"I want you to notify all the hotels, and guest inn's dole tana ɗaya daga cikin su, Benazir must be back home tomorrow! Ban damu da yanda zaku aikata hakan ba just get her back!!"
Ya kashe wayar yana kallon Hafeez dake tsaye kanshi a durk'ushe. Wayar shi dake aljihun shi sai faman vibrating take amma babu damar d'agawa."Wayar ka ce..... It's ringing go ahead and pick it up".
Hannun shi na rawa ya zaro wayar daga aljihu yana duba screen ɗin cike da kula da sauri ya gimtse wayar ya saka ta a Flight mode kafin ya d'ago kai yana kallon Dad d'in
"Aboki na ne, mun yi akan zamu haɗu yau I've changed my mind coz I'm worried about Benazir anjima zan mishi bayani".Kai kawai ya jinjina ya fice daga falon a lokacin ne Hafeez ya saki wani nannauyan sigh of relief cikin sauri ya nufi sashen Mom d'in shi yana sallama ta amsa hakan yasa shi kutsa kai cikin falon inda ya iske ta tsaye tana duban waje daga window, hannunta ɗaya ta d'amke labulen windown har karkarwa yake.
"Ummi....... Are you okay? Har yanzu baki ci ko kaɗan daga abincin da nasa a kawo miki ba, haka ma abincin rana why are you punishing yourself like this?"
"Ta yaya kake tsammani zan iya zaman cin abinci Hafeez bayan Benazir na chan waje ban ma san halin da take ciki ba? Idan na tuna cewa i'm in here safe and sheltered sai in ga ban mata adalci ba, how can i be at ease when i don't know if she's safe or not? Taci abinci ko bata ci ba? I'm worried, na damu sosai Hafeez kuma da ban yi abunda na aikata ba i'm sure da mahaifin ta bazai hak'ura da auren ba, can You imagine damuwar sa a kan kuɗin da zai yi hasara ne ba a kan Y'arsa ba. Wayana dazun ya fadi, baya aiki sam i'm sure tayi ta k'ira na but bazata samu wayana ba tunda ya ɓaci".
"Ummi........ Farko dai yanzu kizo ki zauna. Come on have a seat first".
Janyo hannun ta yayi ya zaunar bisa doguwar kujera sannan ya zauna ƙasa hannunsa cikin nata, yace
"Benazir ta k'ira ni not long ago..... Dad ne ke wajen shiyasa ban d'aga ba, sabuwar numbar da kika nuna min da irin ta aka k'ira ni I'm sure Benazir ce, I'll call her but only after kin ci abinci."
Kai ta girgiza tace "Hafeez my dear i can only eat idan naji Muryar Benazir if not I'm not going to taste any of the food i can't!".
Murmushi yayi ya girgiza kai kafin ya ciro wayar ya yi dialing numbar, tayi ta ringing har ta katse ba'a d'aga ba, Hafeez ya sake dialing a karo na biyu tana ringing still yana kallon Ummin shi da emotions d'in dake fuskar ta domin damuwar ta har ya ninka na baya.....Duk yanda take jin barci kasa wa tayi sai ma jingina tayi a jikin gadon ta rungume pillow tana hawaye, idanuwan ta a kan Rayhan tana mamakin yanda yake barci cikin kwanciyar hankali
"Maybe he doesn't have any problem in life.... Maybe rayuwar shi is a beautiful one, da alama baya kewar kowa duba da yanda yake barci hankali kwance, i wish i could sleep just like him, rabona da barci irin haka wata ɗaya kenan, But today has been my worst day, i have to beg for a place to stay the night, and also food, ina kewar Ummi na, Bro Hafeez, Hanan, Ayeesha, Aliyah and most especially Bro Saleem! Da ace yah Saleem yana nan bazan shiga cikin wannan halin ba".
Tana cikin wannan tunanin taji vibration na wayar ta, da sauri ta ta ɗauka har tana rasa kunnen da zata kara shi tsabar gaggawa."Salaam.. Bro..... Ummiii! How's my Ummi?? Kana lafiya ko? Ina fatan Dad bai cewa Ummi komai ba how's she?"
Dariya yayi hawayen sa suka zubo yace "Relaax! Y'ar Ummi, gata nan tana jin ki, guess what? Ta k'i cin komai wai har sai tayi magana da ke I'm glad kin d'aga wayar......"
Bai gama maganar ba tayi wuf ta wafce wayar tana gyara zama"BENAZIR! How are you my darling? A ina kike yanzun? Have you eaten yet? You must be tired, na kasa natsuwa kwata kwata na damu sosai i thought bazaki d'aga wayar ba, are you safe my dear".
