KADUNA STATE
Alhj. Abdoul_Hameed Zayn Residence.
BENAZIR
Tsaye take bakin taga tana kallon harabar gidan dake cike mak'il da mutane kowa na harkokin gaban sa, mamakin yanda suke farinciki take yi masu gud'a nayi masu ciye ciyen abinci nayi.
Wani nannauyan ajiyar zuci ta sauk'e kafin ta bar wajen ta nufi gaban madubi tana k'are wa kanta kallo, Gown d'in dake jikin ta take kallo rai a dak'ile kafin tace"I can't believe wai mahaifina is getting me married to that Buffalo duk saboda business! He's selling his 18year old daughter for business, what about my dreams? My life will be ruined!".
Turo K'ofar suka yi da sauri suka shigo, Y'ammata uku ne kyawawa da namiji guda d'aya wanda daga ganin shi zai fi ta a shekaru, shi ya tura k'ofar ya sa jam lock ya rufe sannan suka k'araso cikin d'akin.
Da kukanta ta rungume su duka tana sheshshek'ar kuka. "Sis please do not cry, shushhh..... Umma ce ta turo mu afterall ita ma bata amince da auren nan ba ki d'auki abunda kike buk'ata we have to get you out of here!" Namijin shi yayi maganar hannuwan shi biyu bisa kafad'un ta yayinda ita kuwa ta zaro idanuwa tana kallon shi cike da mamaki
"Hafeez Bro Kana nufin Ummi ne tace kuzo ku taimaka min in gudu?"
This means that Our mom is also supporting me......"
D'aya daga cikin y'anmatan Aliyah ta jinjina kai hannunta cikin na Benazir tace "me zai hana? Ita fa Mahaifiya ce, bazata tab'a bari d'anta ya shiga wani hali ba, ko da kika bijire ma zancen auren ita ma dad'i taji domin ta san wasan business politics ake son bugawa da ke Adda Benazir you are our big sis, kin nuna mana soyayya da kulawa tun bamu kai haka ba, sai mu ne zamu juya miki baya lokacin da kika fi buk'atan mu? Sam hakan bazai yiwu ba, muna tare da ke d'ari bisa d'ari".K'aramar cikinsu wanda bata fi shekaru takwas ba ta rungume Benazir tace
"Idan kin tafi yaushe zan ganki?"
Murmushi Benazir tayi sannan ta rungume ta tace "Kar ki damu Ayeesha zan dawo very soon be a good girl"Benazir ya kamata mu tafi, ga wannan kud'in da waya, Ummi ta ce in baki duk inda kika sauk'a ki k'ira ta." Hanan ta mik'a mata kud'i da sabuwar waya fully charged, da sauri ta karb'a ta watsa su cikin jakar ta irin na goyawa d'in nan sannan ta kwashi wasu kayan da zata buk'ata ta hargitsa su ciki ta ja zip ta rufe jakar, duk da cewa ita ba ma'abociyar saka kaya masu nauyi bane bata da lokacin sauya na jikinta gashi kuma idan ta fita da su sai kowa ya gane ta tunda kowa ya san amarya ce kad'ai sanye da irin su, Cire high heels din k'afar ta tayi ta d'auko wasu sneakers nata ta zira sannan ta bud'e closet nata ta d'auko abaya ta zira tasa niqab sannan ta juyo tana kallon y'an uwan nata tace
"Soooo...... What's the plan??"Hafeez ya tura Aliyah ta yi musu gadin hanya kasancewar dogon corridor ne daga d'akin Benazir yayinda suka fice da gudu hannun shi rik'e gam da na Benazir, sun ci sa'a babu kowa a k'ofar da zata sada su da wajen shak'atawar gidan, amma sedai kafin su wuce sai sun ratsa ta babban falo wanda yake cike mak'il da bak'i y'an biki
"Yaya zamu yi yanzu?? Ta yaya zamu wuce wad'annan gayyar sod'in?" Hanan ta tambaya fuskar ta cike da damuwa. Wani shu'umin murmushi Benazir tayi kafin tace
"Relaax Beb! Karb'i jakar nan ki fita min da ita, ki tafi ke da Ayeesha no matter what zan samu hanyar fitowa just wait for us, ku tabbatar babu wanda yake wajen idan mun fito"
Kai Hanan ta jinjina da sauri ta amshi jakar ta ja hannun Ayeesha suka fita, da yake yara ne babu wanda yabi ta kansu ballantana ya lura da harkokin su, Benazir tayi murmushi tace "chill! Guys...... Saikace kun manta waye ni? Hafeez kar kace min ka manta wace Benazir? I never accept defeat easily! Aliyah yi sauri ki d'auko min lighter ko ashana koma de menene in har zai d'aga wannan fire alarm d'in, da sauri Aliyah tayi sneaking cikin kitchen ta d'auko lighter ta mik'a wa Hafeez kasancewar yafi Benazir tsayi, ya kunna a jikin trigger na alarm d'in kafin kace me alarm ya tashi kowa ya nufi k'ofa da gudu, a wannan hayaniyar su kuma suka kutsa kai suka nufi k'ofar da zata sada su da wajen shak'atawa, suna ficewa Benazir ta d'aga Niqab d'in ta kafin tace
"Yanzu ina muka nufa? Hafeez ka san idan muka zagaya za'a kama mu, all our efforts will be in vain"
Kai ya girgiza yace
"Ki rufe fuskar ki mana!! Babu wanda zai kama mu nayi parking mota daf corner bayan haka ma Ayeesha da Hanan suna wajen, they are keeping a watch just follow me".
