chapter 3_4

6 0 0
                                    


*🌹AL AJABIN SO🌹*

     *Write by *RAHAMAKOISE😘*

*MANAZARTA WRITER'S ASSOCIATIONS*   

*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*

Free page3️⃣↔️4️⃣

A hankali umar yake bude idonshi yana kallonsu Sama- Sama yana cewa "Abdul Usman".   da sauri suka amsa sukace "Umar
Alhamdulilah Allah ya tashi kafadar ka".   murmushin jin dadi suka mishi shi kuwa cewa yayi "ina Maryam take".? Ya fada yana dan mikewa zai zauna dafashi sukayi sukace "Maryam kuma umar".? "Aii Maryam Bata nan ta tafi gida".
Ajiyar xuciya Umar yayi yace "dan Allah ku kiranmin ita". zaro ido sukayi da mamaki sukace "Maryam zamu Kira maka?
"Ehh Umar yace dan Allah ku taimakamin inaso muyi magana da ita".
Zaro waya Abdul yayi ya shiga Kiran number Maryam Ringing uku yayi Maryam ta amsa wayan tana fad'in 'hello' "kizo asibiti ana bukatan ganinki yanzu". yana fada ya kashe wayan bai ma bari ta Fadi komai ba ya kashe tare da mayar  da phone nashi cikin aljuhunsa.
Ita kuwa Maryam zuciyarta ne ta wani mugun tsikewa
Dafe zuciyarta tayi tace "na shiga uku ni Maryam kar de ace ya mutu ne" sauri tayi ta shiga daki ta dauko hijabinta
Mommy "xanje gidan su Hauwa in dawo yanxu" tana tafiya da sauri ....Mommy ce takira sunan ta Maryam juyawa tayi tace "na'am Mommy". Mommy ce tace  "ya naga duk hankalin ki a tashe lafiya mai yafaru da Hauwa".? "Kuma ma naga yanzu  Hauwa ta bar gidan nan" shuru Maryam tayi tace "Ehh nima bansani ba Amma yanzu ta kirani tace nazo yanzu zan dawo bazan dade ba".
"Toh sai kin dawo". Mommy ta fada tana shiga kitchen
Toh kawai maryam tace tana fita daga gidan.. gidan su Hauwa kai tsaye ta nufa da sauri ta shiga tana salama Hauwa tana Kiran sunanta karasa shiga cikin gidan tayi
Maman Hauwa ta gaida tace "Mama ina hauwa tana ciki ne".?  "Ehh Maman Hauwa tace tana dakinta ki shiga tana ciki
Toh tace ta karasa shiga dakin Hauwa. Fara Kiran sunanta tayi tana karasa shiga cikin dakin , tana shiga ta tarar da Hauwa  tana bacci wani dan tsaki taja tace Hauwa ke wai baki da aiki sai bacci tana bubugata da sauri Hauwa ta bude ido dan irin bubugatan da Maryam take, tana kallon Maryam tayi tsaki tace "wallahi ke matsala na dake son takurawa mutum ina cikin barcina Zaki wani tasheni kaman nayi sata ta fada tana jan tsaki".
Wani dan murmushin karfin halin Maryam tayi Mata tace ke "kam da wananan baccin kin shiga uku".
Juyawa tayi ta koma cikin bargon ta janyota Maryam tayi tace "ke ni fa akwai matsala babba Wallahi shiyasa nazo ki rakani". juyowa Hauwa tayi tace "wani irin matsala kuma".? " eh mana Abdul ne abokin Umar ya kirani yanzu yace nazo ana nemana a asibiti".  da sauri Hauwa ta Mike tace "innalillahi Umar ya mutune".?? dafe kanta Maryam tayi tace "nima shine abun da bansani ba shiyasa nazo ki rakani Muje muji mai yake faruwa". kallon junansu kawai suke shuru Hauwa tayi chan tace "kingani aii duk ke Kika jayowa kanki wananan matsalar kina xaman xamanki kikaje kikasa dan mutane rasa rayuwansa ni bansan ma dalilin ki na damuwa ba tunda daman hakan kikafi so". kallonta Maryam tayi tace "ni dan Allah ba wananan maganan nazo muyi ba idan zaki rakani kizo mu tafi idan kuma bazakije ba sai ka fadamin". Wani dan kallo Hauwa tayi mata tace "tashi Muje". tashi tayi ta dauka hijabinta itama tace "dama bana nan abun nan ya faru yanzu idan ya mutu nima na shiga uku kai Maryam kinja manah bala'i wallahi".Hauwa ta fada tana fita daga dakin binta a Baya Maryam tayi tace "ki jirani manah mu tafi". fitowa sukayi suna nufan Maman Hauwa.
