chapter 1_2

30 3 0
                                    

*🌹AL' AJABIN SO🌹*

       *Paid book*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATION*

WANANAN LABARIN CIKE YAKE DA TAUSAYI , ABUN AL'AJABI  DA KUMA SOYAYYAR JUNA

     

Free page 1️⃣➡️5️⃣

zaune suke suna Hira matasa uku ne wanda bazasu wuce kimanin shekara 27 ba a duniya...
Sai ga wasu yan mata guda biyu sunzo wucewa suma de Baza su wuce  shekara 18 ba... tafiya suke suna dan hiran su kasa kasa.... suka wuce samarin dake zaune a saman gada.
  daya daga cikin samarin ne yake fad'in "Maryam Maryam  ya Fada". yana isowa kusa da yan matan wacce ake Kira da Maryam kuwa ko juyawa batayi ba da Alamade kamar ta sanshi tohmmmm Wayasani ...

Gaban yan matan ya tsaya yana dan ajeyar xuciya yana fad'in "Maryam please ki tsaya ki saurareni manah". dauke kai tayi tana kallon gefe kaman ba da ita yake magana ba.

Abokanan nashi ne suka karaso suna fad'in "Umar wai mai yake damunka ne".?
Ko kallonsu baiyi ba balle ya Basu amsa
Zaunawa yayi a gabanta yana cewa  "please Maryam help me i can't live without you, accept me as your husband I will make you proud and you will be the most queen in this world I will make sure  that All the happiness you need I can try All my best to keep you happliy forever"..
Yana fada wani dan siririn hawayene ya zubomishi a dan madaidecin fuskan shi
Ba laifi ....bade kyau ba gashi fari ga hanci dan siriri ga karamin baki tohhh nide kam basan mai dalilin da yasa Maryam taki amincewa da soyayyar shi ba,
Toh Mude muje xuwa dan jin yarda xata kaya.

