episode 8

150 16 0
                                    

"Bauchi? Are You telling me that Benazir har tayi ƙwarin gwiwar da  zata tafi har Bauchi state ita kaɗai? Wanne hotel ne?....... Ok do not worry ni da kaina zan zo har Bauchi state ɗin I'll handle her by myself just let her be for the time being, yanzu zan kamo hanya".
    Hafeez dake zaune gefen shi nan take jikinsa ya hau ɓari domin tabbas ya san Benazir ce ake magana a kanta, a ranshi yace "how can we forget that Dad is very influential he can go to any length to make sure Benazir bata bashi kunya ba, a cikin kwana ɗaya kachal ya gano inda take yanzu kam babu wata dabara".

  Yana cikin wannan tunanin ne yaji sallama daga jin Muryar  yaji hankalin shi ya kwanta da ko amsa sallamar bai yi ba ya ruga zuwa ƙofa ya yi hugging ɗin shi

"Bro! Yah Saleem sannu da zuwa I'm relieved you came".
Murmushi wanda aka ƙira da Yah Saleem yayi sannan ya ce "Hafeez..... How have you been? I've missed you guys sooo much! Where are the ladies?". Ya tambaya yana dube duben falon karaf ɗaya suka haɗa ido da Dad, da sauri Dad ya kawar da kai fuska a daƙile shima haka Saleem tun tuni yanayin fuskar sa ta sauya, hannun sa bisa kafaɗun Hafeez suka ƙarasa cikin falon kamar bazai yi magana ba yace "Barka da rana"
Shima Dad kafin ya juyo ya amsa da "Barka dai" sannan ya dawo da duban sa ga Saleem yace "Why are you here?"
Saleem bai jira jin ƙarshen maganar ba yace "Am i not even allowed to come home anymore? Na zo in ga ƴan uwana ne or is that a sin?" Wani kallo Dad ya watsa masa shi ko bai bi ta kansa ba ya ja hannun Hafeez suka haura Upstairs yana tambaya

"Where's Ummi?" Ya tambayi Hafeez
"Tana ɗakin ta lets go, tun ɗazu take jiran isowar ka, you should've called, da an tura driver ya ɗauko ka ai".
Murmushi Saleem yayi kafin yace "yanzu dai ba gashi na iso lafiya ba? Besides i didn't call because i want to see how shocked my so called Dad will be idan ya ganni kwatsam a gida".
Shiru Hafeez yayi na ƴan daƙiƙai kafin yace
   "Yaya...... Wai me yake faruwa tsakanin ka da Dad ne? He even hate seeing you and kaima baka ragar masa ko kaɗan, Yah Saleem ɗin da na sani ba haka yake ba, you love and respect Dad until Ayeesha came into this family, tell me is it because of Ayeesha? Neither you nor Ummi tell us anything ko da yaushe na buɗe ido gani nake wannan familyn namu yana ƙara tarwatse wa, maganar kirki bata haɗa ka da Dad, Haka ma Ummi and Now even our sister is in trouble, bamu san irin halin da take ciki ba, i wish na bita mun tafi then at least Ummi would be at peace knowing that Benazir tana tare da ni, i was sooo foolish".

   "Hafeez.... Hafeez... My Brother! Where's your stop button? Please ka kwantar da hankalin ka komai zai dawo daidai! I will go find Benazir amma affairs ɗin gidan nan, whether it's abunda ya shafi Dad , Ummi, Ayeesha ko abunda ya shafi tsakani na da Dad please stay away from it, concentrate on your sisters and your studies wannan shine abunda zakamin. As for Benazir bazan bari wani ya cutar da ita ba in dai ina raye just relax, muje wajen Ummi."
Kai Hafeez ya jinjina ya bi bayan Yah Saleem.

      Da sallamar sa ya tura ƙofar tana kollon sa tayi saurin miƙewa ta nufo inda yake tsaye, hannuwan ta biyu ta riƙe fuskar sa da su tana ƙwalla,

"Saleem my child...... Finally you are home! Me yasa ka daɗe? Na jima ina jiran ka! Your father is turning into something else, my poor baby BENAZIR.... Ban ma san halin da take ciki ba yanzu, i'm tired of crying i feel suffocated but ganin ka da nayi yanzu a gabana yasa na samu new hope! Please find my Benazir and make sure she's safe i don't care what happens just make sure bata dawo cikin gidan nan ba". 
Kai ya jinjina yace "Ummi..... Ki kwantar da hankalin ki, i promise you bazan bari ta shiga wani hali ba, Benazir ƙanwa ta ne and i will protect her, yanzu ban san inda ta tafi ba if i have a clue where it would be easier for me"

"Tana Bauchi"
Hafeez ya faɗa a taƙaice, da sauri Saleem yace "Bauchi? Akwai wanda ta  sani a Bauchi ne? Me yasa bata tafi Gombe ba gidan Aunty?".
"Auntyn ka ma tana nan gidan abun ya faru, da safe ta tafi tare da y'an bikin  kar ka manta ƙanwar baban ka ce ita, so it's obvious that she will only support him kai kaɗai ne zaka kula da ƙanwar ka, ina so ka tafi Bauchin kawai, saboda bazan iya kwantar da hankali na ba sanin cewa babu wanda zai kula min da Benazir" Ummi ta ƙarashe maganar hanun ta riƙe da na Saleem. Shiru yayi yana jinjina kai ba tare da furta ko da kalma ɗaya ba..