"Mama xamuje mu dawo yanzu nan".  "ina zakuje".? Inji Maman Hauwa ,kallon Maryam tayi'. Maryam ce tace "daman nazo ne Hauwa ta rakani kasuwa Mommy ce ta aikeni". kallonsu tayi tace toh "karku dade sai kun dawo".
Fita sukayi suna sauri ba inda suka tsaya sai a asibiti suka shiga kowa zuciyansa yana bukawa bude kofan dakin da aka kwantar da Umar sukayi suka shiga a hankali suka Fara shiga ..suna shiga sukaga Umar yana zaune dasu Abdul kallonsu kawai suka farayi da mamaki Hauwa ce ta yi ajiyar xuciya cikin zuciyata kuwa cewa take Alhamdulilah bai mutu ba karasawa sukayi sukace "ya mai jiki".?Umar ne ya amsa yace "da sauki". Maryam shuru sukayi ba wanda ya kara cewa komai , Maryam ne ta maida kallonta izuwa ABDUL tace "kace ana nemana gani nazo". Umar ne yace "nine nake nemanki ,nine nace ya kirawoki Maryam ina so naji amsan da kikamin Alkawin furtamin idan nayi abun da kikace nayi". saurin kallon Abdul Maryam tayi tace "daman akan wananan ne kuka kirani Kuka dagamin hankali tsaki taja tace da nasan wananan ne da banxo ba wallahi".
Abdul ne yace "muma bama son kara kallon wannan fuskan taki din".
Umar ne yace "duk ku dakata dan Allah  Maryam shin kin amshi  soyayyata".? Kallon bacin rai tamishi tace "soyayya da kai hmm ni bazan iya Zama da gurguba ta fada tana watsa musu harara". da sauri Usman dake gefanta ya daga hannu zai mareta Umar ya dakatar dashi yace "karka tabata Usman" juyowa yayi yace "toh wallahi saide ka zaba ko mu ko ita Dan baza mu iya jure cin kashin da take maka a gaban mu ba ko mu ko ita ka zaba". Usman yana fada yana  huci yana sauke ajiyar xuciya. Abdul ne yace "ehh ko ka zaba mu da ita wane zaka zauna dasu a ciki ko mu Rabo da kai kaje ka zauna da ita ta karasaka". kafin kace me Umar Kuka yake kaman Ransa zai fita da kar ya iya bude bakinsa yace "kuyi hakuri xan rabu da ita insha allahu daga yau na rabu da Maryam bazan kara tunanin ta bama na zabeku abokanena". yana Kuka yana dafe kansa ... Maryam cewa yayi "Alhamdulillah na godewa Allah da ya hutur dani daga masufan nan". kama hanun Hauwa tayi tajata suka fita daga dakin ...
Shi kuwa Umar Kuka yake kaman Ransa zai fita su Abdul da Usman ne suke bashi hakuri suke cewa "kayi hkr Umar munyi hakane dan ka Dena yaudaran zuciyanka haka ka Dena wahalar da zuciyar ka". Umar ci gaba yayi da Kukan yayi shuru sukaji  suma hawaye yana zubomu su soboda duk mai Imani sai yayi Kuka Kayi hakuri Umar Allah zai zaba maka wanda ta fita kayi hakuri". suka fada suna kama hannushi shi kuwa Umar cikin kuka da muryan shi da kar ake jinshi yace "na dena soyayya har abada tunda na rasa Maryam baxan kara soyayya ba". shuru sukayi basu ce mishi komaiba.
Sallama doctor yayi yana kallonsu a mamaki yace "ya farkane".?  "Ehh". sukace , doctor yace "Amma gashi yana Kuka mai kukayi mishi". babu komai doctor kawai yana tuna wani abune , ajiyar xuciya doctor yayi yace "so kuke ya kamu da hawan jini kuma? jininsa ya hau sosai fah dan Allah ku fita xan Masa Aluran bacci".fita sukayi suka tsaya a bakin kofan dakin suna jiran fitowar doctor ..sai gashi ya fito da hanzari suke tamabaya shi " yasamu baccin ne".? "Eh yace musu sananan ya kara dacewa "dan Allah ku Dena barin duk wani abun da zai sashi cikin damuwa ko kunci dan in ba'ayi hankali ba  zai iya kamuwa da hawan jini". yana fada ya juya ya tafi
Subahanallahi suka fada suna kallon junansu .

A kwana a tashi ba wuya girin allah Saida Umar yayi wata bakwai yana jinya kafin ya samu sauki da kar ya warke yasha wahala kala kala na jinya Amma daga Baya yasamu sauki....

A nan zan tsaya sai kuma mu hadu a page na gaba don jin yarda zata kaya...

AL'AJABIN SOWhere stories live. Discover now