Wani irin kallon raini da harara ta watsa Masa tace "kai wai wani irin mayene wai nace bana sonka Amma kaki sai wani nanikemin kake kaman wani gum".....
Maganar Abdul abokin Umar ne ya dawo dashi daga tunanin da yashiga Abdul ya fada yana cewa "haba abokina kasani fah karatune ya kawo ka garin damaturu (yobe state) ya Kamata ka maida hankali ka kammala karatunka".!
shi ba maganan Abdul bane ya dameshi maida kallonshi yayi izuwa Maryam ya fada yana cewa "please Maryam".. dakatar dashi tayi da hannu tace "karka batamin lokaci malam".
  wani irin kallo Usman yayiwa Maryam dake tsaye a gefen Abdul ya karaso yana cewa "haba ke wai wani irin Imani ne da ke maisa kike so ki wahalar da zuciyar abokin mu".?
wani irin harara Maryam tayiwa Usman ta Fara tafiya da sauri umar yabita
Yasha gabanta ya sugunna a gabanta yana cewa "Maryam why do you hate me or they is anything else you don't like from me".? yana zubar da hawaye mai tsuma xuciyar mutane  zaro ido Maryam tayi tace "wai kai a tunaninka ina sonka ne? nace bana sonka Amma kaki fahimta". Hauwa ce kawar Maryam dake gefe tayi saurin kasemata magana tace "haba Maryam
Maisa bazaki amsa soyayyarshi ba".? wani dan kallon tausayi Hauwa tayiwa Umar
Usman ne ya karaso yana cewa "aii ina taga Imani bale ta san hakan". ya fada yana daka mata wani irin harara
Umar kazo mu tafi fisge hannushi yayi daga na Usman yace "wai maisa bakwa tausayamin ne da
Wane xanji".?  "aii baka so a tausaya maka ba tunda baka tausayin kanka".
"Tausayi shine ka rabu da wananan yarinyar da ke son jefaka cikin halaka". Abdul ya fada yanawa Umar kallon takaici
Shi maganan shi ma bai dameshi ba
shide Maryam yake kallo da take rike da kwankwaso tana kallon gefe kaman bata wajen
Hauwa ce take cewa "Maryam wai dan Allah maisa bazaki amsa soyayyarshi bane".?
A hankali ta juyo da kanka tayi musu wani irin kallo na raini ta maida kallonta ga Hauwa tace "Hauwa saboda ba kowani na miji bane yake da tabbas saboda da zarar ka amshi soyayyar na miji sai ya Fara wulantaka".
Da sauri Umar yace "wallahi  Maryam bade niba ,bazan iya wulakan taki ba haba Maryam ko irin son da nake miki bai isa ya fahimtar dake cewa ina mutuwan sonki ba".
Maryma ne tayi wani irin karamin dariya tace "ohhhh hakane tohhh idan har kana sona da gaske zan maka wani dan karamin jarrabawa". kowa dake wajen shuru yayi yana jiran mai Maryam zatace.
Umar ne yafara cewa "na amince ko wani irin jarrabawa xan karbeshi Amma ban da na rabuwa da ke Maryam ki dore ki fadamin wananan Assignment din naki don nayi Gaggawan yi miki shi".
Ajeyar xuciya Maryam tayi tana dan wani ji da kai tace "okay idan har kana sona ina so kaje ka fada'a  kasan gadan nan". da sauri Umar ya dako kai a gigice yake kallonta 
Abdul da Usman ne suka ji kaman wani saukan Aradu haka maganar ta fado musu a ka.
Fisgen da Hauwa tayiwa Maryam ne ya dawo da hankali su Abdul da Usman
Tana cewa "baki da hankali ne Maryam kin haukace ne Xakice mishi ya fad'a kasan gada".? "Maryam idan bakya son mutum ba sai kin neme kashe shi ba haba Maryam ko makiyinki baza ki so a mishi haka ba". wani irin tashin hankali dasu Abdul da Usman suka shiga karasowa sukayi dafa  Umar sukayi sukace "kagani ko abun da Muke fada maka wananan ba irin macen da ya Kamata ka so bane".
Wani hawayene ya zubo ma  Umar jinshi yake kaman ba a duniyan yake ba
Kallon Maryam yayi yace "shine abun da Zaki tabbatar da irin son da nake miki".?
Tace "Eh da sauri ta fada tana kallon shi"....
shuru sukayi jum kaman an aiko musu da mutuwa gaba dayan su sun kasa cewa komai,
Maryam ne ta bude baki tace "nasan bazaka iya ba aii"..
Usman ne yace "eh bazai iyaba bazai kashe kanshi kan wanda bata da Imani ba kuma Bata sonshi ba".

"Xanyi". Umar ya fada yana wani irin hawayen gigicewa
Da sauri Abdul da Usman suka dafeshi "Umar xakayi kace".?
Yace "Eh".!
"Umar ka haukace ne? kasan gada fah tace wananan kuma kasheka take sonyi saboda wananan abun da tasaka kayi  sakanin mutuwa ne da rayuwa fah".
"Haba Umar karka kashe kanka a kan wata mace mana wanda ko sonka batayi"....suka fada kaman zasuyi kuka.

Toh fah shin Umar zai je ya fada kuwa akafta.😨

Janye jikinshi yayi daga nasu ya nufi hanyar gadan Hauwa da su Usman suke kallon ikon Allah dan shi Abdul ma saban takaici da bakin ciki ya ma rasa mai ke mishi dadi.
Yana tafiya yana jiran ko Zaiji Maryam tace ka dawo Amma ko tarinta baiji ba
Haka ya karasa saman gadan ya tsaya ya juya yana kallonsu
"Maryam Maryam ki duba fah? Fadawa zaiyi kece mishi ya dawo Maryam".... Hauwa ta fada tana jijigata
Dakatar da Hauwa Maryam tayi tace "kibarshi aii shi ba yaro bane da zai fad'a".
Ya juya ya kalli Maryam yace "Maryam xanyi abun da kike so Amma kisani ko da na mutu karki manta dani dan Allah idan na mutu kizo kan gawana ki furtamin kina sona ko ruhina zata samu sauki".
Kafin kace mai wani Abu saiji sukayi Umar ya fad'a damnm.....
Da sauri Abdul da Usman suka zagaya kasan gadan suka ga  Umar a kwance jinine ke ambaliya yana ta zubowa da sauri suka daukeshi sai asibiti..
Hankali kowa dake wajen ya tashi ita kam Maryam ta rikece don a zotanta bazai fada ba ita abun da yafi damunta ma shine bawai tausayin shi take ba kar ace ya mutu ace ta kashe rai shine duk damuwan da ta shiga ciki... tsaye suke a asibiti kowa yana kallon kowa
Nikam  nace Hanya Maryam tana da imanin kuwa😪😨 dan Nikam ban gani ba toh muje zuwa don jin ya zai kasance.

