar auren ki, Allah ubangiji yasa gidan zamankine , Allah ya hada kawunan ku, dan Allah karbkiyi abun da Abey zaiyi fushi dake .

Ya wuce koma a gurin ki, amma ina me tabbatar miki daga rana mai kama data yau bazan sake farin ciki ba, bazaki sake ganin murmushi na ba, zan tayaki yiwa mahaifinki biyayya.

Sannan gobe zan koma London idan an fara biki zan dawo , saboda bazan so bananan ayi auren farin ciki na ba , Fatoouna kina da muhimmanci arayuwata, kisani har abada ke ce farin cikin Amjad, kuma bazan daina sonkiba har karshen rayuwana .

KISANI KE CE RAYUWATA KE CE RUHINA ,KECE DUNIYATA, IDAN DA RABO ZAN SAKE GANIN KI IDAN KUMA ALLAH YA DAUKI RAINA, ZAMU HADU A AL'JANNA ZANGA 'YA'YANKI" , yana gama fadan hakan ya juya yafi ce daga dakin .

Ganin ya ficene yasa Fatouma sulalewa a kasa tana numfashi sama sama.

A palo kuwa ganin Amjad yafita da hawaye a fuskansa yasa Hamdan tashi tanufi dakin Fatouma, ganin halin da take ciki ne ya sakata saurin karasowa , hannunta Fatouma tarike da matukar karfi wanda hakan yasaka Hamdan runtse idanuwan ta da matukar karfi, cike da jin zafi acikin zuciyar ta.

A can waje kuwa Amjad na fita daga cikin part din yaci karo da maman su, ganin da yayi matane yasa wani irin kuka yazo mishi , cike da karyewar xuciya ya karasa inda take ya rungume ta.

Runguma yayi mata irin wacce daka gani kasan zuciyar sa tayi rauni, rungumeshin tayi itama tana shafa bayan shi, sai da yayi kuka har rauninsa yabayyana sannan ta dagoshi ta shiga share mishi hawayen dake cigaba da zuba a fuskan shi,magana tafara yimishi a cikin rarrashi.

"Shh Amjad dear kar kayi kuka, komai yayi zafi maganin shi Allah, kuma nasan kai mai imanine akan komai, nasan kasan Allah ne ya kaddara koma meye amma yanxu kayi shiru addu'a ce maganin wannan kukan naka".

Tana gama fadan haka taja hannun sa suka juya suka nufi part dinsu  , dakin shi ta nufa kai tsaye tare dashi, suna shiga ta sakashi wanko fuskan shi tare da kwanciya a kan gado , sai da taga ya natsu sannan ta fice a dakin.

Tana tafiya tana tuno irin karyewa da raunin data gani a cikin idanuwan shi, lokacinne kuma abokiyar zaman ta ta fado mata a rai , wacce take yayar Amjad , kuma 'kanuwa agurinvta mai tsananin hakuri, da kau da kai, wacce Allah yayiwa rasuwa shekaru kadan dasuka wuce.

Wanda kuma tasan da tana raye Amjad din ba zaiyi kuka haka ba, numfashi tasauke asanda ta karaso kofar da zata sadata da part dinta.

Koda tashiga palon ganin babu kowa yasa ta nufar  dakinta, ta zo wuce wa ta kofar dakin Fatouma taji suna Magana tsakanin ta da Hamdan.

Abun da tajine ya sakata tsayawa domin jin karashen maganar.

"Kina jina Fatou kiyarda da mahaifinki, a farko nayi tunanin dan a cutar dake akayi wannan hadin.

Amma dana duba tsananin son da mahaifinki yake yi miki sai naga ashe babu yanda za'ayi uba yacutar da 'dan daya Haifa acikinsa.

Habban, shine alkhairinki shine duniyar ki kuma shine lakhirarki right now , kiyiwa mahaifinki biyayya.

Nasan mama kanta idan taji wannan maganar, bazatayi bakin cikiba, Habban bayada wani mummunan hali , kawai dai daga yanayinkine, kina da sanyi shiyasa na zaci hakan zai zama cutarwa agareki".

