*fatymasardauna*
*by meeerarh*
*Paid book*
*free page 6*Karfe sha daya daidai aka daura auren Habban da Fatouma.
adaidai lokacin zukatan masoyan biyu ta yi wani kalan duk, Amjad dayake kwance jiki babu karfi .
wani kalan faduwa gabansa yayi, babu shiri yadiro daga kan gadon tareda nufar drower nasa ya dauko wani farin yadi ya zura jikinsa batare daya yi wanka ko sanja kayansa naciki ba.
bedroom sleepers yasaka akafafuwansa tareda rarumar waya yafice daga dakin.
kallo daya zakayimishi kafahimci baya cikin natsuwarsa.
yana fitowa tsakar gidan yaga mutane nashigowa suna nufan part din Abey.
jiyayi zuciyarsa tana shirin faso kirjinsa tafito, yana tsaye a haka yaji karan shigowan sako awayanshi.
da sauri ya duba ganin sunan Fatouna yasakashi bude sakon da sauri, HAMMANA GARDEN.
haka kawai aka rubuta , da sauri yanufi garden dake tsakiyar gidan, bude kofan gurin yayi ya shiga tareda rufewa ta ciki yasaka lock.
a can wani lungu ya hangeta na kanannade guri daya kaman maciji.
jiyayi zuciyarsa ta kara karyewa saboda yasan baza ta iya boye abunda yake arantaba.
jiki asanyaye ya karasa inda take ya tsaya baya kadan.
dagowa tayi da sauri ganinsa yasa hawayen datakeyi suka kara gudu.
idanuwansa dasuke kyalli ya daga sama dan bayaso ya karye mata guiwa.
zama yayi agabanta tareda rike hannayenta acikin nasa.
jin hannayensa anata yasakata rungumeshi da matsanancin karfin ta sake kuka mai ban tausayi.
hawayene suka sulalo daga idanuwansa yayi saurin gogeshi.
sun jima rungume da juna asa'ilin da Habban yake can cikin gida yana neman matarsa.
wacce tunda aka fara maganar bikinsu bai taba nemantaba.
Jin kukan nata yafara ragewa yasa shi dagota tareda goge mata hawayen daduk suka bata fuskanta.
idanuwanta dasuka kankance sukayi wani luhu luhu dasu ya kalla tareda yin murmushi, haba Fatouna nayi tunanin kedin jarumace .
meyasa kikeson nayi wani tunani daban, komai fa daya samu bawa arayuwarsa kaddarar Allah ce.
kuma abunda yayi shine alkhairi, ba kuka zaki zauna kinayiba.
addu'a zakiyi ki roki Allah mafi alkhairi, kiyi addu'a Allah yasaka miki son Habban ko yayane, kicire soyayyar kowa aranki.
sannan kiyimun alqawari duk abunda yake damunki zaki na fadamun.
nikuma nayi miki alkawarin kareki daga dukkan sharri da ikon Allah.
nasan waye mijinki amma komae ze faru kisawa ranki bautar Allah kikeyi, sannan kina yiwa iyayenki biyayya.
inaso daga yau karki sake yin kuka akaina nikuma zan kare mutuncinki, bazan bari mutuncinki yatabuba.
nasan baki mahinceniba amma nan gaba zaki fahimci menake nufi.
Fuskanshi takama tareda fadin, "komae kakeso zan yi makashi arayuwata, amma abu daya yake damuna.
banason wani abu yashiga tsakanina da Habban saboda hakan kaman naci amananka ne.
amma kuma idan natuna hakkinsane sai gaba daya narasa madafa.
dan Allah Hammana kayimun alkawarin bazaso wata ba bayanni.
nikuma nayi maka alkawarinbazan sake kukaba kuma zanyi hakuri daduk halin danake ciki".
Rungume juna suka sake yi daga bayansu sukaji ana tafi, dagowa sukayi dukansu babu wanda fuskansa tanuna tashin hankali.
ganin Habban yasa Fatou sake shigewa jikin Amjad.
Habban kuwa da fuskarsa take kaman panke yayi kansu tareda kaiwa Amjad duka afuska.
ganin hakan yasa Fatou tataso a haukace kafin su ankara ta bawa Habban wani kalan mari dayasakashi seizing a inda yake hannunsa akan fuskansa.
Ke dan uwarki akan wannan kika mareni aikuwa zakici uwarki.
damugum sauri Amjad yayi kanshi zai mareshi Fatou tashiga tsakaninsu.
kallonta Amjad yayi tareda matsawa baya dan yasan halin kayansa, juyawa tayi takalli Habban tareda yin murmushi tace.
uwar data gama maka komae ba, wacce tahaifi ya tabaka ka aura.
Nasan darajar iyaye bansan yanda ake zaginsuba, and kashiga taitayinka hannunka yakuma taba jikin Hammana zanyi maka kaskanci mafi muni.
zan nuna maka asalin wacece ni, cikeda mamaki yake kallonta sannan yajawota jikinsa tareda fadin.
ke nifa mijinkine, jayeta Amjad yayi yayi hanyan fita da ita, suna fita sukaci karo da......
Gamai bukatar book din yatura katin airtel na 200 ta wannan numban (08085056584).
Sannan yatura evidence of payment ta wannan numban a WhatsApp 08085056584
#MEEERARH
YOU ARE READING
ℱ𝒶𝓉𝓎𝓂𝒶𝓈𝒶𝓇𝒹𝒶𝓊𝓃𝒶
Historical Fiction𝐤𝐞𝐜𝐞 𝐫𝐚𝐲𝐮𝐰𝐚 𝐭𝐚,𝐤𝐞𝐜𝐞 𝐤'𝐚𝐝𝐝𝐚𝐫𝐚 𝐭𝐚, 𝐢 𝐩𝐫𝐨𝐦𝐢𝐬𝐞 𝐭𝐨 𝐥𝐨𝐯𝐞 𝐲𝐨𝐮 𝐰𝐢𝐭𝐡 𝐚𝐥𝐥 𝐦𝐲 𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭 𝐅𝐚𝐭𝐨𝐨𝐮𝐧𝐚, 𝐬𝐚𝐧𝐧𝐚𝐧 𝐢𝐧 𝐳𝐚𝐦𝐚 𝐚𝐛𝐨𝐤𝐢𝐧𝐤𝐢 𝐤𝐚𝐦𝐚𝐧 𝐅𝐚𝐭𝐲𝐦𝐚𝐬𝐚𝐫𝐝𝐚𝐮𝐧𝐚 𝐝𝐚 𝐌𝐞𝐞𝐞𝐫𝐚�...