Duk wajen ba wanda yayiwa kowa magana dan hankali kowa a tashe yake sai Usman da ya kala Maryam ya balla mata wani irin harara yace " wallahi ban taba ganin Mara imani irin ki ba ashe kasheshi kike sonyi daman".?
Abdul ne ya dafe Usman ya girgiza mishi kai da Alamu yayi shuru
Tsaki Usman yaja saboda haushin Maryam yake ji
Shi damuwan  shi ma kar ace Umar ya mutu dan kowa yaga haka ba lale bane yasa wa Umar ran tashi..
Maganar doctor ne ya
Dawo da Usman daga cikin zullum tunanin da yashiga
Da sauri suka karaso suka ce "na'am doctor ya jikin nashi ya yake mai ake ciki".? ajeyar xuciya doctor yayi yace "hadari yayi ne".?
Abdul ne ya maida kallonshi izuwa Maryam ya mata wani irin kallon takaici yace "aaa doctor 
Fadowa yayi daga saman gada".
doctor ne yace "gada kuma".?
Usman yace "Ehh doctor
Yanzu ya jikin nashi". doctor yace " gaskiya bazan ce da sauki ba". Hauwa dake  gefe tace "ya mutu ne doctor".? "Aaa". yace
Yana kallonsu yace "Amma ya samu karaya waje uku". zaro ido sukayi gaba dayan su sukace "karaya uku doctor".?  "innalilahi Abdul yace ya  karasa wajen doctor "yanzu mai ake ciki"? kallon su doctor yayi yace "ina iyayen shi ko yana da matane".? sukace "aaa bai da mata kuma ma ba dan garin nan bane karatune ya kawomu nan" "Amma doctor karka damu duk abun da ake nema baga mu nan ba xamuyi mishi komai".
Doctor yace "kusu waya agurin".??? Abdul ne yace "mu abokananshi ne tun na rayinta kaman  yan uwa Muke dan mun shaku".
doctor yace   "ok" yana tafiya da sauri Abdul yace "xamu iya ganinshi doctor".?  juyowa yayi yace "gaskiya aaa saboda bai farfado  daga suman dayayi ba Amma muna sa ran ze farfado insha Allah Amma Zaku iya Zama a kusa dashi har ya farfado". Yana fada musu haka ya shige   office nashi..
Da sauri Abdul da Usman suka shiga dakin da aka kwantar da Umar suka sameshi a kwance dafe kai Usman yayi yace  "innalillahi".Wani kuka ne ya subuce mishi yana fad'in Umar "Allah ya tashe kafadar ka"...

Su Maryam kam sun bar asibitin tunda sukaji doctor yace bai farfado daga suman dayayi ba.....

Ku biyoni don jin yanda zata kaya shin Umar mutuwa yayi ko suman yayi kaman yarda doctor yace dan Nikam naga ko motsi bayayi fahh😨...toh mu hadu a kashi na gaba

wannan book din na kudine naira 200 ka chal yar uwa ki biya kisha karatu cikin kwanciyar hankali ga Mai bugatan biya ga number account da zai tura kudin sa 2378505923 Rahama babagana Bukar zenith Bank ko Kuma katin waya MTN ta wanna layin 08033297383kamin kitura kudinki ki tabbatar kinma marubuciyan magana ga LAYIN MARUBUCIYAN NAN 08033297383

AL'AJABIN SOWhere stories live. Discover now