*fatymasardauna*
*by meeerarh*
*E O W*
*9*
Hospital
Sosai Doctor yayi ta wa Amjad fa'da
dan ya zaci shi yayi aikin ganin yanda ya damu,
Hawaye ne kawai ke zuba a idanuwan both Amjad and Hamdan, ganon irin 'danyen aikin da Habban yayi wa 'yar uwar su, Hamdan da ta kasa ri'ke ba'kin cikin, har ta 'dauki waya ga kira Abey Amjad ya kar'be waye yana fa'din,"ba haka bane mafita kar mu fa'da masa, wallahi hakan zaisa yayi Dana sanin ha'da auren da yayi, kuma kin san Abey baya son abun da zai sa 'ya'yansa su tozarta, kuma hakan zai lalata zumuncin dake tsakanin 'yan uwa biyu", hawaye ta share tare da fa'din , "yanzu shikenan yaci bulus akan abun da yayi mata, nita ba zan kyalesa ba", murmushi Amjad yayi yace,"karki damu Hamdan everything will be fine", Doctor 'din da yake zaune kuwa ya saki baki yana kallonsu, a ransa yana tunanin dama ba Amjad bane yayi wa yarinyar haka, amma ko waye ba karamin aiki yayi ba , dan saida akayi Mata dunki , amma dukda haka jini bai daina zubaba, domun ba karamin ciwo taji ba.
'Karfe sha 'daya aka sallamesu bayan anyi Mata 'karin ruwa da wasu allurori, har I zuwa lokacin Fattou bata bu'de baki tayi magana ba, dukkansu sun rasa me yake musu da'di, Amjad a ransa yana tunanin ya kaita gidan Habban ko ya kaita gidan Abey, so amma idan ya kaita me zai fa'dawa su mama, kuma bazai iya bu'de baki yace ga abun da Habban yayi mata ba, ai dukda matarsa ce bai kamata tayi forcing nata ba akan abun da ba ta so, suna cikin haka yaji motan ta tsaya, ashe wai har an kawo .
Ganinsu a kofar gidan Hammad ya saka Fattou dake jikin Amjad ta kara ri'keshi sosai, rumtse idaniwan sa yayi yace, "it's fine Fatou bazai yi miki komai ba I promise you ", in yace promise ya saka ta fito wa tana nanik'e a gefen sa, shigarsu 'dakin suka ji Habban yana k'ok'arin 'balla kofa ya fito, jikin Fatou ne ya 'dauki rawa , ai kuwa sai gashi ya fito, kuka ta fashe dashi tare da k'ara k'ank'ame Amjad tana fa'din, "Hammana please don't leave me alone, wallahi he will do as he please with me, zai cimun mutunci", cak Habban ya tsaya ya kasa k'ara Sowa inda suke, ganin gaka yasa Amjad sauke numfashi dan yafi kowa sanin Habban , da alamu kuma yaga rashin kyautawar abun da yayi.
Zama yayi ya zaunar da ita , a yayin da Hamdan take tsaye tana jiran ganin abun da Habban zai kuma yi, "komai dakake gani Habban wallahi k'addara ce, banso hakan ta fara faruwa tun farkon auren ba, na zaci zaka kula da ita , amma sai naga sa'banin haka, kana tunanin iyayenmu zasu ji da'di idan suka ji abun da ka aikata, bazan ce ka daina ba , kasan dai dai da rashin ta, kuma kasan tsakanin iyayenmu , Kuma na tabbata bazaka so su samu matsala ba, mu zamu tafi , mun barka da amanar Allah", jin haka yasa Fattou tashi ta k'ara fashe wa da kuka, runguma ta Amjad yayi bayan wasu seconds ya sake ta suka fice shi da Hamdan suka barta tana ruzgar kuka kaman an ce mutuwa zatayi.
Ganin sun fice yasa Habban nufan inda take, ganim haka yasa ta fara ja da baya tana rok'onsa da Allah da Annabi kar yayi mata komai bata so, "Am sorry Fattou ", Jin abun da yace ne ya saka tsayawa cak tare da 'daga hannu ta 'daukeshi da marin da ya sakashi kasa k'arasa abun da ya fara fa'da.
Am sorry for not updating two days, I was a little busy
#MEEERARH
YOU ARE READING
ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶
Historical Fiction𝐤𝐞𝐜𝐞 𝐫𝐚𝐲𝐮𝐰𝐚 𝐭𝐚,𝐤𝐞𝐜𝐞 𝐤'𝐚𝐝𝐝𝐚𝐫𝐚 𝐭𝐚, 𝐢 𝐩𝐫𝐨𝐦𝐢𝐬𝐞 𝐭𝐨 𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐲𝐨𝐮 𝐰𝐢𝐭𝐡 𝐚𝐥𝐥 𝐦𝐲 𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭 𝐅𝐚𝐭𝐨𝐨𝐮𝐧𝐚, 𝐬𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐢𝐧 𝐳𝐚𝐦𝐚 𝐚𝐛𝐨𝐤𝐢𝐧𝐤𝐢 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐅𝐚𝐭𝐲𝐦𝐚𝐬𝐚𝐫𝐝𝐚𝐮𝐧𝐚 𝐝𝐚 𝐌𝐞𝐞𝐞𝐫𝐚�...