*fatymasardauna*
*13*
By meeerarh
haka suka ci gaba da rayuwa a gidan kullum zasuyi s*x cikin jin dad'i da kulawa da juna.A b'angaren Habban kuwa ya riga da yasan cikin jikinta yasa koda yaushe take buk'ace dashi.
Yau cikin yake cika wata takwas da sati d'aya.
Tun safe da suka tashi bayan sun karya kaman yanda suka saba.
Sosai Habban ya lura kaman bata jin dad'i, amma da zarar ya tambayeta zata ce masa lafiyanta k'alau.
A lokacin cikinta yayi girma na ban mamaki.
Yayi yayi suje ayi scanning, amma fir tace sai dai abari ta aihu aga abunda yake ciki.
Haka ya k'yaleta akan idan ta aihun za aga meye a ciki.
Guraren k'arfe sha biyu na rana Habban yana kwance a d'aki yaji ana kiran sunansa a galabaice.
Da mugun gudu ya sauko daga gadonsa har yana k'ok'arin fad'uwa.
D'akinta ya nufa a guje yana had'uwa da tuntub'e, baamm haka ya buga k'ofar kaman yaga kura.
Ganin daya yi Mata kwance a saman carpet dake tsakiyar d'akin tana kukan mutuwa ya sakashi sauri k'arasowa.
"HABIBTIE , meyake damunki, please kiyimun magana", d'agowa tayi ta kalleshi da idanuwanta da sukayi jazur da kumbufa saboda kukan da taci.
Kinkimarta yayi yayi hanyar fita da ita, duk da kayan jikinta sai a hankali, jeans ne da long sleeve tshirt a jikinta.
Sai kanta data d'aure da bandana black colour.
Mota yayi saurin bud'ewa tare da sakata a backseat.
Driver sit ya shiga ya ja motan a tsiyace zuwa asibiti.
Ko da suka isa da gaggawa ya sauka ya shiga asibitin tare da kiran nurse.
Gabon mara lafiya suka dawo dashi aka kinkimeta aka nufi labour room da ita.
K'arfe 4:00pm dai dai Allah ya azurta su da twins mace da namiji.
Tabd'I yau ake yinta, sam farin cikin da suka shiga baya misaltuwa.
K'arfe 7 na dare aka sallame su suka kama hanyar gida.
Suna kama hanya yayi wani tunani, ya nufi gidan Abey saboda yamusu surprise.
Daman sun dad'e da tafiya London gurin Amjad , so yau ne zasu dawo , kuma flight d'insu karfe takwas zaiyi landing.
YOU ARE READING
ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶
Historical Fiction𝐤𝐞𝐜𝐞 𝐫𝐚𝐲𝐮𝐰𝐚 𝐭𝐚,𝐤𝐞𝐜𝐞 𝐤'𝐚𝐝𝐝𝐚𝐫𝐚 𝐭𝐚, 𝐢 𝐩𝐫𝐨𝐦𝐢𝐬𝐞 𝐭𝐨 𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐲𝐨𝐮 𝐰𝐢𝐭𝐡 𝐚𝐥𝐥 𝐦𝐲 𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭 𝐅𝐚𝐭𝐨𝐨𝐮𝐧𝐚, 𝐬𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐢𝐧 𝐳𝐚𝐦𝐚 𝐚𝐛𝐨𝐤𝐢𝐧𝐤𝐢 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐅𝐚𝐭𝐲𝐦𝐚𝐬𝐚𝐫𝐝𝐚𝐮𝐧𝐚 𝐝𝐚 𝐌𝐞𝐞𝐞𝐫𝐚�...