Murmushi maman tayi tare da turo kofan tashigo bakin ta dauke da sallama, ganin mama tashigo fuskanta dauke da murmushi yasa Fatou saurin goge hawayen dake afuskan ta saboda batason ganin bacin rai a fuskar maman ta.

Kuma ta san matukar taga yanayin ta wannan murmushin xai kau daga kan fuskan ta,ganin haka yasa mama kara fadada murmushin dake kan fuskartan.

Saboda tana da yakini saboda kar ranta ya 'baci Fatoun ta goge hawayen, kuma aran ta tana farin ciki da samun 'ya'yan da zasu yankewa kansu hukuncin daya dace koda bata raye.

Karasowa inda suke tayi tare da da xama a tsakiyan su, kwantowa kowaccensu tayi a kafad'an ta ita kuma ta daura hannayenta akawunansu ta fara Magana .

"Yarana sun girma har an fara Magana ba buni aciki, so a fadamun me ake tattaunawaa, takarasa maganan tana kallon Hamdan".

Hawayen dake fuskan ta ta goge tare da fadawa maman abun da ke faruwa, cikeda karfin guiwa maman takalli fatou tace mata, "ALKHAIRINE SHIDIN AGURINKI , YANDA KIKAYIWA MAHAIFINKI BIYAYYA BAZAKI TA'BA GANIN BA DAIDAI BA A RAYUWARKI, NI MAHAIFIYARKI NAYIMIKIN ALKAWARIN HAKAN.

"Now tashi maza ki wanke fuskarki, duk idonki sunyi kananu fuskan ki yayi ja", tana fadan hakanne tana tashin Fatoun daga zaunen datake.

Ganin yanda mahaifiyar ta tayi farin cikine ya sakata sakewa ta fara wasu abubuwan, ganin tasaki ranta ne yasa Hamdan sakin nata ran , dukda tasan acikin ranta tanajin zafi.

ASALIN FATOUMA

Alhaji Muhammad Sardauna, shine sunan mahaifinta, inda yake dan kasuwa mai rufin asiri, yanada mata guda biyu, Hindu ta farko mai kimanin shekaru 18.

Mahaifiyar Fatouma, saikuma Wafiyya matarsa tabiyu mai shekaru 19, a rana daya aka aura mishi su kasancewar daya za'binsace wato Hindu.

Ita kuwa Wafiyya mahaifinshine ya aura mishi ita, kasancewarvta yarinyar amininsa, kuma mahaifinshi babban mutum ne Alhaji Habib sardauna.

Sunyi zaman amana da mutunci a tsakaninsu, inda bayan shekara daya da auren Hindu ta haifi yaranta guda biyu mace da namiji, wadanda sukaci sun MUSTAPHA ana kiranshi da Musty da UMMULKHAIR Hamdan.

Sosai sukayi farin ciki da wannan 'karuwar , bayan shekaru uku har lokacin Wafiyya bata samu ciki ba, tun ba ta damuwa ganin hakan bai damu mijinta ba.

Har itama yafara damunta, alokacinne suka yanke hukuncin ta dauko Amjad saboda babu dadi zama mutuum daya, dukda Hindu ta so tabata Musty amma taki, so lokacin Amjad yana shekaru 3 ne , Amjad kanine agurin Wafiyya .

Bayan wasu shekaru Hindu ta kara haifo yarinyarta kyakkyawa wacce take kama da mahaifin ta sak inda ranan suna taci sunan mahaifiyar Alh sardauna .

Inda ake kiranta da fatou, tun tasowar Fatouma, Allah yahada jininta da Amjad, sosae soyayya tashiga tsakaninsu har girmansu.

A lokacin da Fatou take da shekaru sha biyu Allah yayiwa Wafiyya rasuwa, sosae wannan gida sukayi kukan rashin mace mai hakuri.

Bayan shekaru uku Amjad ya bayyanarwa Fatou abun da ke ransa agame da ita, babu wani bata lokaci ta amince masa , dagananne Allah yasaka wata iriyar shakuwa a tsakanin su fiye da chan baya.....

Ohk done for the day
#𝒎𝒆𝒆𝒆𝒓𝒂𝒓𝒉

ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶 Where stories live. Discover now