♥️FATYMASARDAUNA ♥️
*10*
#MEEERARH
Sosai ta bashi mamaki da ta mare sa, bak'in ciki ne fal ransa , amma haka ya daure dan yasan baiyi Mata adalci ba a daren su na farko.
Shayne komai yayi ya k'ara matsowa, idanuwan ta a rufe ta fara kai mishi duka duk inda hannunta yakai.
Sosai tausayin ta ya shigesa lokaci d'aya yaji kaman bashine Habban ba.
K'arfinsa suka yasa ya jawo ta jikinsa tare da rungume ta tsam.
Har ya zuwa lokacin bata saduda ba dukansa take, sai sa taji duk k'arfin ta ya k'are sannan ta saduda ta lafe a jikinsa ta cigaba da raira kukanta gwanin ban tausayi.
Sai da ya bari ta fitar da duk wani k'uncin ta sannan ya d'ago fuskan ta da niyyar yi mata magana.Tana bud'e ido ta ganshi tayi sauri mayar wa ta rufe gam kaman wacce taga abun tsoro.
Cikin tsananin tausayin ta da ya shigesa lokaci daya yace,
" am sorry Fatooouna, wallahi ban san me ya kaini har na aikata miki hakan ba, sharrin zuciya ne, amma I promise you daga zan lizimci to miki duk wani abu da zai sakaki farin ciki, nasan na cutar dake, amma hakan bashi yake nuna ban damu dake ba, please ki bani last chance ,I promise to change for you, for us, for our parents, and our kids in future".
Tsit Fatou tayi ajikin sa tana sauraran abun da yake fad'a, har a ranta tana son yarda dashi, amma idan ta tuna abun da yayi mata.
zuciyarta na shiga cikin tsananin firgici, kaman an tsakure ta haka ta tashi ajikin sa tana tafiya da baya kaman wacce bata son ta juya.
Ganin haka yasa shi jin babu dad'i a ransa, tashi yayi shima yace,"idan har idan nayi nesa dake zaisa ki yafemun InshaAllah bazan k'ara kusantarki ba, har sai kin yarda dani da kanki.
Wuf tayi ta shige d'aki tare da rufo kofa, numfashi ya sauke yanajin wani iri aranshi, a saman kujera ya zube yana tunanin yanda zeyi ya dai dai ta rayuwar su .
haka rayuwa taci gaba musu yau dad'i gobe babu dad'i , kullum da irin halin da Fatou take fitowa dashi, duk Habban ya zama wani kalan abun tausayi kaman ba shiba.
Kullum yana k'ok'arin ganin ya kyautata mata, kullum zai kawo mata abinci ya ajiye, sai ta tabbatar da yabar kofa sannan zata fito ta d'auka ta koma ciki.
fannin Hamdan kuwa har yau bata dawo gidan ba, mama har ta gaji dayi mata magana.
shi kuwa Amjad yama bar k'asar ya koma London inda yake aiki a k'ark'ashin wani asibi, inda yake da matsayin best doctor nasu.
Yau ya kama ranan asabar ranan da suka cika wata d'aya da aure.
Sai da ta dai daici baya gidan sannan ta fito, ta Jima zaune a falon hankalin ta ya tafi gaba d'aya kan film d'in da take kallo a Bollywood *MARJAAWAN*.
shikuwa daya dad'e a tsaye yana tunanin yanda zai shawo kanta ta sake jiki dashi.
Jin alamun mutum a bayan ta yasa ta juyo a firgice, ganin sa yasa ta tashi da mugun sauri tana neman hanyan gudu.
Wuff yayi ya rik'o ta kuka ta sake da matsanancin k'arfi saboda har yanzu gani take zai maimaita abun da yayi mata a baya.
Ganin hawaye a fuskan sa yasa tayi tsit tana kallon fuskansa, gani tayi ta zube a k'asa kan guiwoyinsa .
"Dan Allah Fatou, na azabtu a ta dalilinki, wallahi tunda kika daina mun magana na rasa duk wata natsuwa, nati nadama, Fatou so kikeyi na kashe kaina saboda azabar da kike gana mun, wallahi nayi nadama , domin Allah da manzon sa ki yafemun, domin son dakike wa Abey, inci alfarmar Amjad dan Allah".
Gama fad'in haka keda wuya ta zube a k'asan itama ta rungumesa, sosai kuka ya kufce mishi .
"Am sorry Ya Habban, badan na cutar da kaiba ne, inajin tsoro ne kayi hak'uri".
Daga wannan ranar rayuwar su ta dawo normal kaman kowa, amma har lokacin Habban bai k'ara neman ta a gado ba, saboda yana ganin hakan zaisa ta yarda dashi.
#MEEERARH
YOU ARE READING
ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶
Historical Fiction𝐤𝐞𝐜𝐞 𝐫𝐚𝐲𝐮𝐰𝐚 𝐭𝐚,𝐤𝐞𝐜𝐞 𝐤'𝐚𝐝𝐝𝐚𝐫𝐚 𝐭𝐚, 𝐢 𝐩𝐫𝐨𝐦𝐢𝐬𝐞 𝐭𝐨 𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐲𝐨𝐮 𝐰𝐢𝐭𝐡 𝐚𝐥𝐥 𝐦𝐲 𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭 𝐅𝐚𝐭𝐨𝐨𝐮𝐧𝐚, 𝐬𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐢𝐧 𝐳𝐚𝐦𝐚 𝐚𝐛𝐨𝐤𝐢𝐧𝐤𝐢 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐅𝐚𝐭𝐲𝐦𝐚𝐬𝐚𝐫𝐝𝐚𝐮𝐧𝐚 𝐝𝐚 𝐌𝐞𝐞𝐞𝐫𝐚�...