________
Cikin sauri ta kammala wankan ta fito tana tsane jiki daidai lokacin ƙararrawar ƙofar tayi ƙara don haka ta zira abayar ta sannan ta buɗe ƙofan bayan ta leƙa ta wani ɗan rami dake jikin ƙofar, murmushi matar tayi mata kafin ta turo trolley ɗin abincin zuwa cikin ɗakin ta sauƙe mata plate ɗin. "Enjoy your lunch"
Matar ta faɗa yayinda ta juya zata fita, tana ficewa Benazir ta danna makulli a ƙofar sannan ta dawo. Shiryawa tayi tsaf cikin doguwar riga iya gwiwa fara da leggings baƙi sannan ta saka baƙin turban. Bakin gado ta zauna zata fara cin abinci kenan taji duk babu appetite tare da ita don haka ta ture shi gefe ta jingina da gadon ko ƙwararan mintina uku batayi ba barci ya sace ta...

*****.    ****
     A kasalance ya tura ƙofar ɗakin sa tun kafin ya zauna kuwa ya wurga jakar tasa bisa gado yana ƙare wa ɗakin kallo, babban ɗaki ne kam wani idan ya gani zai yi zaton falo ne guda biyu a haɗe, gadon dake tsakiyar ɗakin round shape ne da shi se wasu steps guda biyu a gaban gadon, iskar dake kaɗawa yasa farin net ɗin da ya sauƙo shawagi bisa gadon da kewaye. Gefe guda kuwa paintworks ne iri iri wasu an rufe da farin kyalle wasu kuma a buɗe,daga chan baya kuma kuteru ne sun yi U shape  kalar blue da side table a gefe. In short wannan ɗakin shine duniyar Rayhan! It defines him. duk windows biyu manya dake ɗakin buɗe suke da alama daga nan iskar ke shigowa, juyawa yayi bayan shi yana kallon lodin takardun dake jere a shelves yayi murmushi gami da tsalle ya dire a kan gadon yana sauƙe numfashi, i missed this room" ya furta a hankali kafin ya miƙe ya shiga bathroom. Shima yana fitowa ko sa kayan bai iya yi ba tsabar gajiya ɗaure da towel ya kwanta daga ka ganshi ka san barcin wahala yake yi.

    Two hours later......

    Da kyar ta buɗe ido tana ƙare wa ɗakin kallo kafin ta miƙe zuwa bayi lokacin azahar ne don haka ta ɗauro alwala, tana idar da sallah  ta dawo bakin gadon tana ƙoƙarin buɗe plate ɗin kenan aka bubbuga ƙofar, cikin sanyin jiki ta miƙe zuwa ƙofan har zata buɗe sai ta dakata, leƙawa tayi cike da fargaba ta ja da baya tana zaro idanuwa wanda tuni sun fara zub da ƙwalla
"How on earth is this possible? My Dad is here...... Yanzu yaya zan yi? I can't let them catch me in ba haka ba sacrifice na Ummi zai zama na Banza kenan, No! I can't!! Dole in san yanda zan fita daga nan!!."
Cikin sauri ta sauƙe labulayen ɗakin waɗanda suka kasance masu nauyi da duhu hakan yasa ɗakin yayi duhu, jakan ta goya ta saka takalman ta sannan ta rufe kanta da baƙin mayafin ta kafin ta nufi gefen ƙofar daf inda makunnan wuta yake ta kashe, hakan ya ƙara wa ɗakin duhu don haka sai tayi saurin buɗe ƙofar ta koma ta laɓe a gefen tana jin takun su alamar sun shigo ɗakin tayi farat ta fice da gudu har tana faɗuwa ƙasa, ƙarar takunta yasa suka bi bayanta da gudu har ma da Abdoul Hameed amma suka rasa inda tayi, cikin tsawa ya ce "me kuka tsaya yi? Na tabbata bata bar wannan building ɗin ba! Idan har baku kawo min Benazir ba i will kill you guys! Se in kashe banza! Da gudu suka nufi hanyar fita hasalima dai hannun riga sukayi da Benazir, domin tana fitowa ta nufi wata siririyar bene da ta sada ta da restaurant section na hotel ɗin, da sauri sauri ta nufi wata ƙofa  duk ma'aikatan wajen suka tsaya kallon ta da mamaki ita ma kallon su take tana sauƙe numfashi. Ƙarewa wajen kallo tayi sai lokacin ta fahimci cewa kitchen ne, farat ɗaya idea ta faɗo mata da sauri ta nufi inda aka tara ledojin shara ta fara kwashe su
"I'm new here! Yau a evening shift nake so I'll be cleaning up, ina ne wajen zubar da sharan? Ɗaya daga cikin su ta yi mata nuni da wata ƙofa na ƙarfe inda a samanta aka rubuta 'Exit' da jan fenti.  Murmushin dole tayi yayinda ƙirjinta ke dukan uku uku har ƙafafun ta na harɗe wa haka don sauri gani take ƙofar tayi mata nisa. Tana ficewa daga ƙofar ta  zubar da sharan a wajen ganin ta fito fili fayau ga titi tana gani, da gudu ta ƙarasa bakin titin ta tare mai adaidata sahu ba tare da sanin inda zata ba
"Ina za'a kai ki hajiya?".
Tambayar da me adaidata ke maimaita wa kenan yayinda ta lumshe idanuwa tana sauƙe numfashi , abunda ya fara zuwa ranta shine wajen da Rayhan ya ajiyeta lokacin da suka shigo garin Bauchi don haka tace "ka miƙe kawai daga nan zan sanar da kai inda zaka tsaya."

Jinjina kai yayi yacigaba da tuƙi ita kuwa idanuwan ta kafe suke kan titi a zuciyarta Addu'a take Allah ya haɗa ta da Rayhan once again.........
 

NUR_AL_HAYATWhere stories live. Discover now