1

50 4 7
                                    

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM

RABBISHRAH LEE SADREE WA YASSIR LEE AMREE WAHLUL UQDATAN MIN LISANEE YAFQAHU QAWLI.

                     ¶¶¶¶¶¶¶

Tsaye yake yana duba agogon dake daure a damtsen hannunsa mai qirar Rolex sai jera qananun tsaki yake, sanye yake cikin ash suit da loafers.

Idan akwai abinda ya tsana bai wuce African time ba wato makara, in banda baqin mahaifinsa ne da babu abinda zai sa ya jira. Har ya ciro waya zai yi kira sai yaji ance, FA'IZ UTHMAN SAULAWA?

Juyowa yayi yaga wata farar budurwa sanye cikin black abaya tayi rolling veil dinshi GA wani sunglasses ta maka a fuska. Yamutsa fuska yayi yana imagining wacece ita.

'Sorry for the delay, I'm FADEELAH UMAR FAROOQ, flight dinmu ne bai daga da wuri ba saboda weather. Hope baka yi fushi ba.

Idan dutse na magana to FA'IZ ya amsata, wucewa yayi ya shige mota abinshi abinda ya matuqar qona mata rai. Haushin kanta taji da ta bashi haquri ma gashi ya ba Wa banza ajiyarsa. Ganin bata da niyyar tahowa ne yasa ya danna horn kuma ya tada motar alamar wucewarshi zai yi. Boxes dinta guda biyu ta turo daya bayan daya ta saka a boot sannan ta bude qofar ta zauna ai kam ya kashe motar gaba daya sannan yace, 'ina fatan kin san ba direba aka turo daukarki ba'. Jin haka yasa ta bude qofar ta dawo gaba tana qoqarin saqala seat belt taji ya figi motar da gudun tsiya kamar ana binsa.

Ta tsorata ainihi addu'a ka kama yi a zuciya Allah yasa su isa gidan lafiya. Tun kafin ya kai gate ya fara danna horn da sauri masu gadi suka wangale mishi gate. Shagala tayi da kallon gidan tana tuna wasu abubuwa, an gyarashi beyond yadda ta sanshi a da, ko uffan bai ce mata ya fita ya wuce abinshi. Nan taji wani haushinshi ya qaru a ranta, lallai akwai aiki babba a gabanta.

Masu aikin gidan ne suka zo suka gaidata sannan suka bude boot suka kwaso kayanta aka mata jagora zuwa ciki.

'Oyoyo my daughter, ya hanya?'

'Lafiya lau, mum. Da fatan na sameku lafiya.'

'Lafiya lau, ya su Hajiya.'

'Kowa lafiya alhamdulillah.'

'Je ki yo wanka sai kizo muci lunch, bari Bintu ta kaiki dakinki.'

'Thanks mum'

'You're welcome'

FA'AZ DA FA'IZWhere stories live. Discover now