Hawayenta ta share tana jinjina kai kamar ummin tana ganin ta , tace
"Lafiya lau nake Ummi......da fari na shiga damuwa da naga wayarki bata shiga kuma baki k'ira ni ba haka ma yah Hafeez baya d'aga waya, i thought wani abu ya faru ne, now I'm relieved tunda kina lafiya, Ummi nima lafiya lau nake, naci abinci kuma na samu wajen kwana, i'm only missing you and my sisters soo much I'm missing home".Shiru Ummi tayi na ɗan wani lokaci kafin tace " kar ki damu my dear, komai zai dawo daidai, yanzu ki faɗa min inda kike and what happened? Are you sure you are safe?"
"Ummi bayan Yah Hafeez ya tsaya b'uya nayi cikin wata mota, it started moving ban san inda muka nufa ba ni kuma nayi barci, a hanya na farka and guess what? He's such a coward! That man thought that yaga aljana ne kawai se ya tsorita ya yi loosing control motar ta shiga daji, we crashed into a big tree......"
"Innalillahi wa inna ilayhir_ rajiu'n! Benazir kuma kikace lafiyar ki k'alau? Baki ji ciwo ba de ko? Kin ga likita ne?".
"Oh ohhhh Ummiiiiii........ I'm not done yet! And yes lafiya lau nake ko kwarzane ban yi ba haka shima Mr Man is perfectly fine only that motar shi tak'i tashi, lokacin wani yunwa nake ji na ga snacks a motan without a second thought na cinye, Ummi Mr Man is really a nice guy...... He didn't even mind me eating up those snacks. Bayan nan kuma mukayi ta tafiya a hanya mukayi sallar la'asar, da magariba muka shigo wannan ƙauyen, Mr Man ya sama min wajen da zan kwana a gidan maigari, he even got me something to eat, suma suna da kirki sosai but i couldn't eat their food. So ki kwantar da hankalin ki Ummi ina cikin k'oshin lafiya, because i have my guardian angel with me".
Ta k'arashe maganar tana kallon shi yayinda yake barci ko motsin kirki baya yi tsabar ya gaji.
Wani ajiyar zuci Aminatou ta sauk'e sannan ta ɗauki glass na ruwa ta kurb'a kafin tace "Benazir..... Do you trust him that much? Bakya tsoro? He's a total stranger my child you can't just trust anyone who offers help ba duk mutane ne keda hali na gari ba, what if he......."
"Umma.... Shi ne mutum na farko a rayuwa ta wanda despite my childish behavior bai damu ba, duk da cewa nice silar b'acin motar shi he is taking good care of me like a sister, bai bari na shiga damuwa ba ko kaɗan, duk da mun kasance keb'e cikin daji he did not take advantage of me, i trust him completely, ki tuna Ummi ba dan shi ba da yanzu ban ma san inda zan shiga ba. Yanzu dai ba wannan ba, ina so ki ci abinci tukunna. Kinga time kuwa? It's past ten already! Yah Hafeez make sure taci abinci I'm super tired, Ummi ki min Alk'awari zaki ci abinci...."
Murmushi Ummi tayi kafin tace "Yanzu ma kuwa... Zan cinye duk afterall my Benazir is safe and sound babu abunda yafi min wannan daɗi but you have to be careful you can't just trust anyone who has been nice to you ba duk aka taru aka zama ɗaya ba"Hafeez ta miƙa ma wayar suka yi sallama da Benazir sannan ya tisa ummi a gaba har saida yaga ta k'oshi kafin ya k'ira mai aiki ta kwashe kwanukan, sun ɗan yi hira kaɗan kafin ya fita bayan sun yi sallama.
Bangaren Benazir kuma ajiye wayar tayi sannan ta kwanta, sai lokacin taji zuciyar ta tayi sauk'i ko ba komai yanzu zata iya rintsawa domin taji muryar Ummin ta.
Duk maganganun da tayi a waya yana jin ta sarai domin shima barci bai ɗauke shi ba, domin Muryar da ya saba ji kafin yayi barci yau bai ji ta ba Oummin shi dalili kuwa shine babu network na mtn mai kyau a wajen sai na Airtel, haka ya kwanta barci.......
YOU ARE READING
NUR_AL_HAYAT
RomanceIt is said that everything is fair in love and war, Follow the love story of Rayhaan, a young adult full of Adventure, dreamz and ambitions as he comes across an ambitious teen girl Benazir a run away bride, as their lives take a different turn ...