Da gudu ta bi bayan shi, saida ya fara lek'awa yaga mutanen wajen sannan ya bud'e k'ofar motar cikin hikima ta shige ciki ta kwanta bazaka ce da mutum a ciki ba, Hanan ta jefo mata jakar ta a ciki sannan suka rufe k'ofar, daga tagar motar ta lek'o idanuwan ta cike da kwalla duk su ma kukan suke yi, Hafeez yace"Listen........ Yanzu zan fitar da ke daga gidan nan, no matter what kada ki taso just stay calm, by now nasan dole sun fahimci bakya nan so we have to hurry! Ku kuma duk rintsi kar wanda yayi magana idan an tambaye ku kuce baku san inda take ba, if possible kar ku daina wannan kukan naku, we are doing this for our sister right??"
Kai suka gyad'a da sauri Hafeez ya shiga motar duk da cewa shima yana tsoron amma ya dake ya ja motar, zufa na tsattsafo masa daga ganin shi kaga mara gaskiya, dayake biki ake yi gate d'in a wangale yake kawai ficewa yayi da motar, hankalin shi bai kwanta ba saida ya fice daga unguwar tasu baki d'aya..Da saurin shi ya shigo babban falon gidan yana dube dube kafin ya ce "Wai me yake faruwa ne anan? What's the commotion all about? A ina ne wutan ya kama? Ni ban ga alamar gobara ba a nan!"
Alhaji Abdoul_Hameed Zayn kenan, yayinda ya shigo gidan bayan hayaniya da ta biyo bayan saka wuta a jikin trigger na alarm da Hafeez suka yi.Kafin ya samu amsar tambayoyin sa d'aya daga cikin y'an aikin gidan su ta fito da gudu harda haki ta na fad'in
"Benazir........! Benazir!! Yallab'ai.... Benazir!!"."Ke don Allah in zaki natsu kiyi magana ki natsu, what's all this? Ina Benazir d'in? Me ya faru da ita?"
Ya tambaya a rikice.
Da kyar ta fisgo maganar tace "Bata d'akinta, ta gudu!"
Wani Harara da Ya watsa mata yasa ta sunkuyar da kai jiki na b'ari."You think I'm a fool? Benazir ta gudu ba kika ce... What a joke! Bata da wannan zarrar, kai!!!! Ku dai duba she must be somehere around here!!!
Five minutes later...
Rai a dak'ile, yake tafiya jikinsa har rawa yake yi ga zufa dake karyo masa tamkar mara gaskiya. Banko k'ofar d'akin ta yayi ya kutsa kai cike da isa
"Ina kike!!!? Aminatou!! Aminatou!!......"Da sauri ta fito daga bathroom tana tambayar dalilin da yake rafka mata k'ira haka
"Ina Benazir take?....... Ina y'arki? Ina kika b'oye ta? Ki ban amsa ina tambayar ki""Ban san inda take ba! Ko ban fad'a maka ba cewa babu hannuna a cikin harkokin bikin nan? Tun da gari ya waye ban sa k'afa na fita daga d'akin nan ba kamar yanda ka saka aka tsare min y'a ta a d'akin ta, so zai fi kyau ka koma ka tambayi wad'anda ka baiwa ajiyar ta ba niba, kuma ka saurareni kaji...... Bazan tab'a yafe maka ba indai wani abu ya samu y'ata now get out of my room! And you'd better go find my child kafin ta shiga wani hali...... Abdoul_Hameed i said get out of my room!!"
Kaushin dake cikin kalaman ta yasa shi ficewa kafin ta sake goga masa wata bak'ar maganar. Share hawayenta tayi cike da isa tace "Bazai yiwu ace na k'arar da rayuwa ta cikin k'unci ba dalilin auren ka sannan y'ata ma ta shiga irin halin da na shiga ba, i know my Benazir very well, she will never be able to endure the pain i endured, ba kuma zan bari a buga wasan business politics da ko d'aya daga cikin y'ay'a na ba! Dole ne tasa na tseratar da ita daga wannan auren, ba don ina son tayi nesa da ni ba kuma ko kad'an bana nadamar yin hakan".
Lek'a window tayi taga securities da motoci suna fita daga gidan yayinda Abdoul_Hameed ke tsaye yana magana da d'aya daga cikin police dake wajen.
"Zan k'ira Hafeez! I must warn him about the police." Ta fad'a da sauri yayinda ta janyo wayar ta tana lalubo lambar sa.....___________
"Zuwa yanzu na tabbata sun fahimci bakya nan, i know Dad will not rest until he finds you! Zan kai ki......." Bai k'arasa ba wayarsa tayi k'ara
"Umma ce!...... Hello Mom"
"Hafeez listen to me carefully mahaifin ka ya baza forces suna neman Benazir! Ka kula da k'anwar ka no matter what kada ka bari ta dawo nan! Remember dawowar ta nan kamar ta yanki ticket d'in tarwatsa rayuwar ta ne, Hafeez......""Kada ki damu Mom, just relax and take care of yourself, ga Benazir kuyi magana i have to keep driving, ko tashan ma bamu isa ba...."
"No! Kada kuje tasha! Shine waje na farko da zasu fara dubawa I'm sure of it!".
"Ok Mom zan san abunda zan yi".
Ya kashe wayar ya ajiye sannan ya maida hankali kan tuk'in da yake yi.............__________
Here we go again! It's the Second episode!!! Hope you enjoyed reading. Do share your views and opinion on the first two episodes tell me what you think and please don't forget to vote #showlove
YOU ARE READING
NUR_AL_HAYAT
RomanceIt is said that everything is fair in love and war, Follow the love story of Rayhaan, a young adult full of Adventure, dreamz and ambitions as he comes across an ambitious teen girl Benazir a run away bride, as their lives take a different turn ...