"Yanzu yaya zan yi? I'm sure Rayhaan ne yake zuwa, Benaziiiiirr......... look at the mess you've gotten yourself into na tabbata he'll not let this slide"
Tana gama rufe baki aka turo ƙofa don haka ta sake ja da baya tana leƙowa a hankali.
"Wait! Wannan ba Rayhaan bane, who is he? Ban taɓa ganinsa ba a nan, what if he's Rayhaan's bodyguard?"Cike da isa yake taku yana ƙarema ɗakin kallo baki a taɓe, duk wani abu kuwa da yake gabansa hankaɗe wa yake yana jefarwa ƙasa ko kuma ya take ya wuce yana dariyar ƙeta
"Wow Rayhaan........ You are such a pain in the neck! But I'll soon get rid of that pain, so this is how you've been living lavishly momma's boy"
Ya ƙarasa jikin gadon ya ɗaura ƙafarsa ɗaya a kai yana kalle kalle kafin daga bisani ya zauna bakin gadon idanuwansa basu daina browsing ɗakin ba.
"Har yau i couldn't get the kind of love you've got from Dad why? Because of you! Or is it Because you are his own flesh and blood while ni kuma agola ne?, He doesn't consider me his child, but soon....... Very soon labarin zai chanja i will make sure they pay for all the pain they have inflicted on me!"
Ƙafafuwan Benazir sun gaji matuƙa gashi Mu'azzam bashi da niyyar tashi, ita kuwa duk maganganun da yayi a kunnen ta yayi don haka bata da wata damar fita jikinta yana rawa hakan yasa curtain ɗin yayi motsi, karaf idanuwan Mu'azzam suka sauƙa a kan ta.
"Ya Allah save me".
Benazir ta faɗa idanuwan ta a rufe.
"Who's there?"Ya tambaya yana miƙewa daga gadon cikin sanɗa ya nufi wajen ya kai hannu zai ɗaga labulen ya jiyo takun tafiya hakan yasa ya yi saurin juyawa ya bar ɗakin cikin sauri yana cije baki................
"Hayaaty....... We're home"
Rayhaan ne ya ƙwala ƙira tun daga ƙofa cike da fara'a yayinda Mahmoud ke biye da shi yana dariya. Turus yayi a tsakiyar falon ganin Hajiya Zainab zaune ta zuba musu na mujiya. Rayhaan ya juya ya dubi Mahaifinsa sannan ya sake maida dubansa gare ta da ƙyar ya buɗe baki yace
"Ina yini Hajiya"
Burus tayi da shi kamar bata ji shi ba shi kuwa bai tsaya ɓata lokaci ba ya juya ya dubi Mahmoud yace
"I'll be in my room Dad"
Kai Mahmoud ya jinjina yace "alright son"
"What was that Zainab?"
"What? Me kuma nayi?"
Mahmoud ya girgiza kai jin amsar da ta bashi yace "na tabbata ke ba yarinya bace, amma ki cigaba, kowa yayi na gari don kansa."
Taɓe baki tayi tace "ga dukkan alamu baka farin ciki da zuwan mu, wato ni da yara na ba mutane bane ka zuba mu a chan ka ɗauko matarka da shalelen ɗan ka kun taho nan mu kuma mu ci uwar da zamu ci, wannan ai rashin adalci ne a fili."
Murmushi Mahmoud yayi sannan yace
"Ina de gashi yanzu kun taho? "
"Aw! Haka ma kace?"
"Toh me zan ce Zainab? Kin yi abunda kika ga ya dace so ni bani da abunda zan ce, I've had a long day already, bani da ƙarfin biye wa duk wani guntun drama da zaki kawo, ni na wuce ciki, goodnight"
Baki a sake take kallon Mahmoud har ya ɓace daga ganin ta, cike da takaici ta miƙe tana ƙwala wa ruƙaiyah ƙira a hasale...........
________
Da murmushin sa ya tura ƙofar ɗakin shi sedai yanayin da ya tsinci ɗakin ba ƙaramin girgiza shi yayi ba, da sauri ya ƙarasa ciki har yana karkarwa tsabar ɓacin rai.
Daga inda take leƙowa tana kallon yanda Rayhaan yake fuming with anger, ita kanta yanayin nasa ya girgiza ta.
YOU ARE READING
NUR_AL_HAYAT
RomanceIt is said that everything is fair in love and war, Follow the love story of Rayhaan, a young adult full of Adventure, dreamz and ambitions as he comes across an ambitious teen girl Benazir a run away bride, as their lives take a different turn ...